Nijeriya na buƙatar matashin Shugaban Ƙasa don kawo sauyi – Jikan Sanata

Daga AISHA ASAS

Tsundumar matasa a harkokin siyasa abu ne mai matukar muhimmanci, domin matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, don haka idan sun gyaru, to dukkan kasar ta gyaru. Wakiliyar Blueprint Manhaja, AISHA ASAS, ta samu damar tattaunawa da jajirtaccen matashin da ya jima yana fafutukar wayar da kan matasa kan hanyoyin da za su iya cin gajiyar kurciyarsu ta fuskar siyasa, sannan matashi ne da ya shiga harkar siyasa da kafar dama, kuma ya jima yana cin moriyar ta, tare kuma da janyo matasa ‘yan uwansa don su lashi zumar da ya samu ba tare da kyashi ko hassada ba. Ga tattaunawar kamar haka:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da kanka?

JIKAN SANATA: Au’zubillahi minal shaidanir-rajim, bismillahi rahmanir rahim. Da farko dai sunana Kamaludeen Abubakar Lemie. Ni haifaffen Jihar Sakkwato ne, kuma har zuwa yanzu Ina zaune ne cikin jihar ta Sakkwato. Daya daga cikin jagororin matasa na Jihar Sakkwato, wanda ke fafutukar ganin matasa sun samu ‘yancin kansu.

Wane irin alfanu ke tattare da shigar matasa siyasa?

To, Alhamdu lillahi, shigar matasa siyasa yana da alfanu da yawa, wanda kuwa zan iya cewa, babban alfanun sa shi ne, babu wani cigaba da za a iya kawo wa kasa ba tare da matasa ba. Kuma babu ta wata hanya da ake iya ba wa matasa dama kamar ta fuskar siyasa. Idan zan yi misali da ni karan kaina, kwata-kwata shekaruna 27 ne, amma sanadin siyasa, da kuma damar da na samu ta siyasa kinga ga shi har mun kai inda muna kokarin mu jawo wasu, mu taso da su. Don haka shigowar matasa siyasa zai samar da cigaban da ba a tava samun irinsa ba.

Idan na fahimce ka, ka na nufin cewa matasa su suka san ciwon matasa ‘yan uwansu, don haka matasa ne a fuskar siyasa za su iya samar wa matasa canji daga irin rayuwar da suke yi?

Zan dan yi maki gyara kadan da ki ka ce ciwon matashi na matashi ne, wato shi matashi kala-kala ne, akwai matashi da yake da iyali da kuma iyaye, sun san darajar iyaye, sun san darajar ‘yan’uwansu, sun kuma san darajar matasa ‘yan’uwansu, kinga kenan sun san darajar kowa da kowa, to irin wadannan matasa muke magana kansu, domin su ne idan aka ba su dama kwalliya za ta biya kudin sabulu.

 Amma fa ba na ce za su fi wadanda suka gabace su ba, sai dai ta fannoni da dama za a iya samun biyan bukata, saboda yadda matashi zai iya jajircewa, ya yi ta jira da naci kan abu ba lallai ba ne ka samu hakan a wurin mai manyan shekaru ba, don bugun da matashi zai sha ya iya miqewa datijjo ba zai iya jurewaa ba. Saboda haka babu cigaba a siyasar ita kanta idan ba matasa a tare da ita.

Daya daga cikin alfanun shigar matasan siyasa akwai saka wa matasa kishin kai. Misali yau a ce ka ga abokin karatunka, tare ku ka gama makaranta, sai a ce an wayi gari ya zama kwamishina, dole za ka ji kishi, ka samu kwarin gwiwar ai kaima za ka iya. Shi kuma da ke kan kujerar, indai matashi ne mai hankali, idan ka je wurinsa nema, zai dubi alakar ku ta zama abokan karatu, ya yi tunanin yadda zai taimake ka don ba zai so ka cigaba da yawon barace-barace ba.

Wani lokacin ana samun matasa na korafin idan matasa ‘yan uwansu suka zama wata tsiya suna kin taimakon su, alhali sun san irin halin da suke ciki. A matsayinka na matashi da ya samu dama me ka ke yi na taimakon matasa ‘yan uwanka?

To, abubuwa dai da dama, sai dai kamar yadda ki ka ce matsala ce tamu mu matasa, sai dai kowanne matashi da irin tasa matsalar. Misali a kwanaki akwai wani da ya zo ya same ni, ya ce min ya gama NCE yana so ya karvi sakamakon shi, inda aka buqaci ya biya kudi 39000. To sai na ba shi zabi, shin yana so ne in sa a ba shi ‘result’ din nashi ne, ko kuwa yana so ne in ba shi kudi ya amsa? A mamaki na sai na ga ya tafi ne kan lallai dai shi in ba shi kudin ya karba da kanshi. Kin ga kuwa zancen nasa akwai alamar tambaya. To ire-iren wadannan matasa ne ke kawo wa matasa matsala.

