Daga BASHIR ISAH
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bada tabbacin gwamnatinsa ta bada himma wajen samar da ilimi mai nagarta a Zamfara.
Ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake jawabi a wajen gasar wasannin motasa jiki na bana wadda makarantar Almufida International Academy ta shirya a Gusau, babban birnin jihar.
Kakakin Gwamana, Sulaiman Bala Idris, ya ce mamallakin makarantar ya karrama Gwamna Lawal da kambar yabo ta ‘Grand Commander of Friends of the College’ (GCFC).
Da yake jawabi, Lawal ya nuna gamsuwarsa dangane da bajintar da ɗaliban makarantar suka nuna a gasar tare da yaba wa hukumar makaranta kan bisa yadda take gudanar da harkokin makarantar yadda ya dace.
Ta bakinsa, “Na gamsu da abubuwan da na gani a nan. Wannan na nuni da samun gobe mai kyau a jihar.
“Na zo nan ne domin nuna goyon bayana ga fannin ilimin Zamfara. Idan ba ku manta ba, ta ayyana tokar ta ɓaci ga fannonin ilimin da kiwon lafiya a matsayin ɓangare na ƙudurorin gwamnatina.”
Ya ƙara da cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin kawar da ƙalubalen da fannonin ke fuskanta da kuma tabbatar da samun ilimi mai nagarta a faɗin jihar.
Ya ce, “Ilimi shi ne ƙashin bayan kowace al’umma, kuma Zamfara ba za ta yi sakaci da wannan ɓangaren ba. Muna ɗaukar muhimman matakai don amfanin ‘yan baya saboda an baro Zamfara a baya.
“Muna ƙoƙarin ganin mun mangace matsalolin ɓangaren ilimin jihar ta hanyar ƙara masa kason da yake samu, inganta ilimin da ake koyarwa da kuma horar da malamai,” in Lawal.
