Yadda dillalin jarida ya rikiɗe zuwa shehin malamin jami’a

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi 

An shawarci manema labarai da suke kan ganiyarsu a fagen fama, mazauna Jihar Bauchi da cewar, kowane ɗaya daga cikinsu zai iya ko za ta iya murjewa daga masomi ko tale-tale, cikin sana’arsa/ta ta yaɗa labarai, har ya/ta kai ga cimma muradun sa/ta na rayuwa, walau kan wannan sana’a da yake/take kai, ko wata makamanciya da za ta kai shi/ta ga tudun mun tsira.

Wannan shawara ma’abuciyar ƙarfafa zuciya ta fito ne daga bakin wani jigon gwamnatin jihar Kaduna, kuma babba sakatare na sirri wa Gwamnan jihar ta Kaduna, Farfesa Bello Ayuba a kwanakin baya lokacin da ya ziyarci tsofaffin abokan sana’arsa ta yaɗa labarai mazauna jihar Bauchi, musamman ma dai ‘ya’yan ƙungiyar kafofin watsa labarai da a turance ake kira “Correspondents’ Chapel” ta Ƙungiyar ”yan jarida ta qasa (NUJ) inda daga nan ne Shehin malamin jami’ar ta Abuja ya fara bayyana shiga fafutukar rayuwa.

Farfesa Ayuba ya shaida wa tsofaffin abokan sana’ar tasa ta aikin yaɗa labarai cewa, “Ba ina yi maku wannan matashiya ko shawara domin kawai na busa kakaki ko sharewa ta ba ne, a’a, ina son ƙara faɗakar da ku ne kan batu na ƙarfafa zuciya ga duk wata sana’a da mutum yake son gudanarwa, ko kuma tsara rayuka yadda mutum zai kai ga cimma manufofin rayuwa cikin, sauƙi, nasara da falala wa kansa, da al’ummar da yake ciki.

Farfesa Bello Ayuba dai ya hau kan dandalin fafutukar rayuwa ne da fara aikin yin dillancin jarida da mujallun yaɗa labarai a garin Bauchi, bayan da ya kammala karatunsa na firamare a makarantar ‘ya’yan sojoji dake garin Kaduna, da kuma ilimin sakandare a Kwalejin Kufena dake Wusasa ta Zariya, kasancewarsa ɗan masarautar Zazzau ta jihar Kaduna ne.

Yana yin bayani ne wa tsofaffin abokan sana’ar tasa ta aikin yaɗa labarai lokacin da ya kai masu ziyarar ƙarfafa zumunci ne a garin Bauchi, a kwanakin baya lokacin da ya samu hutun shiga sabuwar shekara ta 2024, inda ya fara da cewar, “Ina matuƙar farin cikin samun wannan zarafi na saduwa da abokai, abokan tsohuwar sana’a ta, kuma ‘yan-uwa na da muka tashi tare. Na ga ya zame mun wajibi na yi wannan ziyara domin ƙarfafa zumunci na da ku, amma ba don burgewa wata ba.”

Ayuba sai ya yi waiwaye da cewar, “Na samu kai na a garin Bauchi a shekara ta 1984 inda na fara sana’ar dillancin jaridu da mujallun watsa labarai da kamfanin buga jarida na ‘New Nigerian Newspapers’. Na kasance dillalin jaridu da mujallu a shiyyar Arewa maso Gabas ta asali, wato kafin ƙirƙirowar jihohin Adamawa, Gombe da kuma Yobe daga cikin Gongola, Bauchi da Borno.”

Dillalin na jaridu da mujallu ya fara yin canjin sana’a ne da zamowa manemin labari, wato ‘Reporter’ a maɗabar buga jarida to ‘Today’ wacce a wancan lokaci ke fitowa sati-sati a shekara ta 1984, lokacin da ya dulmuye cikin ƙungiyar wakilan kafofin watsa labarai, wato “Correspondents’ Chapel” ta Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) kuma a wancan lokaci ya riqe muƙamin jami’in walwala na ƙungiyar, daga bisani kuma ya zama mataimakin sakatare.

Yayin da yake aikinsa a matsayin dillalin jaridu da mujallu, kuma jami’in kasuwanci na jaridar “New Nigerian Newspaper”, dillalin wanda daga bisani ya rizike zuwa mai ilimin Farfesa, yana nan kwance-tashi a ƙarƙashin jagorancin manema labarai yana koyon aikin jarida, musamman ta hannun jami’in na kamfanin ‘NNN’ da yake da laqabin ‘editor’ ko mai tace labarai, kuma a lokacin ne sha’awar aikin jarida ya dabaibaye zuciyarsa.