Wannan ya na daya daga cikin yunkurin da muke yi na wayar da kan matasa, kan maganar nan da ake yi ta ‘da a ba ka kifi, gwara a koya ma yadda ake kama kifin’. To gaskiya samarin mu na wannan lokacin ba sa hangen nesa, su dai kawai a biya masu bukatarsu, wato da sun zo a ba su su kashe, wannan dabi’a na matukar ci mani tuwo a kwarya. Kuma zancen da ki ka yi wasu na ganin matasa ‘yan’uwansu ba sa son taimakon su lokutan da suka samu dama, akwai abinda masu azancen zance ke cewa, ‘wai idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai’, to hakan ce take faruwa lokuta da dama.

Yanzun nan wani zai zo da bukatar shi, idan ka yi masa, zai sanar, kafin a ce me wasu sun zo da irin ta, idan ka yi masu, za su sanar da wasun su ma su zo, to idan su wadannan ba ka samu yi masu ba, sai su koma da kai a ba ki, suna zagi, bayan cewa, Allah ne kawai ke da abin ba wa kowa.

To shi ya sa idan da a ce matasan za su karkata ne kan yadda za a gina su, sai ya zama an samu matasa da dama da za su iya bayar da agaji ga matasan, dom haka yayin da mutum biyu suka zo wurin Kamal ya taimaka masu, wasu biyun idan sun tashi akwai wani irin sa da za su iya zuwa wurin sa shi ma ya ba su irin tallafin, ta haka sai kiga kowa ya samu ba tare da an gajiyar da wani ko an kai kur din wani ba har ya ce babu ba.

Matasa da dama sun kasa fahimtar ita kanta siyasa, hakan ke sa su shigeta ido rufe wanda ke haifar da yawaitar ‘yan jagaliyar siyasa. A matsayinka na matashi me za ka ce ga matasa game da harkar siyasa?

Maganar gaskiya zancen ki haka yake, zan iya cewa kaso sitin na matasa ba su ma san meye siyasa ba. Ita siyasa ba tana nufin fada ba, ka cin mutuncin wannan, ka zagi wancan ba. Siyasa na nufin bajikolin hanyoyin nema wa kasa mafita, kai da naka ni ma da nawa, sai a tankade a ga shin wane ne zai iya kawo cigan da bangaren ke bukata. Idan kuma an yi amanna cewa wane ne zai iya ciyar da vangaren namu gaba, to ga mai hankali da ya san ma’anar siyasa, za su dunguma ne su marawa wancan baya don ya kai labari, koda kuwa suna da bambancin jam’iyya.

Amma abin takaici ne ki ga wasu ma uba da da ne ana gida guda, amma saboda siyasa ana gaba. Ko kiga saboda kawai wani ya yi PDP ko ya yi APC, sai a kore shi daga aiki, don kawai ba jam’iyyar da ya yi ba ce ke ci. Ni a nawa tsarin wannan ba daidai ba ne. kuma yana daya daga cikin abinda ya sa Nijeriya ta kasa cigaba.

Akwai wanda ya iya aiki, kuma zai iya samar da abinda ake bukata, sai dai shi a nasa ra’ayi waccan jam’iyya ce ta fi cancanta ya zava, kuma ya zaba, to bai kamata a ce don kawai ra’ayinsa a hana shi bayar da gudunmuwa ga mutanensa a vangaren da ya kwarai.

Yanzu misali, shekaru hudu ne ko a tsarin karvar mulki ba, to idan aka nada wani a wata kujera, zai dauki tsayin shekaru biyu yana rerafe a wurin, a fadi, a tashi, a yi kure, a gyara, a rubuta, a soke, ba zai zama gwani a kujerar ba har sai kusashen shekarun hudu, to lokacin da za a fara morar abinda ya iya, sai kawai saboda siyasa, sai wata gwamnatin ta daban ta sauke shi ba tare da la’akari da abinda ya iya ba ko zai amfanar ba, ta kawo wanda yake nata ba tare da duba da cewa shi zai faro ne daga kasa ba kamar wanda aka sauke. Kinga kuwa mun tattara a wuri daya. Karba-karba ta fuskar aiki na daga cikin ababen da suka hana Nijeriya cigaba.

Masu iya zance suna cewa, in ka ji wane ba banza ba, ko ba a sha dare ba, an sha rana. Za mu so sanin matakan da ka bi har ka kawo yanzu?

To, Alhamdulillahi, kamar dai fadar da ki ka yi, in ka ji wane to tabbas ba banza ba, sai dai Allah sheda ne, wallahi ni Kamal ban taba yin wani abu don wani ya sanni ba. Ni kawai na waye gari ne naga an sanni. Kuma shi sha’ani na kalubale duk wata rayuwa tana tattare da shi kowacce iri ce kuwa. Sai dai idan kana son ka ci galabar naka kalubalen to ka kwatanta rayuwa kamar wasan kwallo.

Ba za ka taba iya dauko kwallo daga wancan ragar, ka kai ta can ba, dole sai ka ba wa wani, ka sheka, shi ma ya ba wa wani ya yi gaba, har ya kai an wurgota daidai lokacin da ka isa kusa da wurin da za ka iya sata raga. Kuma harwayau dai za ki ga a cikin wasar, za a iya shurin ka, ka fadi, ka mike, a bangaje ka, kayi kamar za ka fadi, ka dake, ku yi karo da wani, ka ji ciwo, muradin dai ka samu ka isa ka ci wannan ‘goal’ din.

