Gaza, Amurka ta sake hawa kujerar ta ki

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Zantawa kan yaƙin Gaza na cigaba da zama mai muhimmanci kuma kasancewarsa cikin manyan lamuran da ke ɗaukar hankalin ƙasashen duniya. Dalilin rincavewar fitinar Gaza an daina batun yaƙin nan na Sudan tsakanin shugaban mulkin soja Janar Abdelfatah Burhan da na ‘yan sa kai Janar Hameti Hamdan Daglo. Kuma ba wai fitinar ta Sudan ta kare ba ne.

Ga yaƙin da Rasha ke yi kan Yukrain inda ƙasashen yammacin duniya ke marawa shugaban Yukrain Volodymyr Zelenskyy baya. Hakiƙa an san shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai dakatar da kunce ɗamarar yaƙin ƙasar Yukrain ba don kange ta daga shiga ƙungiyar tsaron yammacin turai wato NATO. Tun fara gwabzawa a Gaza daga kutsawar HAMAS yankin Isra’ila a ranar 7 ga Oktobar bara hankalin duniya ya koma batun Falasɗinawa.

Ba ma don ba a kashe Falasɗinawan a kusan kullum ko ma kama wasu su a jefa a gidajen yarin Isra’ila ba ne a’a wannan karon don yadda mayaƙan Hamas su ka keta shingen Isra’ila mai matuqar tsaro su ka kai hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da ɗauke mutum 270 don zama garkuwa in yaƙi ya ɓarke. Akwai masu ra’ayin tamkar an hakawa Hamas rami ne ta faɗa ta hanyar kyale ta ta kai hari cikin Isra’ila da gangan don samun damar wargaza Gaza da murƙushe ko kashe dukkan ‘yan HAMAS ɗin masu turjiya ga Isra’ila a huta.

A zahiri da ma duba lamuran da su ka biyo baya ya nuna wannan tunani hasashe ne kawai da ba shi da inganci ko wata hujja mai kwari. Zahirin lamari ya nuna Hamas na sane kuma na shirye da martanin da Isra’ila za ta mayar. A kan neman mutum ɗaya rak Isra’ila kan iya tashin jirgi don kai hare-hare. Don haka Isra’ila ta fi duk wani mai sharhi sanin martanin Isra’ila ko abun da ke faruwa a gwagwarmayar yankin da ta fara tun 1948. Ai masu iya magana na cewa mai ɗaki shi ya san inda ke yi ma sa yoyo.

A karo na 4 tun ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra’ila da HAMAS, ƙasar Amurka ta sake hawa kujerar naki don hana ƙudurin dakatar da buxe wuta kan Gaza nan take.

Ƙasar Aljeriya da ke da ke wakiltar ƙasashen Larabawa a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ta kawo ƙudurin inda ƙasashe 13 cikin 15 su ka amince da dakatar da yaƙin, Amurka ta hau kujerar ta ki Birtaniya kuma ta qi kaɗa ƙuri’a.

Jakadan Aljeriya a majalisar Amar Bendjama ya bayyana matsayin su gabanin kaɗa ƙuri’ar cewa qudurin na da zummar yaƙi da masu kisan gilla ne da nuna ƙiyayya wato ƙasar Isra’ila kenan.

Amurka ta ce ta hau kujerar ta kin ne don yin hakan zai kawo karantsaye ga yunƙurin ta na sulhu da zai kawo ƙarshen kashe-kashen.

Jakadiyar Amurka a majalisar ɗinkin duniya Linda Thomas Greenfield ta ce shirin na da zummar sako waɗanda HAMAS ke riƙe da su da kuma sako kenan wasu daga dubban Falasɗinawa da Isra’ila ta riƙe a gidajen yarin ta.

Greenfield ta ce Amurka na son kawo tsagaita wutar na aƙalla mako 6.

Tsarin kwamitin tsaro shi ne sai ƙasashe 9 cikin 15 sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙuduri kafin a amince da shi bayan kuma rashin hawa kujerar ta ki daga ƙasashe 5 masu kujerar dindindin da su ka haɗa da Amurka, Faransa, Burtaniya, Sin da Rasha.

Zuwa yanzu fiye da Falaɗinawa 29,000 su ka rasa ran su a sanadiyyar harin boma-bomai na Isra’ila kuma hakan na cigaba da karuwa.

Koma dai me za a ce Amurka ce babbar aminiyar Isra’ila don haka ba mamakin matakan da ta ke ɗauke da ke yin hannun riga da na sauran ƙasashen duniya kan batun na Gaza. Duk da haka a na samun sauyin manufofi da muradu a siyasar ƙasashe ta duniya.

Yaƙin kan Gaza da ke sanadiyyar mutuwar akasari mata da ƙananan yara na ƙara fito da matsayin ƙasashe da yanda adalci ya dogaro kan muradu ko yanda ƙasashen ke ɗaukar lamari ga yadda ya shafe su ta fuskar tsaro da tattalin arziki. Ƙasashen da ke jin tausayin Falasɗinawa ba su da dama ta kai tsaye ta farmaki ko tura makamai ga HAMAS.

Duk abun da ‘yan ƙasashen ƙalilan za su iya tavukawa sai ta hanyar nuna tausayawa da bayan fage. Kazalika Larabawa kakaf ba su da sha’awar tunkarar Isra’ila don yadda tarihin yaki tsakanin su ya kasance a 1967 inda Isra’ila ta yi nasara a kan su bisa dalilan rashin haɗin kan su da kuma yadda Turai ke marawa Isra’ila baya. A gaba ɗaya ma Isra’ila ta gallabi Larabawa to bare a je ga maganar su tsaya tsayin daka wajen kare Falasɗinawa. Maimakon hakan ma wasu hasashen Larabawan sun dawo da hulɗar diflomasiyya da Isra’ila.

