Buƙatar samar da ’yan sandan jihohi

Spread the love

Ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a Nijeriya.

Bayan kwashe shekaru masu yawa, shugabannin Nijeriya sun samu matsaya kan batun samar da rundunar ‘yan sanda jihohi a ƙasar.

A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi 36 suka tattauna kan batun samar da ‘yan sandan jihohi don magance matsalolin tsaro da ke barazana ga ƙasar, waɗanda suka haɗa da satar mutane da fashi da makami da suka zama ruwan dare.

Ƙudirin samar da ‘yan sandan jihohi a Nijeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi ƙasar.

Ƙudirin wanda ‘yan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen ‘yan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka.

Sakamakon matsalar tsaro da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan, gwamnonin jihohin Arewa 19 ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da kuma Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi.

Gwamnonin da sarakuna sun bayyana cewa, ’yan sandan jihohi za su taka rawar gani wajen magance matsalolin tsaro a yankin Arewa da sauran sassan ƙasar nan. Baya ga haka, babu shakka a halin yanzu ƙasar na fama da matsalar ’yan bindiga, tada qayar baya, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in laifuka.

Dangane da ƙaruwar rashin tsaro da aikata laifuka a dukkan sassan ƙasar nan, an cigaba da gudanar da zanga-zangar neman kafa sabuwar hanya kan ‘yan sandan Nijeriya. Magoya bayan kafa ’yan sandan jihohi na ganin hakan zai rage yawaitar rashin tsaro a ƙasar.

Sun kuma yi nuni da cewa tsarin ’yan sanda na tsakiya na yanzu ba zai iya ba kuma ba zai magance matsalar rashin tsaro a tarayyar Nijeriya ba. Sun yi ta rarrashin cewa abu ne mai wuya tsarin ’yan sandan da ake da shi a halin yanzu ya yi aiki yadda ya kamata a ce qasa mai girman Nijeriya daga Abuja.

Ga alama gazawar tsarin ‘yan sandan ƙasa abu ne wanda ba za a iya ɓoyewa ba. Wataqila wannan shi ne dalilin da ya sa kira ga ‘yan sandan jihohi ke ƙaruwa tare da samun sabbin kiraye-kiraye a faɗin ƙasar. Wani ɓangare na shawarwarin taron ƙasa na 2014 shi ne samar da ’yan sandan jihohi. An dai yi ittifaƙin cewa aikin ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen rage yawan aikata laifuka a ƙasar.

Tunda kowane laifi na gida ne, samar da tsarin ’yan sanda na jiha, zai daƙile rashin tsaro, idan an sarrafa shi da isassun kayan aiki. Kasancewa kusa da jama’a, jami’an ‘yan sandan jihohi su na da damar sanin kowa da kowa. A lokaci guda, hakan zai amsa ga kiran gaggawa ga al’amuran tsaro.

Tare da isassun matakan bincike na hukumomi, za a kafa ’yan sandan jihohi yadda ya kamata. Hatta tsarin ’yan sanda na yanzu ba za a iya cewa ba lalle ya haɗa kafaɗa da wannan sabon tsarin ba. Idan aka yi la’akari da gazawar da ke tattare da tsarin ‘yan sanda na zamani, lokaci ya yi da za a ba ‘yan sandan jihohi dama.

Ma’ana, Nijeriya za a iya cewa ta isa ga jahohi da sauran sassan ’an sanda. Muna goyon bayan aikin ’yan sanda na jiha da sauran matakan ’yan sanda a ƙananan hukumomi da ma matakan al’umma. Wataƙila wannan ita ce hanya mafi dacewa don tunkarar dodo na rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.

A shekarar 2012, a matsayin hanyar tinkarar ƙalubalen tsaron ƙasar, gwamnonin jihohi 36 sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi. Mun yi imanin cewa gwamnoni za su iya yin aiki tare don tabbatar da cewa an kafa ‘yan sandan jihohi. Kafa ƙungiyoyin tsaro a yankin, irin su Amotekun a Kudu maso Yamma da Ebube-Agu a Kudu maso Gabas yana ƙara jaddada muhimmancin aikin ’yan sandan jihohi.

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tsaya ƙam ga buƙatar kafa ’yan sandan jihohi ta kuma ba ta kulawa cikin gaggawa.

Muna kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Majalisar Dokoki ta Jihohi da su gabatar da muhimman dokokin da za su kai ga kafa rundunar ’yan sandan jihohi. Ajanda ce da ba za a iya ɗage ta ba.

By Editor