Dandalin shawara: Ina matuƙar ƙyamar matata a lokacin da ta ke shayarwa

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Asas ya yau. Kwana da yawa. Ya iyali. Kin dai san na yi amarya a kwanan baya, kuma kamar yadda muka tattauna a lokaci da yawa Ina matuqar ƙyamar matata lokacin da ta ke shayarwa, dalilin kenan ma da na nemi shawararki a baya, saboda na ce, ba zan iya kusantar matata a lokacin. To yanzu amaryata ta haihu har an yi arba’in, shi ne da sunka yi maganar dawo wa na ce, ta zauna gida tukuna, daga baya ma sai na yi shawarar ta zauna gida har ta yaye jinjirin kana ta dawo. To fa kan haka ake ta tada jijiyoyin wuya, iyayenta sai fassara ni suke ba daidai ba, wai idan ba na son ‘yarsu, kawai in sake ta a wuce wurin. Har ita …………ta bi layinsu, ta ƙi fahimta ta. Kuma wallahi na yi duk abinda ya kamata, kuma Ina kula da su gwargwadon hali. To dai sun caza min kai da yawa, shi ne na ce bari na tavo ki, saboda na san ba a rasa mafita gurin ki. Na gode.

AMSA:

Bari mu fara da ma’anar shayarwa a al’ada da kuma a Musulunce. Shayarwa dai wata ɗabi’a ce ta ciyarwa ga sabon haihuwa ta hanyar tsotsar nonon mace. A shari’ance ita ce, shayar da yaron da bai haura shekaru biyu ba ta hanyar tsotsar nonon macen da ta ke lokutan haihuwarta.

Ayoyi da dama sun yi magana kan shayarwa tun daga matakin haihuwar, wanda a nan zan so a fahimci wani abu, babu inda addinin Musulunci ya sanya shi wajibi ga uwa ta shayar da ɗan da ta haifa, anan Ina so in fitar da abu mai muhimmanci da ya kamata ka fahimta, shayarwa haƙƙi ne na uba, wanda aka tabbatar ma uwa na da damar neman biya kafin ta shayar, wannan zai iya lurar da kai cewa, miji ba shi da hurumin ganin illar mace yayin da ta ke shayar da jinjirin da ta haifa, don shi ta ke wa taimako.

A zamanin baya, a tsakanin Larabawa, ana kai ‘ya’ya shayarwa, inda ake biya wata mace da ta mayar da shayarwa sana’a, kuma hakan bai zama abin haramci ga zuwan Musulunci, sai dai ya zo da sharuɗɗa na tsarkake shayarwa, da hukuncin da ke haramta auratayya tsakanin ‘yan’uwa na shayarwa.

Kamar yadda a cikin littafi mai tsarki, suratul Nisa’i, inda Allah ya yi bayanin matan da suka haramta maza su aura, a ciki aka sa “…da ‘yan’uwanku na shayarwa.” Kuma malamai sun yi bayyani sosai kan irin shayarwar da ke haramta aure, da duk abinda ya dangance ta. Ba za mu zurfafa ba, domin ba wannan ne darasin namu ba, abinda yake muradin mu, a fahimci wanda nauyin ciyar da jinjiri yake kansa, wato uba.

Idan mun yi duba kan ita kanta shayarwa da mata ke yi, za mu iya cewa, ta bambanta, domin kowacce mace da yadda ta ke irin tata. Akwai matan da ko mata ‘yan’uwansu za su iya ƙyamar su a lokacin da suke shayarwa, sakamakon rashin kulawa da ƙazantar da suka runguma, don haka ba abinda zai hana su da jinjirin ƙamshi irin wanda ba a so. Akwai matan da suke cutatar da jinjirin ma ba iya cutar da mijin kawai ba, ta sanadiyyar qazantar da suke yi, sai yaro ya sha ƙwayoyin cuta da zai lasa daga kan nonon sakamakon rashin tsaftar jiki da tufafi. A wannan gaɓar, ba na tunanin za a ga laifin mijin da ya qyaramace mace a irin wannan yanayi.

