Tinubu ya sabunta wa NAHCON Kwamitin Gudanarwa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabon kwamitin gudanawar na Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCOM), kafin lokacin da Majalisar Dattawa za ta tabbatar da nadin.

Majiyarmu ta ce Tinubu ya dauki wannan mataki ne domin tabbatar da samun sahihin aikin Hajji kuma mara cunkoso a 2024.

Kwamitin zai gudana ne karkashin jagorancin Shugaban NAHCON na Kasa, Jalal Arabi, yayin da sauran mambobin Kwamitin sun hada da:

  1. Aliu Abdulrazaq — Commissioner, Policy, Personnel, & Finance
  2. Prince Anofi Elegushi — Commissioner, Operations
  3. Farfesa Abubakar A. Yagawal — Commissioner, Planning & Research

Wakilan Shiyya:

  1. Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta Tsakiya
  2. Abba Jato Kala — Arewa maso Gabas
  3. Sheikh Muhammad Bin Othman — Arewa maso Yamma
  4. Tajudeen Oladejo Abefe — Kudu maso Yamma
  5. Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas
  6. Zainab Musa — Kudu maso Kudu
  7. Farfesa Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam
  8. Farfesa Adedimeji Mahfouz Adebola — Majalisar Kolin Harkokin Musulunci a Nijeriya Nigeria