Ba wani gata da iyaye za su yi wa ‘ya’yansu da ya wuce tarbiyya – Mariya Durumin Iya

“iyaye su dinga bibiyar ‘ya’yansu mata a gidan aure”

Daga AISHA ASAS

Mai karatu sannu da jimirin bibiyar shafin Gimbiya. A yau dai da yardar mai kowa da komai za mu kai karshen tattaunawar da muke yi da Mariya Inuwa Durimin Iya, inda za ta fara da amsa tambayar da muka tsaya kanta, kafin sauran tambayoyin su biyo baya.

MANHAJA: Wacce shawara ki ke da ita ga iyaye mata kan irin rikon sakainar kashi da suke yi da tarbiyyar ‘ya’yansu da sunan zamani?

HAJIYA MARIYA: Gaskiya tarbiyyar ‘ya’ya mata tana cikin wani hali da za ka kasa gane shin su ma iyayen sun samu tarbiyyar. Shi ya sa a farkon tattaunawar mu na ce ma ki, dalilin kenan da ya sa na rubuta littafina na ‘Rayuwar Mace daga Haihuwa zuwa Tsufa’. Akwai abubuwa masu matuqar muhimmanci a rayuwar mace wadanda idan aka bar su ba kulawa, to rayuwar tata za ta iya shiga mawucin hali. Abu mafi muhimmanci shi ne iyaye su san cewa dole ne su dauki dawainiyar ‘ya’yansu mata.

Duk da cewa haqqi ne na iyaye su kula da ‘ya’yansu bakidaya, sai dai ta mace na zama ninkin-ba-ninkim saboda rauninta, da kasancewar hallitar ta ba ta iya tsayuwa karin kanta duk girman ta. Don haka komai kankantar bukatar mace a tabbatar an kawar mata da ita, har zuwa lokacin da za a yi mata aure. Kuma ko bayan auren ya zama iyaye suna bibiyar ‘ya’yansu mata a gidajen mijin, a san halin da suke ciki da kuma irin kawayen da suke mu’amala da su.

Sannan iyaye su tabbatar sun ba wa ‘yarsu ilimi, ba ma a iya matan kawai ba, har ma maza, ta hakan ne za su yi alfahari da su kuma al’umma ba ta more su. Abu na uku shi ne, tun yarinya na tasowa, lallai ne iyaye su kula da abokanin mu’amalar ta. A kullum ina gayawa iyaye, idan ‘ya’yansu mata suka yi kawaye, idan kawayen suka zo ziyara, ya zama da ke ake fira, ko ki dan maida hankali kan ababen da suke tattaunawa. Idan kin lura da mai rawar kai a cikin su, ko mai wata dabi’a marar kyau, kada ki yi wa ‘yarki fada kan ta rabu da ita. Ki hada su a tare ki masu fada, kuma ki shiga cikin kawancen nasu don saka ido.

A bangaren uba kuwa, idan yarinya ta kai lokacin fara yin samari kuwa, dole ne a sa ido sosai. Kar ka bar yaro yana zuwa wurin ‘yarka shekara daya, shekara biyu ba tare da zancen aure ba, musamman ma zamanin nan da muke ciki, idan mutum ya yi wata daya zuwa biyu yana zuwa, to ya kamata ka nemi sanin iyayenshi, idan da gaske yake yi sai ku zauna da iyayenshi a yi abinda ya kamata.

Kuma dole a san inda yarinya take sa gabanta idan ta fita makaranta, da su wa take mu’amala a makaranta, sannan daga makarantar ba ta zuwa ko’ina sai gida. Idan kuwa za ta je wani wurin ya zama ta sanar da inda za ta je din. Idan zai yiwu ma a hada ta da kaninta ko wani dan’uwanta su mata rakiya. Ma’ana dai dole iyaye su matsa sosai ga tarbiyyar ‘ya’yansu. Saboda yadda rayuwa ta koma yanzu, babu wani gata da iyaye za su yi wa ‘ya’yansu da ya wuce tarbiyya.

