Hazo: NiMET ta gargaɗi masu cutar asma da ma’aikatan jirgin sama

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, NiMET,  ta ba da sanarwar taka-tsantsan ga masu fama da cutar asma da masu fama da lalurar numfashi da kuma ma’aikatan jirgin sama kan yanayin buji mara kyau da ke tafe.

Rahoton da hukumar kula da yanayi ta fitar a ranar Talata ya kuma yi hasashen yanayin zafi da sanyi a jihohin Arewa ta tsakiya na kasar nan daga ranar Laraba 3 ga watan Janairun 2024.

“An shawarci mutanen da ke fama da asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan game da yanayin”, inji rahoton.

“An shawarci ma’aikatan jirgin sama da su sami sabbin rahotannin yanayi daga NiMet don ingantaccen shiri a ayyukansu.”

Ya kuma yi bayani dalla-dalla cewa mai zuwa ranar Alhamis “ana sa ran yanayi mai cike da buji a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.”

A ranar Juma’a an ce, “An sa ran yanayi na zafin rana da buji a yankin Arewa da Arewa ta Tsakiya a lokacin hasashen.