Nijeriya na duba yiwuwar sallamar kocin Super Eagles

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya ta fara laluben wanda zai maye gurbin mai horas da tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar, Super eagles, Jose Peseiro, yayin da ta ke duba yiwuwar sallamar sa.

Kwamitin gudarwar hukumar, ya ce bai gamsu da yadda kocin ke jagorantar Super Eagles ba, inda ya yanke shawarar nemo mai horaswa daga cikin gida.

Tun lokacin da Kocin ɗan ƙasar Portugal ya karvi jagorancin ƙungiyar a shekarar 2022, wasanni shida kacal ya samu nasara a kai, inda ya yi rashin nasara a wasanni 15.

Shugaban kwamitin, Shariff Ahlan yayin wata ganawa da manema labarai, ya ce idan har yana da cikakken ikon sallamar wannan mai horaswa da tuni ya daga masa jan kati, domin kuwa yadda yake jagorantar ƙungiyar babu abin a yaba a ciki.