Hamas da Isra’ila sun sake tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra’ila da Hamas sun amince da qara tsawaita yarjejeniyar da ke tsakaninsu da aƙalla kwana guda, matakin da ke zuwa mintuna ƙalilan gabanin kawo ƙarshen makamanciyar yarjejeniyar ta kwanaki shida da aka faro.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan tsanantar kiraye-kirayen ganin an ɗauki wannan mataki, inda sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ke miqa buƙatar ganin an samar da yarjejeniyar dindindn tsakanin ɓangarorin biyu tare da isar da kayakin agaji cikin gaggawa a Gaza.

Sai dai sanarwar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce an ɗauki matakin ƙara kwana guda a yarjejeniyar ne, don samun damar sakin ƙarin fursunonin Isra’ila da ke tsare a hannun ƙungiyar Hamas.

Da misalin ƙarfe shida na sanyin safiyar Alhamis ne yarjejeniyar farkon ke shirin kawo ƙarshe sai dai an ɗauki matakin bayan sakin Falasɗinawa 30 a daren Laraba wanda ke matsayin ladan sakin fursunonin Isra’ila 16 da Hamas ta yi.

Wani fitacccen ɗan fafutuka a yankin Falasɗinu Ahed Tamimi na cikin fursunoni 30 da Isra’ilan ta saki a Larabar, ɗan fafutukar da ya yi suna a shekarar 2017 bayan zabgawa wani Sojan Isra’ila mari.

Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da Antony Blinken ke dhirin kai ziyara a Tel Aviv.