Ko akwai rawar da gidauniyar ke taka wa kan sha’anin yawaitar almajiranci?

To gaskiya maganan almajiranci ba abinda za mu iya cewa face, la haula wala kuwwata ila bii llahi. Ni dai a kan ra’ayi na, Allah Ya sani ba na son almajirancin nan, to amma wani abu ne da ya shigo cikinmu, kuma an ba shi wurin zama. Don haka duk da cewa yana da muhimmanci a yi maganin sa, amma ba za mu iya maganin sa ba, shi ya sa ba mu ma ba shi wani muhimmanci ba. Domin dole sai hukuma ta shigo ciki, kuma sai al’umma ta yarda da yaqar sa a birni da qauye. Don haka mu mun fi bada qarfi ne ga iyayen marayu da muke tare da su. Ita matsala ta almajiranci duk sanda ta shigo mukan yi maganin wannan matsalar da ta zo hannunmu.

Sai dai akwai kungiyoyin da suka mayar da hankali kansu, mu dai muna kyamatar abin, kuma muna fatan Allah Ya kawo mana sauki. Ya kawo mana sauyi kan yadda za a gudanar da ilimin na tsangaya din, saboda yawanci ana fakewa da shi ne, amma ba shi din ba ne, domin yawancin mabaratan da za ka gani kan hanya ba su da ma alaqa da karatun. Kawai sun dauki baran ne a matsayin sana’a. kinga kuwa irin wadannan ba abinda za ka iya yi masu.

Za mu so ki yi dan tsokaci kan aure da soyayya a Kasar Hausa.

Aure da soyayya a Kasar Hausa za mu iya cewa a yanzu wani abu ne da muke kokarin barin kyawawan al’adunmun mu na Hausawa mu koma wasu al’adun na daban. Kamar yadda muka sani, a Kasar Haausa soyayyar da ake yi a baya kusan in ce babu ma soyayyar ta kafin aure. Mafi yawa biyayya ce suke yi ga iyaye, sai kuma a yi auren har a samu abinda ake bukata a ciki.

To daga baya kuma da soyayya ta fara kunno kai, sai ana yin ta tsaftatacciya, ba a yi ta don wani burin duniya ba, ba a sabi Allah a cikinta ba, har akai ga aure. Sai kuma a ga auren ya yi albarka.

Wato akwai bambanci sosai tsakanin baya da kuma yadda muka tsinci kanmu a ciki yanzu. Yanayin ya kai ba mata ma ba kawai, har maza suna yin aure don abin duniya, saboda abinda za su samu a ciki. Sabanin da da ake cewa mata ne ke aure don kudi. To yau an wayi gari mazan ma suna aure don kudi. Sannan su kansu hanyoyin da ake bi na neman auren sun sha bamban da na da, domin a da kafin ma wani zance ya yi tsawo tsakanin budurwa da saurayi, ko mai neman auren za ka ga iyaye ne za su fara shiga ciki, su san wa zai nema, ita ma iyayen yarinya sun san wane ne ke zuwa wurin ‘yarsu. Amma yanzu sai a hadu a yi shekara biyu ana soyayya iyayen yarinya ba su san wa ke zuwa wurin ‘yarsu ba, shi ma iyayenshi ba su ma san yana zuwa zance wurin yarinyar ba.

Wannan kuwa ba karamar matsala ba ce, domin a irin wannan ne varna take shiga ciki, saboda ba idon manya a cikin zancen nasu. Wasu kuma za ki tarar suna son juna da auren, amma saboda yanayin bakin al’adu da suka shige mu sai ya zama duk wani abu da ake tsammanin sai an yi aure ne za a yi shi, sai ki ga an yi shi tun kafin a yi auren ma. Saboda an samu kusancin da ya yi yawa har ana ganin duk abinda aka yi ma ba laifi ba ne tunda dai aure za a yi. Sai kuma an yi auren matsalolin sun fara fitowa sai a rasa ta ina ne matsalar ta fito.