Sai dai a wani vangare, za ku samu mata masu shayarwa da jajircewa wurin gyara jikinsu, tsaftace kayan yaransu tare da amfani da turarukan da za su ɓoye ƙazgin tumbuɗi da na nonon da zai iya zuba a kayan, kuma suna iya ƙoƙarin kawar da idon mazajensu daga duk wata ƙazantar da ke tare da reno. Idan hakan ta kasance, menene za a iya kira da ƙazanta a tare da irin waɗannan matan? Menene abin ƙyama a tattare da su?

Abu na farko da ya kamata ka fahimta shi ne, idan har za ka nuna ƙyama ga matarka yayin da ta ke shayar ma da yaronka, kamar yadda na faɗa ma ka a baya, tamkar kana bata zavi ne tsakanin zama da kai da kuma shayar da jinjirin da ta haifa ma, wanda hakan ba adalci ba ne.

Idan kuma ka nemi ƙaurace wa matarka a lokacin da ta ke shayarwa (kamar yadda ka yi da uwargidanka) a nan ma ka cutatar da ita. Ba ka yi tunanin tata buqatar zuwa gare ka ba, tsayin lokacin da ka ƙaurace wa shimfiɗarta, kuma ka cutar da jinjirin dalilin saurin yaye shi da uwar ta yi, don kawai ka dawo da kwana tare da ita, da kuma cin abincin da ta dafa.

Idan zan faɗi ra’ayina a nan zan iya cewa, na fi ɗaura alhakin wannan ɗabi’a ta ƙyamar shayarwa da ka ke kan zugar shaiɗan, wadda nake ganin za ka iya magance ta idan ka yaƙe shi. Kuma ba wanda zai iya kawar da shi daga ranka face kai karan kanka.

Nonon shayarwa na ɗaya daga cikin abinci mafi tsafta da tsarki da aka yi a duniya, ka tambaye likitoci da malamai za su yi ma bayyani kan ruwan nonon da lafiya da tsaftar su, don haka ba su daga cikin abin da za a iya kira ƙazanta. Wannan ne ya sa na ce sharrin shaiɗan ne ke wahalar da zuciyarka, wanda nake fatan ka fara da yaƙar shi, idan hakan ya samu, zai fi, domin zai kawar da matsalar bakiɗaya.

Idan kuwa ba ka buƙatar gwada wannan hanyar dalilin tasirin abin a tare da kai, to akwai mafita ta biyu, wadda ita ce shawara ta ƙarshe da zan iya ba ka kan wannan matsala ita ce, ku nemi mai shayarwa, tunda dai bai haramta ba. idan har matarka zata iya fahimtar inda matsalar taka ta ke, kuma ta ji zata iya to sai ku nemi wadda zata shayar da jinjirin kai ka biya ta, inyaso nonon matar taka ya tsaya, sannan ta dawo gare ka.

Sai dai wannan shawarar zai yi wuya ta yi aiki a wannan gava, domin tun kan a kai ga haka ne ya kamata ka sanar da matar matsalar, ma’ana tun kan ta haihun har akai ga wannan lokacin da ka hasala iyayenta, wanda ko kaɗan ban ga laifin su ba, ko ba komai, ba wanda zai so ya riƙe ‘yar da ya aurar gida tun daga zaman jego har ta yaye abinda ta haifa, kuma wai ubansu na nan ba nesa yake ba.

Duk da haka, za ka iya gwada neman matar ku yi magana ta fahimta, idan har ka samu ta fahimce ka, ko a gidan naku za ku iya ajiye mai shayarwar har sai an yaye shi, ga shi tare da ku, kuma kai ka samu yadda ka ke so.

Sai dai da za ka ba ni damar zaɓa ma wanda ya fi ƙarko, zan ce, shawarar farkon dai ita ce mai ƙarko, idan ka magance matsalar zai fi, kuma shi ne adalci ko ga yaranka, idan ka tuna da cewa, ko kai karen kanka, wata bare bata shayar da kai ba, ka sha daga mahaifiyarka cike da so da kulawa, kamar yadda ka faɗa, to mai zai sa ka ƙwace wa ‘ya’yanka wannan damar.

Allah Ya sa mu fi ƙarfin zukatanmu.