Burina shi ne kada na yi tarayya da ƙanena wurin dogaro da iyayenmu – Aisha Tanabiu

“Ina da burin samun mijin da zai bar ni na nemi na kaina”

Daga AISHA ASAS 

Neman na kai bai zama lallai sai ga macen da ta yi aure har ta haifafa ba, kamar yadda a shekarun baya a Ƙasar Hausa an fi ba wa sana’ar matar aure mai ‘ya’ya muhimmanci fiye da ta matashiya mai shirin yin auren. Wataƙila hakan bai rasa nasaba da cewar, ita mai auren ta fi mallakar hankalinta, kuma ita ce ke da ‘ya’ya da za ta nema don su amfana.

Yayin da wasu ke ganin macen da ba ta yi aure ba ba ta buƙatar sana’a domin ana yi mata komai a gida daidai gwargwado, wanda ba lallai sai ita abinda ta ke so ba, sai dai idan ta ci, ta sha, an gama da ita.

Wannan ke sa a wannan zamani da muke ciki matasan mata da ba su iya sa wa zukatansu birki suke bin hanyoyi don samun ababen da suke buƙata da a gida ba a ɗauke su da muhimmanci ba, kamar yawan roƙon samari wanda muka sani hanya ce da ke da sauƙin kai mace ga varna.

Ba wai na ce waɗanda suka yi wannan tunanin sun kuskure ba, sai dai zan so na san ta yaya icen da aka ɗauko daga wani wuri da girman sa, aka ajiye a wani gun zai iya wanzar da tsiro, ya ci gaba da girma har a jima ana shan inuwar shi? 

A gani na sai dai ya bayar da inuwar ta tsayin lokaci, kafin ya bushe, saboda ba a dasa shi ba tun a lokacin da yake a ganiyar ƙurciyarsa ba. 

Da wannan zan iya cewa, dasa mata a lokacin tasowa ta fuskar sana’a ce hanya mafi sauƙi da za a iya taimakon ta da ‘ya’yanta a lokacin da ta fi buƙata.

Dalili kuwa shi ne, a lokacin da ta ke da ƙurciya, babu nauyin kowa kanta, idan ta haɗu da ƙalubalen sana’a, za ta dinga tashi ba tare da wahala ba, ko da kuwa sana’ar ƙarama ce, za ta yi saurin tashi ba tare da dogon suma ba, saboda ba wani nauyi da ta ke ɗauka da ya fi ƙarfinta.

Amma idan ya kasance da girma ta faɗa sana’ar matsaloli irin na rashin sanin makama ga hidimar gida da yara, ga lalurori da aka ɗora kan sana’ar tun kan ta tsayu da ƙafafuwanta, waɗannan kawai sun isa su hana sana’ar tasiri, har a kai ga ta haƙura, ko masu ba ta jarin sun gaji da sunan ba ta san cuwon kanta ba, tana cinye sana’a idan an mata.

To me zai hana su cinye jarin tunda ɗawainiyar yara kawai za ta iya cinye jarin a kwana biyu ko uku. 

Kar na cika ku da surutu, masu karatu, shafin Gimbiya na wannan makon ya karɓi baƙuncin matashiyar da ta soma sana’a tun a lokacin da ta ke a gidan iyayenta, kuma ta ke da burin ta samu mijin da zai bar ta ta nemi na kanta ko da kuwa yana da halin ɗaukar ɗawainiyarta.

Mai karatu, Aisha Asas ce tare da Aisha Kabir Ahmad, wadda aka fi sani da Aisha Tanabiu:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.

AISHA TANABIU: Da farko sunana Aisha Kabir Ahmad, ana kirana da Tanabiu, shekarata 23. An haife ni a garin Kano, unguwar Dandago. Na yi makarantar nursery, primary da sakandare a garin Kano. Na kuma kammala karatun NCE ɗina a makarantar FCE da ke garin Kano a shekarar 2021.

Mece ce sana’arki?

Sana’ata ta asali ita ce siyar da kayan snacks, sai dai zuwa yanzu babu abinda ba na siyarwa.

Idan na fahimce ki kin yi ilimin zamani har matakin NCE. Me ya sa ki ka zaɓi sana’a ki ka bar aiki, ko dai aikin ne bai samu ba?

