*’Yan bindiga sun nemi a saki babansu, cewar iyayen yaran
*Ba ni da masaniya, inji Gwamnan Dauda
Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau
A halin da ake ciki yanzu kimanin watanni biyar da suka gabata kenan da wasu ’yan ta’adda suka afka wa gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da kimanin ɗalibai mata 30 da wasu ma’aikatan kamfanin gine-gine su tara yayin da a halin yanzu kimanin ɗalibai mata 12 suka rage har yanzu babu wani cikakken bayanin akansu. Wakilin Blueprint Manhaja a Zamfara, SANUSI MUHAMMAD, ya yi bincike game da lamarin:
Wasu ɗalibai mata 12 na Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 22 ga Satumba, 2023, yanzu haka sun shafe watanni biyar a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun nuna cewar, ɗaliban mata da abin ya shafa na daga cikin ɗalibai 30 na Jami’ar da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su watanni biyar da suka gabata.
’Yan bindigar a wannan rana sun mamaye ɗakunan ɗaliban a ƙauyen Sabon Gida da ke wajen babbar harabar jami’ar, inda suka yi garkuwa da ɗalibai sama da 30.
Blueprint Manhaja ta tattaro cewa, sauran ɗaliban mata su 12 da abin ya shafa har ya zuwa yau ba su san makomarsu ba, saboda babu wanda ya san inda suke a halin yanzu.
Sai dai majiyarmu ta tattaro cewa, sauran ɗaliban mata da har yanzu suke hannun ’yan bindigar sun shafe makonni 21, wanda ya kama kwanaki 148 a hannunsu.
Idan dai ba a manta ba, a farkon watan Oktoban shekarar da ta gabata ne mahukuntan Jami’ar Tarayyar ta Gusau (FUGUS) ta tabbatar da cewa, har yanzu ɗalibai 12 na jami’ar da ’yan bindiga suka sace na hannunsu.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Ya ce, daga cikin mutane 28 da harin ya rutsa da su, takwas sun tsere daga hannun ’yan bindigar yayin da sojoji suka ceto takwas.
Wasu daga cikin iyayen da suka zanta da Wakilin Blueprint Manhaja sun koka da yadda har yanzu mahukuntan jami’ar da hukumomin tsaro ba su yi musu wani cikakken bayanin inda ’ya’yansu suke ba.
A yayin tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho ranar Asabar da ta gabata, Alhaji Ibrahim Mai Unguwa Shema, wanda yana ɗaya daga cikin iyaye 12 da har yanzu ’yayan nasu suke hannun ’yan ta’addar, ya bayyana damuwarsu tar eda alhinin rashin ganin ’ya’yansu da ke hannun ’yan ta’adda watanni biyar da suka gabata.
A cewarsa, ’yan ta’addar sun kira su ɗaya bayan ɗaya sun gargaɗe su da kada su kuskura su bayar da ko sisi ga duk wanda ya kira su da sunan su bayar da kuɗin fansar ’yarsa. A cewarsa, sun bayyana ma shi tare da sauran iyayen yaran cewar ba za su sake su ba har sai gwamnati ta sakar masu babansu da aka kama a lokacin da ya ke yunƙurin zuwa aikin hajji.
“Sun kira mu sun bayyana mana cewa, ba sa bu kkatar kuɗin fansa, amma sun bayyana mana cewa, ba za su sake su ba har sai gwamnati ta sakar masu babansu da hukumomin tsaro suka kama a filin jirgin sama na Sultan Abubakar na III da ke Sokoto lokacin da zai je aikin hajji a shekarar bara,” inji shi.
Alhaji Shema, wanda cikin alhini da kaɗuwa ya bayyana wa wakilin Blueprint Manhaja cewar, Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara ya kamata su dubi Allah su saki wannan da ’yan ta’addar suke buqatar a saki, domin ’ya’yansu su samu ’yancin dawowa ga iyayensu.
A cewarsa, sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau, inda suka miqa saqon ƙorafinsu ga Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Mani Mumini, a watan da ya gabata, amma shiru, babu wanda ya tuntuve su game da matsalarsu.
