Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Majalisar Wakilai ta gayyaci muƙaddashin Babban Sakatare na Hukumar Jami’ar Ƙasa (NUC), Darakta Janar na Majalisar Ilimin Shari’a kan dakatar da kwas ɗin karatun shari’a a Jami’ar NOUN.
Sauran waɗanda aka gayyata sun haɗa da shugabannin makarantar koyon aikin shari’a ta Nijeriya, da shugaban kwamitin Benchers da mataimakin shugaban jami’ar NOUN.
Hakan ya biyo bayan wani quduri ne da aka yi tsakanin mataimakin shugaban jami’ar NOUN, Farfesa Olufemi Peters da wasu ɗaliban da suka kammala karatun shari’a da suka koka da shugaban kwamitin ilimin jami’ar, Abubakar Fulata, a Abuja ranar Alhamis.
An zargi NOUN da dakatar da kwas ɗin, bayan matakin majalisar jami’ar ya samo asali ne daga umarnin majalisar ilimin shari’a.
Shugaban ya buƙaci ministan ilimi da shugabannin sauran hukumomin da abin ya shafa, da su duƙufa wajen ganin an kawar da ɓarnar da ke tattare da faɗuwar darajar ilimi a Nijeriya.
Ya ce, yajin aikin, rashin tsaro, rashin isassun kuɗaɗe, da samar da ababen more rayuwa, da dai sauran su, za a iya magance su ta hanyar jajircewa da haɗin kan masu ruwa da tsaki ciki har da Majalisar Wakilai.
Fulata ya ce, hakan na yiwuwa ta hanyar samar da sabbin hanyoyi amma masu inganci tare da aiwatar da waɗanda ake da su.
Wannan, a cewarsa, ya shafi sake tsara dabarun baya ga samar da isassun kaso don kula da ababen more rayuwa.