Bello ya ce, “Da damar shiga cikin aikin jarida ta bayyana gadan-gadan, ko’a fili ƙarara, sai kawai na dulmuye a cikin ta. Na fara aikin jarida na manemin labarai da ake yi wa laqabi da ‘Reporter’ tare da wata jarida da take fitowa sati-sati mai suna “Today”, a shekara ta 1988, kuma da sannu, yau da gobe ne likkafata ta cira zuwa matsayin babban jami’i na shiyyar Arewa maso Gabas na ita wannan jarida ta ‘Today’.

Bello ya bayyana cewar, yayin da yake yin wancan sana’a na aikin jarida, yana kuma zurfafa iliminsa, ya kasance mafaraucin labarai da rubuta su, kana yana zuwa makaranta domin zirga ilmin sa, kuma a wannan hali ne, ya samu ya yi jarabawarsa ta IJAMB a kwalejin fasaha da kimiyya ta jihar Bauchi da ake kira ‘BACAS’, har ma aka zave shi a matsayin shugaban ƙungiyar ɗalibai ta jiha.

Wani zai yi kintacen wannan mutumin da ya kasance ɗan jihar Kaduna ne, kuma ɗaukacin ɗaliban jihar Bauchi suna sane da hakan, amma suka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar su ta jiha, ba don komai ba, sai saboda ya mayar da Bauchi gida a gare shi.

Yayin da yake aiki da wancan jarida ta ‘Today’, sai tunanin Bello ya laqanta masa cewar, wajibi ne ya ƙara zurfafa iliminsa, kuma wannan tunani ne ya sanya, ya miqe ƙafa zuwa Jami’ar Maiduguri dake jihar Borno, inda ya fara samun digirinsa na farko a fannin ilimin gudanar da mulki. Kuma a lokacin da yana cigaba da aikinsa na jarida ne, bayan ya gama jami’ar ne, aka tura shi aikin bautar ƙasa a jihar Ogun ta Kudu maso Yammacin ƙasar nan. Bayan ya gama aikin bautar ƙasa, Bello sai ya sake dawowa da cigaba kan sana’ar sa ta aikin jarida a nan garin Bauchi.

Ayuba ya ce, “Saboda da haka, abinda nake son yin bayani a nan wa tsofaffin abokan sana’a ta shine, za’a ce na fara aikin jarida ne bayan gama karatun sakandare. Yayin da nake cikin wannan aiki na jarida, ina kuma cigaba da ƙaro ilimi, kuma bisa wannan manufa ce yasa na garzaya neman digiri na biyu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma digiri na biyun ma na same shine akan ilimin gudanar da mulki, wato digiri da ake kira ‘Masters’ akan ‘Public Administration’.

Bello Ayuba ya cigaba da cewar, “Saboda haka, a wannan hali sai nayi adabo da sana’ar aikin jarida, kuma na bar sana’ar ce zuwa fagen ilimi a jami’a, inda a shekara ta 2000 na samu aikin koyarwa a jami’ar Abuja a matsayin mataimakin mai koyarwa (Assistant lecturer), kuma daga bisani bayan shekaru uku sai aka ɗaukaka ni zuwa matsayin mai koyarwa (lecturer 11), kuma bisa qwazo dayin aiki tuƙuru, haɗi da wallafe-wallafe na mujallu, sai hukumar gudanar wa ta jami’ar ta Abuja ta ɗaukaka matsayina, ɗaukakawa na gaggauce zuwa babban mai koyarwa (senior lecturer).

A yayin da yake jami’ar Abuja, Bello sai ya sake cusawa kansa sha’awar ƙaro ilimi, lamarin daya sake mayar dashi garin Bauchi domin yin karatu a jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU), kuma a wannan jami’ar ce ya samu digirin digirgir a fannin Tafiyarwa/Gudanarwa (Management), wato PhD. Bello yace, “Mu tara ne farkon yin wannan kos a wannan jami’a ta ATBU, kuma mu uku ne daga ciki muka samu nasarar kammala wannan kos a ƙarshen zangon karatun, yayin da muka baro guda shida a baya, wato a jami’ar suna ta bugawa”.

Ya shaida wa tsofaffin abokan sana’ar tasa na aikin jarida cewar, “Bayan da na ci nasarar samun digirin digirgir, sai na koma jami’ata ta Abuja, kuma komawa ta jami’ar bada jimawa ba, sai aka sahale mun matsayin shugaban sashin koyan ilimin cinikayya ko hada-hadar ciniki (Business Administration) ta jami’ar.

