Hajjin 2024: An buƙaci maniyyatan Sakkwato su gaggauta biyan kuɗaɗensu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Sakkwato (PWA) ta yi kira ga maniyyatan jihar da su gaggauta biyan kuɗin kujerunsu kafin ranar 25 ga watan Disamba da Hukumar Hajji ta Ƙasa ta tsayar.

Shugaban Hukumar Alhaji Aliyu Musa ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Sakkwato jim kaɗan bayan ganawarsa da jami’in rijistar alhazan ƙananan hukumomi 23 da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya ce kiran ya zama wajibi bisa la’akari da gyare-gyare da matakan da Masarautar Saudiyya ta vullo da su gabanin aikin Hajjin 2024.

Shugaban na PWA ya buƙaci jami’an rajista da su kara himma wajen siyar da dukkan kujerun aikin Hajji da aka ware wa ƙananan hukumominsu.

Ya yi nuni da cewa lamarin ya yi gaggawar faruwa, yayin da ya jaddada wajabcin karvar kuɗi Naira miliyan 4.5 na farko daga hannun maniyyata kafin ranar 25 ga watan Disamba, matakin da ya ce zai ƙara wa hukumar ƙwarin gwiwa ta ci gaba da shirye-shiryenta.

Sai dai shugaban Alhazan na Sakkwato ya umurci jami’an hukumar rijistar alhazan ƙaramar hukumar da su ƙara ƙaimi wajen siyar da kuɗaɗen ajiya daga maniyyatan da ke da niyyar neman kujerun da aka ware wa ƙananan hukumominsu.

Musa ya ci gaba da bayyana cewa, a bana gwamnatin jihar Sakkwato ta ware kujerun aikin Hajji 4,996 domin siyar wa maniyyatan da suka fito daga ƙananan hukumomin jihar.

Ya ce a bana ana sa ran kowane mahajjaci zai ajiye kuɗi Naira miliyan 4.5 har zuwa lokacin da hukumar alhazai ta ƙasa ta bayyana a hukumance.

Musa ya bayyana cewa, duk da halin da ake ciki a halin yanzu na tattalin arziki, maniyyatan jihar na ci gaba da bai wa hukumar kula da kuɗaɗen ajiyar kujerun aikin Hajjin da suka samu.

Ya ce, tuni aka fara shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2024, yana mai bayyana fatan cewa tsare-tsare da matakan da hukumar ta ɗauka za su haifar da sakamako mai kyau.

“Muna yin tsokaci ta kafafen yaɗa labarai kuma an sanar da jama’a cewa mahajjata daga jihar su ajiye Naira miliyan 4.5 a matsayin ajiya na farko.