Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos
Hafiz Anas Abubakar Ɗahir da ya wakilci Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa shi ne ya samu nasarar zama gwarzon Musabaƙar Haddar Alƙur’ani Maigirma na shekarar 2023, wanda Gidauniyar Musabaqar Alƙur’ani Maigirma ta Ƙasa Reshen Jihar Filato ta saba shiryawa duk shekara karo na 38.
Ɗalibin, wanda ya fito daga Madarasatu Al-Bunyan ya samu nasara ne da maki 92.5 cikin ɗari, a rukunin haddar Alƙur’ani da Tafsir. Yayin da Hafiza Hafsat Ahmad a vangaren mata ta samu zama gwarzuwa da maki 89.3 cikin xari.
Shugaban Gidauniyar Musabaƙar Alƙur’ani Mai Girma ta ƙasa Reshen Jihar Filato, Sheikh Abdul-Azeez Yusuf wanda Na’ibin Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Isma’ila Adam ya wakilta ya bayyana cewa waɗannan gwaraza da suka yi nasara su ne za su wakilci Jihar Filato a Musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa da za a gudanar a Jihar Yobe.
Babban malami mai jawabi, Sheikh Rasheed Abdulganiy Daraktan Kula da Harkokin Koyarwa na Jami’ar Jihar Gombe, ya buƙaci al’ummar musulmi su zama masu nazari game da saƙonnin da ayoyin Alƙur’ani Mai Girma suke koyarwa, domin aiki da su a rayuwarsu.
Shugaban Hukumar Shirya Jigilar Aikin Hajji ta ƙasa, NAHCON, Alhaji Jalal Arabi wanda ya kasance babban bako a taron ya aika da saƙon fatan samun ga gwarazan da suka samu nasara tare da jaddada ƙoƙarin da Hukumar NAHCON ke yi don ganin an samu sauƙin kuɗin kujerar Hajjin Bana duk da yadda aka samu tsadar rayuwa a sassan duniya daban-daban.
Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Ahmad Adamu Mu’azu ya aika da saƙon kira ga iyaye su tsayu a kan tarbiyyar yaransu, duba da yadda ake samun yawaitar ƙaruwar aikata laifuka, wanda ake samun hannun matasa sosai a ciki.
An yi addu’o’i na musamman ga al’ummar Gaza da ke cigaba da fuskantar hare-hare daga ƙasar Isra’ila.