Ina kuma shaida maku cewar, ba ina yi maku waɗannan bayanai domin burgewa bane, ina nufin na cusa maku muhimancin ƙarfafa zuciya ne bisa kan dukkan abinda mutum ya sanya a zuciyar sa na rayuwa, ko cimma buri, ko bukace-bukace na rayuwa, domin naga akwai matasa masu sabbin jini a cikin ku, waɗanda zasu iya farawa tun daga tale-tale, saboda da haka, magana ce ta niyya, ta ƙuduri, kamar yadda bahaushe ke cewa, abinda zuciya ta ƙudura, gangar jiki bi take yi, don haka wajibi ne mutum ya niyyata a ƙudurce kan dukkan abinda ya sanya a gaba.

Bello Ayuba ya ƙara da cewar, “Zan iya tunawa lokacin dana samu zama shehin malami, wato Farfesa, wani jami’i mai kula da ɗakin karatu a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, yana yi wa yaransa nuni da cewar, ku dubi wancan farfesan, a da mai sayar da jaridu ne a nan garin Bauchi, wai yau ya kasance farfesa.

Ba ni da niyyar yin jayayya da shi, amma ni ban tava yin yawon tallace-tallacen sayar da jarida ba, ni dillancinta na yi, nakan rarrabawa masu sayarwa ne, suma suna samun wani abu akai. Ni kuma a matsayin ma’aikacin kamfanin buga jarida ne ake turo min jaridu da mujallu ga masu tallar ɗaiɗai. Saboda da haka, na kasance babban jami’i dake jagorancin wancan fanni na Jami’ar Abuja a wancan lokaci.

Farfesa Ayuba ya ce, “Sun yi matuƙar yabawa da hazaƙa ta a yayin da nake jagorancin wancan fanni na koyarwa a jami’ar, ya sanya bayan shekaru biyu da ƙwarewa suka ɗaukaka ni zuwa matsayin muƙaddashin gangaran (Deputy Dean) kan koyarwa a jami’ar ta Abuja. Saboda haka, akwai buƙatar ku kasance masu lura akan dukkan lamurran rayuwa da kuka sanya a gaba, wajibi ne ku kasance masu matsanancin lura da kowace irin manufa ce ta rayuwa da mutum ya sanya a gaba da yadda zai iya cimma muradun ta, saboda mutum zai yi aiki domin cimma buƙatunsa, ko na al’ummarsa, ko ‘yan uwa da abokai, ko kuma ya zama bandaro.

“Wannan aiki da kuke yi, kuna yinsa ne domin amfanin abokai ko ‘yan-uwa. A wani juyin, mutum zai tsara kansa ne ta yadda zai cimma muradun sa bisa tsari da dacewa, don haka, ya zame wajibi mutum ya tsara rayuwar sa ta yadda zai cimma muradunsa.”

Ayuba ya ci gaba da cewa, “Saboda haka, lokacin da nake dillancin jaridu da mujallu, bani fatar na qare rayuwa ta akan wancan matsayi, ko wancan sana’a, duk da cewar, ina samun waraka ko kudade a wancan tsohuwar sana’ar, domin a duk jarida ko mujalla da nayi dillancin ta, Wallahi ina da kamashon kwabo biyu ko uku a kanta a wancan lokaci, saboda haka, ina samun kuɗaɗe, amma duk da haka, wajibi ne na tsara yadda zan tunkari ƙalubalolin rayuwa nan gaba ko masu tahowa.

“Idan kai ke taka rawa yau, ba lalle ne ya kasance kai ne gobe ba, al’amura suna iya canjawa, al’amuran rayuwa da yanayi waɗanda ke sassarfa turakun rayuwa. Ka duba da idon basira a yau, yadda kafofin sadarwa na zamani, soshiyal midiya, suka yiwa aikin jarida karan-tsaye. Kafin ka kinkimtsa labarin ka, ka tura shalkwata, cibiya ko ma’aikatar ku domin bugawa, nasu ya jima a yanar gizo, duk da cewar, yawancin ire-iren waɗannan labarai basu da sahihancin sahalewa”.

Bello sai yaja kunnuwan tsofaffin abokan sana’ar tasa da cewa, “Idan mutum ba zai tsara rayuwar sa ta yau da kullum ba, da sannu zai kasance abin dariya ga wasu, kuma wannan dalili ne ya tilasta ni na ziyarce ku da zummar faɗakar wa dangane da ƙalubalolin rayuwa, lamarin daya sanya ni tun farko, ko tun tale-tale, na dinga canjin tsarin rayuwa ta tare da yin dubi da ƙalubaloli gwargwadon yadda suke tasowa, ɗaya-bayan-ɗaya ba.

