Daga Umar Garba a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewar tun da ya zama gwamnan jihar Katsina ba qaramar hukumar da ta gagare shi shiga saboda tsoron ta’addacin ‘yan bindiga a jihar.
“Zancen banza ne ‘yan bindiga ke yi cewar za su kai mani hari, ba inda ɗan ta’adda zai hana ni zuwa a Katsina, ba kuma hanyar da zai hana ni bi.” Inji gwamnan.
Raɗɗa na mayar da martani ne lokacin da yake zantawa da majiyar jaridar Manhaja ta DW, game da wani rahoto dake cewa ‘yan bindiga na shirin kai ma shi hari saboda matakan tsaron da yake ɗauka kan ‘yan ta’addar jihar.
“Waɗannan ‘yan ta’adda ruwa ne ya ƙare wa ɗan kada ƙaryarsu ta ƙare sun ga cewa da gaske ake za a yi faɗa da su shiyasa suke kai harin mai kan uwa da wabi, suje ƙauye su harbe mutane, su ƙona gidajen mutane.” Inji shi.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa ba zai yi sulhu da ‘yan bindigar ba.
Raɗɗa ya ce, ” ‘yan bindigar na kashe mutane ba tare da an masu laifin komai ba.
“Abunda ya sa na dage kan cewar ba sulhu shine ba laifin fari ba na baƙi ka iske al’uma cikin gidajensu ka ci zarafin iyalensu ka kasashe su ka ƙwace masu dukiya.”
Sai dai gwamna Raɗɗa ya ce idan ‘yan bindigar suka kawo kansu suka kuma nuna suna son ayi sulhu da su zai amince ya zauna da su. Amma shi ba zai tava kiransu ba akan su zo ayi zaman sulhu.
“Yau idan ɗan ta’adda ya ga cewa abunda yake aikatawa ba dai-dai bane ya zo ya ce muyi sulhu da shi zamu yi, idan akwai yadda zamu iya taimakon shi zamu taimaka ma shi ya shiga cikin mutane ya zama ɗan ƙasa na gari, amma abunda ba zan yi ba shine, in tafi ina cigiyar ɗan ta’adda yazo mu zauna mu yi sulhu da shi ba zan yi ba.” Inji shi.
Gwmnan ya ce zai yi dukkan mai yiwuya don ganin ya samarwa al’umar jihar zaman lafiya don su cigaba da zuwa gona,asibiti da kuma makaranta kuma su iya yin rayuwa kamar yadda tsarin mulki ya ba su dama.
Da yake magana kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, Raɗɗa ya ce, yana farin ciki da ya ji shugaban ƙasa na maganar kafa ‘yan sandan na jihohi.
“Ana cewa gwamnoni sune shugabannin tsaro a jihohi amma ba su da ƙarfin iko na tabbatar da tsaron saboda basu ke ɗaukar soja ko ɗan sanda ba kuma ba su ke ba su kayan aiki ba, ba su ke biyan albashi ba iyakar su bada shawara ga jami’an tsaron.” Inji shi.