Don haka duk wanda zan ba wa shawara zan ba shi ne kan ya yi amfani da wannan misali, kuma ya sanya hakuri, domin duk wanda za ka ga ya shure ka, ba wai yana yi ba ne don ya tsane ka, sai don shi ma yana kokarin ganin ya isa ne a inda kaima ka ke da muradin zuwa, idan kuwa ka tsaya fada da shi, za ka iya rasa taka damar.

Abu na karshe da zan iya cewa, babu kamar gaskiya da biyayyar iyaye. Ko ba ka yi komai ba, idan yau ka zauna, duk abinda iyayenka suka ce ka yi, ka masu yadda suka yi farin ciki, to ka jiraye babban sakamako.

Kenan biyayyar iyaye na daga layin matakan nasara?

Ba wai a layi ba, ita ce matakin nasara, saboda ni ko ga labari ban taba jin wanda aka ce ya bijirewa iyayensa ya cigaba ba. To kuma duk wanda ki ka ji ance ya cigaba a duniya, to ki bincika akwai biyayya ga iyaye a tare da shi.

Ko Kamal na da burin tsayawa takara?

(Murmushi) To, ba zan iya masa wannan tambaya da kalma daya ba, eh ko a’a ba, saboda kamar yadda na ce ma ki, a yanzu muna kan hanyar wayar wa matasa kai ne, don su fahimci rayuwa da yadda za su gina kansu tare da sanin muhimmancinsu a tsakanin al’umma. To zuwa yanzu dai muna da dama, saboda zan iya kiran gwamna shi daga, duk sanatocin da muke da su, mutum daya ne ba ni da tabbacin idan na kira shi zai dauka, bangaren ‘yan majilisun jiha ma haka. Kuma idan muka nemi a mana, daidai gwargwado ana mana. Kwanan nan bada dadewa ba, na kira gwaman na sanar da shi wani al’amari da ya taso, kuma ba a fi mintuna goma ba aka yi al’amarin. Kinga kuwa idan irin haka na samuwa babu buqatar sai mun fito takara.

Kuma kamar yadda na fada abubuwa na sauyawa, idan hakan ta kasance, abubuwa za su iya sauyawa, to a lokacin za mu iya fitowa mu nemi hakkinmu, ba wai mu tsaya takara don kanmu ba, sai don matasa.

Idan hakan ta kasance, wacce kujera ce ka ke ganin za ka iya takara da za ta iya samar da canji?

Gaskiya babu kujerar da ba a iya kawo sauyi a tare da ita. Idan ki ka duba, ko ‘class rep’ aka ba ka, idan kana da kwazo sai kiga aji ya gyaru. Kansila na mazaba idan ya tashi kawo cigaba sai kiga abin da ya yi ya yi tasiri a mutanen shi. Haka ma ciyaman zuwa sama. Shi ya sa za ki ga an cewa, wane ya fi kowanne takwaran sa ta fuskar mukami, kuma abu iri daya suke samu, sai dai shi ya fi shi son cigaba ko iya aikin.

To, mu ma zan iya cewa za mu yi duba ne da inda idan mun samu kanmu za mu iya samar da cigaba sai mu tsaya takara ta bangaren.

Samun matashi a matsayin Shugaban Kasar Nijeriya. Mene ne ra’ayinka kan hakan?

A nawa gani babu abin da zai kawo sauyi a Nijeriya kamar samun matashi a matsayin shugaban kasa. Saboda kusan idan za ki duba, duk wadanda ake yi, sun fita shekarun matasa, dattijai ne, kuma sun yi, sun yi har sun gaji. Ba za su tava zama daya da masu tasowa ba.

Idan ki ka dubi matsala ta rashin tsaro da Arewa ke fama da ita, wadda ita ce kan gaba da komai, za ki samu cewa, duk inda matasa ke mulki a jihohin da wannan matsala ta addaba, za ki samu an fi samun sauki a wurin, domin an fi ingantattun hanyoyi da shiri na dakle matsalar.

Shi matsahi a kodayaushe zuciyarshi a tsaye take, kuma fatanshi ya yi abu na bajinta da za a iya kallonsa da shi ko a yaba masa da shi. Don haka ina mai tabbatar miki yau da za a samu matsahi a matsayin shugaban kasa, tsaf zai iya zuwa Sambisa ya yi kwanaki goma a can, kuma ba abinda zai faru, saboda dakewa irin tasa na duk abinda ya sa gaba sai ya ga bayansa, kuma a lokacin bai cika damuwa da ko ya yi rai ko ya mutu ba matukar burinsa zai cika.

To idan shugaban qasa ya je sansanyin ‘yan ta’adda ya yi kwana har goma mai zai rage, ai nasara ta samu, don dole dai da kwararru zai tafi yakin, kuma da ingantattun kayan aiki, kuma ba zancen kuskure ko gangaci don ga shi yana kallon yadda ku ke yin aikin.