Mun canja rayuwar ’yan shaye-shaye fiye da ɗari – CAWI

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wani ɓangare na cigaba da ƙoƙarin ganin an dawo da hankalin matasa da hankalin su ke neman ɓacewa ta dalilin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sinadarai masu bugarwa, wasu matasa a Jos babban birnin Jihar Filato sun yunƙuro domin wayar da kan sauran matasa ‘yan uwansu da suka ɗauki hanyar shaye-shaye, da nufin canja musu tunani da salon rayuwa, ta yadda za su zama mutane nagari waɗanda al’umma za ta yi alfahari da su. Muhammad Lawal DeeDee Abubakar shi ne jagoran waɗannan matasa da suka kafa ƙungiyar ‘Community Aid Workers Initiative’ (CAWI) a ganawarsa da wakilin Blueprint Manhaja ABBA ABUBAKAR YAKUBU, shugaban ƙungiyar ya bayyana irin ƙoƙarin da su ke yi na ganin rayuwar matasa ta inganta.

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kan ka?

LAWAL DEEDEE: Sunana Muhammad Lawal Abubakar, wanda aka fi sani da Lawal DeeDee, kuma ni ne shugaban ƙungiyar yaqi da shaye-shaye a tsakanin matasa ta ‘Community Aid Workers Initiative’ wato CAWI wadda ke aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyar ‘League for Societal Protection Against Drug Abuse’ wato LESPADA.

Waɗanne ayyuka wannan ƙungiya ta ke gudanarwa?

Wannan ƙungiya da nake jagoranta tana aiki ne a ɓangarori huɗu, da suka haɗa da wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, samar da cigaban al’umma, kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma yaƙi da shaye-shaye.

An san ka kai da abokin tafiyar ka a matsayin Almajiran Zaman Lafiya, inda ku ke zuwa tarukan jama’a don yaɗa saƙonnin zaman lafiya, sai kuma ga shi kun tsunduma cikin harkar yaƙi da shaye-shaye, yaya abin ya ke?

E, babu shakka haka ne. An fara sanin mu a matsayin almajiran zaman lafiya, inda muke yawo wuraren tarukan jama’a muna yaɗa saƙonnin zaman lafiya. A cikin wannan ne kuma muka gano cewa shi kansa rashin zaman lafiya da muke fuskanta yana da nasaba da yadda matasan mu ke tu’amali da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran kayan sa maye masu gusar da hankali. Shi ne ya sa muka ga ya dace mu yi nitso cikin wannan batu na yaƙi da shaye-shaye, don magance matsalar tun daga tushe.

E, babu shakka haka ne. An fara sanin mu a matsayin almajiran zaman lafiya, inda muke yawo wuraren tarukan jama’a muna yaɗa saƙonnin zaman lafiya. A cikin wannan ne kuma muka gano cewa shi kansa rashin zaman lafiya da muke fuskanta yana da nasaba da yadda matasan mu ke tu’amali da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran kayan sa maye masu gusar da hankali. Shi ne ya sa muka ga ya dace mu yi nitso cikin wannan batu na yaƙi da shaye-shaye, don magance matsalar tun daga tushe.

Waɗanne ayyuka wannan ƙungiya taku ta gudanar kawo yanzu?

Da farko dai mun samu cikakken haɗin kai da goyon bayan manyan ƙungiyoyi da su ke taimakawa wajen samar da horo, da shawarwari kan dokoki da matakan yaƙi da shaye-shayen ƙwayoyi, irin su British Council, da LESPADA, da sauran ire irensu. Sannan mun gudanar da wasu ayyuka na faɗakarwa da wayar da kai a cikin anguwanni, inda muke neman irin matasan da suke ganin ya kamata su daina wannan harka, kuma suna buƙatar taimako.

Sannan a ɗaiɗaikun jama’a, ana samun waɗanda ke ziyartar ofishin mu da neman buƙatar mu taimaka wajen dawo da yaransu da suka kauce hanya saboda mu’amala da miyagun ƙungiyoyi, ko kuma su kansu yaran ana samun wasun su da ke zuwa suna neman mu taimaka musu su fita daga wannan mummunar hanya. A halin da ake ciki mun kai mutane fiye da ɗari gidan tarbiyyar gyaran hali, don a taimaka musu su gyara rayuwarsu.

Mene ne ka ke ganin yake haddasa shigar matasa cikin wannan mummunar harka ta shaye-shaye?

Abu na farko da muka fara fahimta shi ne rabuwar ma’aurata, rashin zaman iyaye a tare da juna, sai yaran su shiga wata irin rayuwa, babu kulawar uba ko uwa, ko kuma ya zama vangare ɗaya ne ya ke ɗaukar nauyin kulawar tarbiyyar yaran. Wannan na daga cikin dalilan da ke birkita rayuwar yaran su rasa madafa su, saboda rashin samun kyakkyawar tarbiyya, daga nan ne suke samun kansu a wannan harka. Na biyu kuma, mun lura da cewa wasu iyayen ba su san mene ne tarbiyya ba, saboda su kansu tarbiyyar ba ta ishe su ba.

Kamar yara ne suke haifar yara, iyayen ba su samu kyakkyawar tarbiyya ba, ga su kuma sun zama iyaye. Wannan yana taimakawa wajen jefa yara cikin rayuwa marar tsafta da shiga-shaye. Sai kuma wasu abubuwan da ba a rasa ba, da suka haɗa da tasirin muggan abokai ko ƙawaye a makaranta, ko a cikin anguwa, ko haɗuwa da yaran masu kuɗi da ke tavara iri iri babu mai kwaɓarsu, da kuma kwaikwayon rayuwar wasu jarumai, kamar mawaƙan turai, ko dai wasu fitattun mutane da ke rayuwa ta gaba gaɗi.

Yaya batun yadda ake samun ‘yan mata da matan aure da ke jefa rayuwarsu cikin harkar shaye-shaye, kuna cin karo da irin su?

Babu shakka mun samu kan mu cikin wani irin zamani, inda kwaɗayin abin duniya, da gasar kece raini da ya fi yawa a tsakanin mata, cire tsammani daga samun sauqin rayuwa, da mu’amala da ɓata garin samari ko ƙawaye, kamar yadda na faɗa a baya, su ke sa mata shiga wata irin rayuwa. Idan yarinya mai son abin duniya ce, tana son bin manyan yara, don ita ma a ce tana sahun wayayyu, sai ta shiga yin irin rayuwar waɗancan, ko idan mai kunya ce ta ga in ba ta sha wani abu ba, ba za ta iya aikata abin da ta ke so ba.

Wacce karin magana ce ka riƙa wacce ta ke zama maka mizani a wannan aiki da ku ke yi?

Karin maganar da ko da yaushe na ke gaya wa irin waɗannan matasa masu shaye-shaye ita ce, Tsalle Ɗaya Shi Ke Jefa Mutum Rijiya! Na kan gaya musu cewa, da kaɗan-kaɗan mutum ya ke farawa, amma idan ya so bari kuma ƙalubale ne mai girma!