Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri, NURTW, na ƙasa reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana cewa, ba shakka kawo yanzu da ya kama aikinsa a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ta Nasarawa ana cigaba da samun kyakkyawar dangantaka tsakanin ƙungiyar tasa da takwararta ta NARTO.
Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke hedikwatar NURTW a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar ranar Litini na mako da ake ciki.
Ya ce kasancewa shi shugaban NARTO a jihar ɗan uwa ne a gunsa sannan dukan su daga garin Lafiya ne yasa suke cigaba da samun fahimtar juna ayayin gudanar da harkokin su dabandaban a jihar.
A cewar Alhaji Muhammadu Maikwarya kasancewar duka ƙungiyoyin biyu suma taimaka matuka wajen inganta harkokin sufuri ne na ababen hawa a saboda haka bai ga dalilin samun rashin jituwa tsakanin su ba.
Ya cigaba da bayyana cewa, “Kaga tunda nazo ofishin nan a matsayin sabon shugaban ƙungiyar mu nan ta NURTW a jihar nan abinda yake yi shine ina tabbatar da kyakkayawar dangantaka ne tsakani na da shi shugaban wannan ƙungiya takwarar mu wato NARTO a jihar nan da sauran ƙungiyoyi ma baki ɗaya.
Kuma ina tabbatar maka cewa a yanzu ma zan iya raba ofishina in ba wa NARTO bangare guda idan suna buƙata don dai mu cigaba da wannan mutunci da zaman lafiya da muke samu tsakanin mambobin mu da nasu baki ɗaya a yanzu.
Kuma ina kara tabbatar maka cewa bazan taba yin kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da daurewar wannan kyakkyawar alaƙar tsakanin mu,” inji Maikwarya.
Dangane da rashin jituwa da mambobin ƙungiyoyi biyu suka ta samu a baya da har yakai ga aka yi ta zage-zage dama ba hamata iska inda akayi ta jikata mambobin ƙungiyoyin biyu ada Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana cewa an riƙa samu waɗannan sabanin ne a baya sakamakon rashin fahimtan juna da haƙuri da kuma juriya ne inda ya tabbatar cewa hakan bazai sake faru ba a ƙarƙashin jagorancin sa da hardar Allah.
Daganan sai sabon shugaban ƙungiyar ta NURTW a jihar Nasarawa Alhaji Muhammadu Maikwarya yayi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga duka mambobin qunkiyoyin biyu a jihar dama ƙasa bakiɗaya su tabbatar suna hada kai su kuma rika guji duk wani abu da ka iya tada rigima tsakanin su inda ya ce a shirye shugabancin ƙungiyoyin biyu suke su ɗauki kwararan matakai akan duk wani qan ƙungiyar da aka kama da laifin don ya kasance darasi ga saura.
Binciken wakilinmu dai ya gano cewa kafin yanzu dai an rika samun rashin jituwa tsakanin mambobin ƙungiyoyin sufurin biyu a jihar wato NARTO da NURTW ɗin inda saudayawa lamarin yakan kai ga kai wa juna munanan hare-hare tareda jikata juna da dai sauran su.
