21
Jun
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Sabon lauya, Barista Ibrahim Dauda Adamu, wani matashi ne mai ƙarancin shekaru a garin Gombe, wanda ya kasance ya fito daga gidan da ba su da ƙarfi ya ke faɗi-tashin rayuwa, don ganin ya rufa wa kansa asiri. Ibrahim, wanda ya ɗauki sana’ar leburanci ta yin gini a matsayin hanyar dogaro da kai da ita, ya ƙuƙuta ya biya kuɗin makarantarsa daga sakandare zuwa Kwalejin Koyon Aikin Shari’a ta Legal dake garin Yola har zuwa Jami’a, matashin da ya kasance har a jami’a bai bar aikin na leburanci ba, don ya samu kuɗaɗen biyan…