A lokacin da hakan ya fara a tsohuwar gwamnatin Donald Trump ta Amurka; shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya nuna takaicin Falasɗinawa kan yadda ‘yan uwan su Larabawa ke kulla hulɗa da Isra’ila da ta danne mu su hakki da neman dauwamar da su cikin ƙangin da ya yi kama da bauta.

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken na ganin samuwar dama ta ɗinke ɓaraka tsakanin Isra’ila da makwabtan ta ƙasashen Larabawa.

Blinken na magana a zauren taron shekara na tsaro a Munich.

Anthony Blinken ya ce ta hanyar kafa kasar Falasɗinu za a iya samun jituwa tsakanin Larabawa da Isra’ila.

A nan Blinken ya ce akwai shirin dawo da alaƙa tsakanin Saudiyya da Isra’ila dama wasu ƙasashen na Larabawa; amma cikin yarjejeniyar akwai kafa ƙasar Falasɗinu.
Blinken ya ce ita kan ta Isra’ila za ta samu zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasar ta Falasɗinawa.

Ƙasashen duniya da dama na magana da babbar murya don dakatar da aniyar firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na tura sojoji garin Rafah da sunan murƙushe ‘yan HAMAS.

Isra’ila na ganin Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar na zama a yanzu tungar ƙarshe ta HAMAS.

Majalisar ɗinkin duniya ta ce muradin na Netanyahu na da hatsarin gaske don zai kare ne kan kashewa da raunata mata da ƙananan yara.

Rabin mazauna Gaza miliyan 2.3 sun garzaya Rafah don samun mafaka inda garin ya cunkushe da jama’a da lalle su ka bar yankunan su na arewacin Gaza don ruwan wutar Isra’ila.

Gaskiyar magana Isra’ila ba ta sauraron wani kira na dakatar da muradun ta don yadda ta ke samun goyon bayan qasashe mafiya karfin tattalin arziki da makamai a duniya.

Amurka na buƙatar rage salon da Isra’ila ke kai a yanzu don kare fararen hular da ke shan azaba.

Isra’ila ta ceto wasu mutanen ta biyu a Rafah inda a gefe guda ta kashe Falasɗinawa 70 da ke samun mafaka a garin da ke kan iyakar Gaza da Masar.

Waɗanda a ke ceton na daga mutum 270 da HAMAS ta tafi da su a lokacin da dakarun ta su ka kutsa kan iyakar Isra’ila a ranar 7 ga Oktobar bara.

Mutanen da Isra’ila ta ce ‘yan asalin Argentina Fernando Simon Marman mai shekaru 60 da Louis Hare mai shekaru 70.

Kimanin rabin mutan Gaza miliyan 2.3 sun garzaya Rafah don samun mafaka amma a yanzu Isra’ila na kai hare-hare garin da zummar murkushe HAMAS amma gaskiyar zancen mata da kananan yara ke mutuwa.

Shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya buƙaci ƙungiyar HAMAS da ke mulkin Gaza ta amince da yarjejeniyar musayar kamammu da Isra’ila don kaucewa tozarta mazauna Rafah.

Mahmud Abbas da ke jagorantar ƙasar Falasɗinu daga birnin Ramallah ya ce yin hakan don kaucewa abun da ya faru a kafa ƙasar Isra’ila a 1948 da a ke kira NAKBA ta farko inda a ka tilasta Falasdinawa 760, 000 barin gidajen su.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na cigaba sa dagewa cewa lallai sai ya murƙushe ‘yan HAMAS duk da yadda a ke ta kiraye-kiraye na janye kai farmaki ta ƙasa kan Rafah.

Falasɗinawa ba sa ganin katabus ɗin jagorancin su ƙarƙashin fadar Ramallah don haka ‘yan HAMAS da ke amfani da makamai ke zama madogarar kwatar ‘yanci ga Falasɗinawan.

Sarki Abdullah na Jodan ya shiga jirgi da kan sa don duba aikin jefa kayan tallafi ta sama a yankin Zirin Gaza.

An ga hoton bidiyo da ke nuna Sarkin da kan sa a cikin jirgi a na aikin jefa kayan tallafin ga asibitocin da ke fili a yankin Gaza.

Wannan shi ne karo na 11 da Jodan ke shiga aikin jefa agajin inda aƙalla biyu daga ciki su ka zama da jiragen Faransa da Jamus.

Sarki Abdullah ya samu nasarar samun dama da yardar Isra’ila wajen kai kayan agajin ta ƙofar Jodan don rage yadda aikin ya kuntatawa shigo da kayan ta kan iyakar Rafah wato kan iyakar Gaza da Masar.
A na sa ran Sarki Abdullah da ke rangaɗi wasu ƙasashe kan Gaza zai gana da shugaba Biden na Amurka don neman a dakatar da yaƙin.

Kammalawa;

Ba wani abu a duniya da ya ke ɗorewa ko kai gaci a ƙarshe shi ne adalci. Matuƙar ba a samu daidato tsakanin sassa biyu ko fiye da ke fito na fito da juna ba to ba za a samu maslaha ba. A fili dai ko HAMAS ta mutu gwagwarmayar Falasɗinawa ta kafa ƙasar su ba za ta gushe ba.

By Editor