Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano

Kotun Ƙoli ta ayyana Juma’a ta wannan makon a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kano da ke gabanta.

Sakataren tawagar lauyoyin Jam’iyyar NNPP, Barista Bashir Tudun Wazirci, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai.

“Gaskiya ne, an tabbatar da hakan a hukumance. Sun faɗa mana mu zo kotu ranar Juma’a don yanke hukunci.

“Sun shaida mana kada kowane ɓangare ya zo da lauyoyin da suka wuce biyu,” in ji Barista Bashir.