Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Majalisar Tsofafin Manyan Sakatarori da Tsofaffin Shugabanin ofishin Ma’aikatun Gwamnatin Kano 134 da suka yi ritaya a lokuta daban-daban kuma suke raye yanzu haka da ake kira Council of Retired Heads of Service and Permanent Secretaries Kano State CORHSPS-KN ƙarƙashin shugabancin Alhaji Isah Mahmoud Babban kundi ne mai amfani ga al’ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya kasancewar sun yi aiki har zuwa ƙololuwar muƙami da ake kaiwa na ƙwarewa a aikin gwamnati.
Don haka a cewarsa za su cigaba da tuntuɓarsu a wajen tafi da gwamnati don cigaba Kano kamar yadda dama da wasu ake tafiyar da gwamnatin ƙarƙashin shugabancin Injiniya Abba Kabir Yusuf Abba Gida Gida kamar dai yadda SSG Dr Baffa Bichi, sakataren gwamnatin Kano ya bayyana a wajen taron majalisar KN CORHSPS na shekara-shekara da aka gabatar a ranar Laraba da ta gabata.
Shi ma Alhaji Bala Muhd Ɗanbatta Mataimakin Shugaban Majalisar, da Alhaji Mukhtar Giɗaɗo wanda ya shugabanci taron Majalisar na bana yaba wa gwamnatin Kano, su ka yi kan turo babban wakilinta a taron da kuma gudunmawa da haɗin kai da suke samu daga gwamnatin a ko yaushe, musamman ƙudirinta na ware biliyan shida don biyan kuɗin sallamar ma’aikata da kuma ƙoƙarinta na inganta aiki da ilimi lafiya da sauran fannoni na cigaban al’umma.
A qarshe Sakataren Majalisar Alhaji Muhd Ɗanyaro Yakasai a jawabinsa na godiya ya ce sama da shekara 50 da Kano ta zama jiha ba a tava samun irin wannan majalisar ba sai yanzu, don haka abin godiya ne ga Allah musamman yadda shugaban wannan majalisa ta tsoffafin manyan sakatarorin gwamnati ya bayyana nasarorin majalisar da matakan da ta biyo har zuwa, “ga kuma jawabi na kula da lafiya bayan ritaya daga MD Sulaiman Sani Wali da MD Shehu sai kuma tsokaci daga Gwani Dr Faruku Umar duk abin a yaba musu ne kan halartar wannan taro mai albarka.”
