‘Yunwa ta sa kan ‘yan Nijeriya ya haɗu’ – Obi

*Ya cacaki gwamnatin Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tsadar kayan abincin da ake fama da ita a ƙasa, yana mai cewa a halin da ake ciki “yunwa ta haɗa kan ‘yan ƙasa.”

Obi ya bayyana haka ne a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta gaza daƙile matsalar hauhawar farashin kayan abincin da ke ci gaba da addabar ‘yan ƙasa.

A cewarsa, “A yau, mun zama ƙasa wadda yunwa ta haɗe kanta lamarin da ya kai wasu na mutuwa saboda yunwa da wahala.

“‘Yan ƙasa na mutuwa” sakamakon yunwar da ƙasa ke fana da ita.”

Ya ƙara da cewa, a halin da ke ciki, miliyoyin ‘yan Nijeriya ba su san ta inda za su samu abincin anjima ba sakamakon ƙuncin rayuwar da jama’a ke fuskanta.

A cewarsa, “Jiya na karanta labarai yadda wasu ‘yan Nijeriya suka rasa rayukansu a wajen ƙoƙarin sayen shinkafa mai sauƙin farashi a ofishin Kwastam da ke yankin Yaba a Legas.

“Abin da taɓa zuciya yake, a ce duk da irin ɗinbin arzikin da ƙasarmu ke shi, amma ‘yan ƙasa na mutuwa a wajen neman sayen kayan abinci mai sauƙin farashi saboda yunwar da ƙasa ke fuskanta,” in ji Obi.