Daga BASHIR ISAH
‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zaɓi Danladi Jatau a matsayin sabon Kakakin da zai ci gaba da jagorancin majalisar.
A ranar Juma’a aka naɗa Jatau a matsayin sabon shugaban majalisar jihar biyo bayan tsige Ibrahim Balarabe Abdullahi da Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta yi daga kujerasa.
Kazalika, ‘yan majalisar sun naɗa Mohammed Oyanki a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar.
Jatau na wakiltar shiyyar Kokona ne a majalisar, yayin da Oyanki ke wakiltar mazaɓar Doma ta Arewa.