“Na fara da aikin kasuwanci ne, kuma ina matuƙar ƙoƙarin kan hakan a wancan lokaci, na sayi motata ta farko da kudaden kasuwancin jarida da mujallu, na auri matata da ire-iren waɗannan kuɗaɗe shekaru 35 da biyar kenan da suka shige. Duk da haka, na ƙwammaci na canja sana’a, la’akari da ire-iren canje-canjen rayuwa. Daga bisani na yanke shawarar komawa makaranta, kana a hannu ɗaya kuma ina yin nazari kan canje-canjen lamurran rayuwa.

Saboda haka, idan mutum ya dubi canja-canjin yanayi, idan mutum bai yiwa kansa qiyamul-laili ba, mutum zai gaza ga duk wata shimfida ta dabam da yayi wa kansa. Wannan shine dalilin daya sanya naga bai kamata na ƙare rayuwa ta akan sana’ar dillanci dana fara da ita tun farkon rayuwa ta ba, don haka bai kamata wani ya fara da matsayin manemin labari (reporter), kuma ya qare rayuwar sa akan hakan ba.

“Babu shakka, daman-maki da suka bayyana, kuci gajiyar su, kada ku yarda su kuvuce maku, kuma ire-iren waɗannan daman-maki suna wanzuwa ta kowace fanni na rayuwa. Ina da dalilai daya sanya nake yin wannan furuci akan lamurran rayuwa dabam-dabam, saboda ku masu aikin jarida ko manema labarai a sana’ance, ku mutane ne masu kima a idanun jama’a, kuma karɓaɓɓu akan dukkan lamuran rayuwa, zaku sanya ayi, kuma zaku hana yiwuwar abu saboda martabar aikin ku, daku kanku a idanun jama’a, duk abinda kuke bukata, in dai zaku sunkuya gare shi, sunan sa samemme, ya danganta ga yadda kuka tunkari bukatar abun ko kuma warware wata matsala”.

Farfesa Bello Ayuba dai, kafin naɗin nasa a kwanakin baya a matsayin babban sakataren sirri wa gwamnan jihar Kaduna, shine shugaban tsangayar karatu ta masu fiye da digiri ɗaya a mashahuriyar jami’ar ta Abuja (Unibuja), amma saboda ɗaukaka da Allah yayi masa, hazaƙar sa, sadaukar da kai, dayin aiki tuƙuru wa jami’ar da zummar biyan bukatun ma’abuta neman ilimi, ya amince dawowa baya zuwa muƙaddashin shugaban tsangaya ko gangaran (Deputy Dean) domin ya haɗa da rungumar fannin samar wa jami’ar kuɗaɗen shiga, wato ‘University of Abuja Ventures LTD, sashin da yake kula da dukkan kafofin kasuwanci na jami’ar.

Waɗannan kafofi ko kadarkun kasuwanci, kamar yadda shi Farfesa Bello ya zayyana, sun haɗa da
Amintacciyar Gidauniyar Jami’ar, Abuja (Abuja Trust Station); Masana’antar Yin Burodi da Tava Ka Lashe (University of Abuja Bakery and Confectionary); Sashin Makanikanci ta Jami’ar Abuja (University of Abuja Mechanics); Sashin Sufuri na Jami’ar Abuja (University of Abuja Transportation), da dai makamantan su bargaje.

Farfesa Bello Ayuba shi ne ya kasance Darakta na farko na wannan fanni na kasuwanci ta Jami’ar Abuja, ɗa’a gwamatse ya kasance Muƙaddashin Gangara na Tsangayar Masu Neman Ilimi Fiye da Digiri Ɗaya, kana Darakta kan Fannonin Kasuwanci na Jami’ar Abuja, wato ‘Deputy Dean, Post Graduate School kuma Darakta na Ventures Ltd a Jami’ar Abuja.

Abin lura a nan, a bisa matakai na fafutukar rayuwa da Farfesa Bello Ayuba ya kutsa ciki shine, kamar yadda ya fara da sana’ar dillanci, wanda wani fanni ne na kasuwanci, ya rayu akan wannan aniyar tasa, tare da gwamutsin qara ilimi wanda shine jigo a qalubalolin rayuwa da ya keta, har ya cimma muradunsa na kasuwanci zuwa ga samun ilimin shehin malami, wato Farfesa, lamarin da Bahaushe ke cewa, ‘tsintar dami a kale’, ko ‘gobarar titi’.

By Editor