Shin ku ne ke zakulo iyayen marayu da ku ke ba wa tallafin, ko kuwa kofa ku ka bude ga duk wanda ke da bukata ya neme ku?

Eh to duk da cewa nemo iyayen marayu ba wani abu ne mai wahala ba, amma mu muke nemo su da kanmu, saboda koda a ce dama ta samu wadda za mu bar kofa a bude din to dole sai mun bi mun tantance su din, saboda yadda mutane suka zama yanzu kowa ma ya zama mabukaci, jira yake a baku mu samu. Don haka ni da abokan aikina da muka sadaukar da lokacin mu da aljihunmu ma wurin gudanar da wannan aiki, idan dama ta samu da za mu ba iyayen marayu, to mukan raba su ne tsakanin mu, inda kowanne zai kawo wasu a bangaren sa.

Wadanne irin nasarori ki ka samu zuwa yanzu a wannan tafiya ta wannan aikin taimako?

Alhamdu lillah. Babbar nasara da nake jin dadin kuma wadda ko iya wannan ne na samu nasara, wato addu’a da nake samu daga mutane, wadanda tallafin mu ya je hannunsu da ma sauran mutanen gari. Za a yi wa mahaifina da ya rasu addu’a, za a yi wa mahaifiyata da ke raye addu’a, za a yi min addu’a. To gaskiya wannan a kullum idan na tuna shi ina jin dadi. Nasara ta biyu ita ce, fara aikin nan da muka yi zuwa yanzu akwai wasu nasarori da muka samu masu yawa, ko in ce ayyuka da muka yi masu yawa da kamar mun shekara goma da kafa ta. Nasara ta uku, samun damar iya tsallake wasu daga cikin kalubalen da ake fuskanta a wannan tafiya. Wadannan kadan ne daga cikin nasarorin da na samu. Alhamdu lillah ko iya yanzu zan iya cewa na ci nasara a wannan aiki.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata masu zaman kashe wando?

Mata masu zaman kashe wando ko mata masu zaman kashe zani (dariya). To Allah ya sani wannan rayuwa ko da can da muka taso iyayenmu suna sana’oi. To sana’a dai a wurin mace dole ce, sai dai idan tana wani aiki na gwanmanti ne wannan da sauki. Amma yanzu da rayuwa ta yi tsada, maza ba za su iya yi su kadai ba. Rayuwar ta yi tsada, maza suna shan wahala, duk da dai mun san Allah ne Ya dora masu, kuma shi zai taimake su, to amma tadar rayuwar ta sa dole mace sai ta dan sa hannun ta a ciki ko yaya ne ta taimaka wa maigidanta a ciki. Kuma ba za a jira a ce sai randa mace mijinta ya mutu, ko auren ta ya mutu ne za ta fara sana’a ba. Ya kasance ta taso da son yin sana’ar tun kan ma ta yi auren ta koya. Kinga sai ta hada haske biyu ma, don wataqila tana da ilimin addini wanda dole ne, sai ya zama tana da ilimin zamani da sana’a shi kuma saboda duniyar ta. Rayuwa ba ta da tabbas, idan muka kalli iyayen marayun nan da yawa idan ka bi labaran rayuwarsu da yadda rayuwa ta tsananta gare su sai kiga ya samo asali ne da rashin sana’a, ko rashin ingata sana’ar, ko rashin taimako da ba su samu ba daga mazajensu.

A kullum ina ba wa mata shawara da su yi sana’a, sannan maza su taimaka wa mata su yi sana’a, kuma kada a dora mata wani nauyi da ya fi qarfin sana’ar ta. Don haka ina ba wa mata shawara da su nemi sana’a, kuma kar su rena sana’ar.

Mun gode da lokacin ki.

Ni ma na gode kwarai. Allah Ya kara daukaka Blueprint Manhaja Newspapers tare da dukkan ma’aikatansu, amin.