CBN ga bankuna: Ku cigaba da hada-hada da dukkan takardun Naira

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya ya umurci dukkanin bankuna da su cigaba da bayarwa tare da karvar duk wani nau’i na takardun kuɗin Nijeriya, tsofaffi da sababbi waɗanda aka sakewa fasali.

Muƙaddashin Daraktan Sadarwa na Kamfanin Ali Hakama ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Hakan ya biyo bayan umarnin da Kotun Ƙolin ƙasar ta bayar a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, 2023, wanda ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi a ƙara tsawaita amfani da tsofaffin takardar kuɗin Naira.

A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta cigaba da cewa tsofaffi da sababbin takardun kuɗi su cigaba da zama a matsayin takardun kuɗi har bayan ranar 31 ga watan Disamba, har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta tsara tsarin maye gurbinsu ko sake fasalin su bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Wani ɓangaren sanarwar ta ƙara da cewa, “Don kauce wa shakku, Kotun Ƙoli ta ba da umarnin cewa tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500, da kuma 1,000 za su cigaba da kasancewa a matsayin doka, tare da sabbabin da aka sakewa fasalin.

“Saboda haka, bisa ga sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, duk takardun kuɗin da babban bankin NIjeriya ya fitar, za su cigaba da kasancewa a kan doka har sai Baba-ta-gani.”

Sanarwar ta ƙara da jan hankalin jama’a cewa, “Su karɓi duk takardun kuɗin Naira (tsofaffi ko sababbi) don gudanar da mu’amalarsu ta yau da kullum tare da kula da waɗannan takardun kuɗi da matuƙar taka-tsan-tsan, don kiyayewa da kare haƙƙin kuɗaɗen.

By Editor