Daga BASHIR ISAH
Bayanai daga jihar Legas sun ce, wata ma’akaciyar banki mai suna Amarachi Ugochukwu, ta kashe kanta daboda tsadar rayuwa.
Jaridar Intelregion ta rawaito cewa wannan al’amari ya auku ne a ranar Litinin da ta gabata, kuma matar ta kashe kanta ne a cikin bankin da take aiki ta hanyar kwankwadar maganin kashe kwari.
An ce da misalin karfe dayan rana na wannan rana ne Ugochukwu ta tafi bandaki inda a nan ta kwankwadi maganain kashe kwari ba tare da abokan aikinta sun sani ba.
Daga bisani ne aka ce abokan aikin nata suka fara neman ina ta shiga ganin wayar da ta bari a kan teburinta na ta ringin alhali ba ta kusa.
Daga nan ne aka fara binciken ko’ina a bankin inda daga bisani aka gano gawarta a bandaki da kwalabar maganin kashe kwari a gefenta wanda ake kyautata zaton da shi ta yi amfani wajen kashe kanta.
Kazalika, an tsinci wata ‘yar takarda a kusa da gawar mai dauke da bayanin yadda marigayiyar ta bayyana irin kuncin rayuwar da ta fuskanta.
