Na’urar VAR na ɓarna fiye da gyara – Bincike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu ruwa da tsaki na cigaba da miƙa ƙorafe-ƙorafe game da kuskuren da na’urar taimakawa alƙalin wasa ta VAR ke c gaba da tafkawa a wasannin gasar Firimiyar Ingila, ta yadda na’urar ke sahale bugun fenariti a wajen da bai kamata ba, baya ga soke ƙwallayen da suka cancanta.

Lamarin da ya faru a wasan da Fulham ta yi nasara kan Wolverhampton Wanderes da ƙwallaye 3 da 2 jiya Litinin ƙarƙashin gasar ta Firimiyar ya ja hankalin masharhanta bayan da alƙalin wasa Michael Salisbury ya amince da bugun fenariti ga Fulham a wajen da kowanne ɓangare ya yi ittifakin babu bugun.

Wasu alƙaluma da aka tattara sun nuna yadda VAR ke tafka manyan kurakurai a cikin wannan kaka kwatankwacin kakar wasan da ta gabata lamarin da ya sanya masu sharhi ke ganin na’urar ta haddasa matsaloli fiye da gyaran da ta yi daga lokacin da aka faro amfani da ita shekaru 4 da suka gabata zuwa yanzu.

A wannan kaka, tun gabanin kukuren na wasan Wolves da Fulham, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ke matsayin ƙungiyar da VAR ta fara yi wa varna bayan soke ƙwallon Luis Dias yayin wasansu da Brighton duk kuwa da yadda su kansu jami’an da ke kula da na’urar Darren da Dan Cook suka yi imanin cewa ƙwallon ta cancanta, amma na’urar ta nunawa alkalin wasa cewa babu ƙwallo kuma nan take ya soke ta dalilin da ya sanya aka tashi wasa Brighton na da 2 Liverpool na da 1 gabanin bai wa tawagar ta Jurgen Klopp hakura game da hukuncin daga bisani.

A vangare guda akwai kuma haɗuwar Fulham da West Ham wanda aka tashi wasa babu ƙwallo, shima dai a wannan wasa na ranar 6 ga watan Fabarairun 2021 anga tarin kurakuren da VAR ta tafka, bayan korar ’, ’yan wasa har biyu ba tare da haƙƙinsu ba da kuma soke ƙwallo guda.

A ranar 8 ga watan Aprilun da ya gabata ma yayin wasan da Totttenham ta yi nasara kan Brighton da ƙwallaye 2 da 1, VAR ta qi amincewa da bai wa Brighton bugun fenariti duk kuwa yadda aka tatsile Kaoru Mitoma a da’irar 18, hakazalika daga bisani na’urar ta soke ƙwallayen ƙungiyar har guda biyu.

Sauran kura-kuran na VAR sun haɗa da na wasan canjaras ɗin Arsenal da Brentford wanda aka sokewa Arsenal ɗin ƙwallo, gabanin bai wa ƙungiyar haƙuri bayan wasa, wanda ake ganin shi ya ragewa ƙungiyar karsashi tare da mako ta daga saman teburin Firimiya a kakar da ta gabata.