Alhaji Ibrahim Shema ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara da jami’an tsaro da su dubi halin da suke ciki su sanya baki wajen ganin ’ya’yansu sun samu ’yancin dawowa ga iyayensu, domin su cigaba da rayuwa, kamar sauran mutane. A cewarsa, babbar damuwarsu ba ta wuce cewar yaran ba maza ba ne, mata ne, kuma dukkaninsu sun kai matsayin mata, inda suna iya fuskatar ƙalubalen keta mutuncinsu daga hannun ’yan bindigar da suke tsare da su.
“Akwai tashin hankali matuqa kasancewar waɗannan yara duk sun balaga kuma su na iya fuskatar ƙalubalen keta mutuncinsu daga waɗannan ’yan ta’addar ko ma ta kai ga halaka su, idan sun ƙi yarda. Saboda haka mu ke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara da su dubi Allah su saki wannan da ’yan ta’addar suke buƙatar a saki, domin ’yayanmu su samu ’yancin dawowa gare mu,” a cewarsa.
Dangane da ko su na da tabbacin ’yan matan nasu su na raye, Alhaji Ibrahim Mai Unguwa Shema ya ce, wani lokacin a baya sun kira shi kuma sun haɗa shi da ’yarsa, yana mai cewar, ko da ta ce mashi ‘assalamu alaikum, Baba ina kwana’, sai suka amshe wayar suka ce ma shi ɗiyarshi na nan da ranta kuma cikin ƙoshin lafiya.
“Wani lokaci sukan kira mu su haɗa mu da su, amma da zarar ɗiyarka ta ce ‘Baba, ina kwana?, sai su amshe wayar. Iyaka kenan,” a ta bakinsa.
Sai dai a wata zantawa da gidan rediyon DW kwanakin baya, Gwamna Dauda Lawal na Jihar zamfara, ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta na yin iya ƙoƙarinta na aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya, don samun cikakkiyar maslaha da za ta kai su ga nasarar ceto ɗaliban da suka rage a hannun ’yan ta’addar. Sai dai game da batun buƙatar ’yan binidgar cewa, a sako masu ɗaya daga cikinsu da hukumomin tsaro suka kama a lokacin da ya ke yunqurin zuwa aikin hajji a bara, Gwamna Lawal ya ce, ya yi bincike ko ina ba su samu bayanin hakan ba.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu jim kaɗan bayan faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Cif Ajuri Ngelale, ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, 24 ga Satumba, 2023, ya umarci jami’an tsaro su gaggauta ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayyar da ke Gusau.
A ranar 25 ga watan na Satumbar bara ne rundunar haɗin gwiwa ta JTF na Operation Hadarin Daji ta ceto wasu ƙarin ɗalibai mata na Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUG) a jihar ta Zamfara yayin da aka ceto aqalla mutane 13 da wasu ma’aikatan kamfani gine-gine uku.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da Merry Litinin MCB 2010301126 300 Level, Ruqayya Sani Batola Educ Chemistry 2110405077 200 Level (Zamfara), Salamatu Jummai Ɗahiru MCB 2110301034 200 LEVEL, Maryam Salawuddeen Accounting 191020106 300 Level Jihar Osun, Fiddausi Abdulazeez Edu Biology 2110404008 200 Level, Amamatullahi Asabe Ɗahiru Education Chemistry 2110405010 200 Level da Ketora Bulus Education Physics 2210407027 100 Level (Kaduna).
Sauran sun haɗa da Felicia Sunday Computer Science 2110308127 200 Level (Osun), Aisha Aminu Ujong Edu Physics 1710113023 ta sauke karatu (Cross River), Jamila Ahmad BCH 2220304001 200 Level, Mariya Abdulrahman Usman Turanci 1810103018 400 Level Katsina, Saadatu Aminu Abubakar Ilimi Biology 2010404011 da kuma Usaina Abdulrahman Education English 2210402007 100 Katsina Level.
Akwai kuma ma’aikatan kamfanin Gupran Engineering Services Limited da su ma aka ceto kamar haka; Mustapha Abdullahi, Kamalu Shuaibu da Ishaq Idris.
Kawo ya zuwa yanzu, babu wani takamaiman bayani daga jami’an tsaro ko hukumomin Nijeriya da ke nuni da cewar, akwai ingantaccen tsari da ake bi don tabbatar da a ƙwato ragowar ’yan matan 12 da ke a hannun masu garluwar a jihar ta Zamfara.
Duk wani ƙoƙarin da wakilinmu ya yi na jin ƙarin bayani daga bakin hukumomin tsaro kan halin da yaran suke ciki, ya ci tura.
