An ƙaddamar da bikin girbin amfanin noma a gonar Daɗin Kowa a Funtuwa

Spread the love

Daga WAKILINMU

An kaddamar da bikin cire shinkafa da albarkatun noma na bana a gonar ‘Daɗin Kowa Farm’ dake garin Dakamawa a karamar hukumar Funtuwa dake Jihar Katsina.

Bikin wanda ya kasance ana aiwatar da shi a karshen damina duk shekara ya kayatar yayin da a ka samu albarkatun noma fiye da na shekarun da suka shude, inda aka samu shinkafa wacce ta fi ta ko’ina yawa da albarka har tan miliyan daya a mashahuriyar gonar ta Daɗin Kowa.

Sauran albarkatun noman da aka girbe sun hada da farin wake, masara, gero da dai sauransu.

Hajiya Zainab wacce aka fi sani da Gimbiya ‘yar Sarkin Noma Garba Dan Ammani Funtuwa ta kasance ita ce mamallakiyar gonar Daɗin Kowa yayin da gonar ta samo asali tun daga mahaifinta Alh Garba Danammani Funtuwa wanda ya kasance shahararren manomi ne a karamar hukumar Funtuwa da ke jihar Katsina.

Gimbiyar ta kuma yi kiran lumana ga ‘yan uwanta magada sakamakon takaddamar da suka yi ta samu tun bayan rasuwar mahaifin na su a kan katafariyar gonar a inda wasu daga ciki ke ganin ba ai masu daidai ba ganin nasarar da Gimbiyar ta samu a kansu bayan dauki ba dadin da ya wakana a tsakanin nasu.

Sannan Gimbiyar ta yi kira tare da yin manuniya akan fa’idoji da alfanun fitar da zakka ga manoman da Allah ya bawa iko domin tana daga cikin turba na taimakawa addinin Musulunci wanda ya kasance abu mafi kyawu da ta ke tutiya da shi wajen taimakawa al’umma.

Gonar Dadin Kowa ta kasance bango ga al’ummar kauyen Dakamawa da kewaye yayin da ta yi fice wajen samar wa matasa maza da mata aikin dogaro da kai daban-daban inda suka bayyana alhininsu na kasancewar wannan mashahuriyar gona wajen sama masu ayyukan yi.

A karshe Gimbiyar ta nuna dimbin godiyarta ga Allah Madaukakin Sarki da ya bata amfanin noma mai tarin yawa da albarka kamar yadda aka saba a duk shekara.

Sannan ta kuma kara da mika godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shi Kashim Shettima kan namijin kokarin da yake wajen ganin tsaro ya tabbata musamman a bangaren harkokin noma. Kana daga bisani Gimbiyar ta ci gaba da miqa godiyarta ga jami’an tsaron Nijeriya musamman na ‘yan sanda na kokarin su wajen bai wa manoma kariya a ko da yaushe. 

Kazalika kuma Gimbiyar ta mika godiya da jinjina ga shugaban alkalan jihar Katsina Justice Musa Danladi kan namijin kokarin da ya ke na ganin an tabbatar da adalci tsakanin al’ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya.

Gimbiyar ta ci gaba da mika godiyarta ga tsohon shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari da irin su Baba Aminu Dogo Alhassan Dantata, da kuma sarakuna irinsu Maigirma Sarkin Musulmi Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III, mai girma tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi, Sarkin Katsina Baba Abdulmumini da Sarkin Daura Faruk Umar Faruk sai Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli. Sannan ta karkare da mika godiya ga yara da ma’aikata da sauran manoman Nijeriya.

By Editor