A’a, Ina sana’a kuma Ina haɗawa da aiki. Ina aikin koyarwa a wata makaranta ta kuɗi, wato private School kenan, kafin a samu permanent. Kuma ko an samu ɗin ba zai hana ni yin sana’a ba, dukka zan haɗa da aikin da sana’a, insha Allah.

Ba mu labarin yadda ki ka faro sana’arki ta farko?

Tun Ina secondary school na ke da son girke-girke, don har na so ace shi na karatsa a higher institution. A lokacin ummana ta ƙi yarda, hakan ya sa na haƙura na fara karatun ENG/SOs a FCE. Ina cikin karatun Allah ya haɗa ni da wata baiwar Allah a Facebook tana sana’ar cakes a shekarar 2020, ta ce, za ta koyamana a kyauta sai dai kawai mu siya kayan kaɗi. Haka kuma akai ta koya mana cake’s Wajen kala goma.

(Aunty Sefsy Allah ya raya mana Amatu). Daga nan na fara yi a gida. Ina gwadawa a Facebook na fara samun first customer da ya yi patronizing dina. Daga nan na fara yin Meatpie a lokacin Ina siyar da shi 150. Har kuma na fi maida hankali akan candies(alawar madara, gullisuwa da kuma iloka). A 2022 na ƙara kawata Meatpie ya zamana Ina siyar da shi akan 300 don mutane sun xɗan fi sanina ma da meatpie akan kakes.

Kin yi zancen wasu sana’oin na daban. Kamar me kenan?

Yanzu haka a ɓangaren abinci Ina siyar da, alkubus, doughnut, gireba, aya mai suga, iloka. Sai ɓangaren kayan kicin komai Ina siyarwa. Haka nan ɓangaren kayan ado na mata da maza.

Ta yaya ki ke cin kasuwar taki?

A online nake samun kaso casa’in bisa ɗari na kwastoma na. Musamman ma a kafar WhatsApp. Na fi son samun customers anan fiye da Facebook.

Me ya sa ki ka zaɓi samun kwastoma a kafar WhatsApp fiye da Facebook?

Saboda na fi tallata kayana a Whatsapp fiye da Facebook.

Wacce shawara za ki ba wa matasan mata kan neman na kai?

Neman na kai a wannan zamani da muke ciki kusan wajibi ne, matuƙar kana son ka guje wa wulaƙanci. Sana’a mutuncin kai ce, komai ƙanƙantar sana’a da ka ke yi za ka yi daraja a idanuwan masu daraja domin sun san ka wuce ‘yar murya. Don haka na ke kira ga ‘yam’uwa mata, mu tashi mu nemi abinda zai kare mana martaba. Babu ƙasƙantatar sana’a, matuƙar ba ta saɓa wa addini ba, domin ƙasƙanci shi ne rashin sana’a ba yin ƙaramar sana’a ba.

Waɗanne irin ƙalubale ki ke fuskanta a kasuwanci a kafafen sadarwa?

Babban ƙalubale shi ne sai kun saba ciniki da mutum sai ya ce, ka ba shi kaya daga baya zai cika ma ka kuɗi amma kuma sai ya hana ka .

Menene alfanun kasuwancin mace a kafafen sadarwa?

Sana’a a kafafen sadarwa sauƙi ne ga mace domin kina daga kwance a ɗaki za ki iya siyar da kayan sana’arki.

Sanar da mu irin nasarorin da ki ka samu a wannan sana’ar da ki ke yi?

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Nasarori kam akwai su. Babban burina dama ace kar ƙannena su ce a gida ayi musu wani abun, ni ma babba da ni na kawo tawa buƙatar. Abinda dai bai fi ƙarfina ba Ina ɗauke wa kaina. Alhamdulillah.

Mata da sana’a; shin dole ne mace ta yi sana’a ko ra’ayi ne?

A nawa ganin dole ne mace ta tashi ta nemi na kanta indai ba roƙo za ta dinga yi ba. Ba wani batun “ai karatu na ke ba sai na yi sana’a ba, ko a gida ana min komai ba sai na yi sana’a ba.” Akwai abubuwan da dole sai dai ka yi ma kanka ba komai ka dinga a bani a bani ba.

Mu koma ɓangaren iyali. Shin kina da aure?

A’a ba ni da aure.

Wasu na cewa, sana’a na ƙara wa mata daraja a idon samarinsu ko mazajensu. Menene naki ra’ayi kan hakan?

Sosai ma kuma domin ko ba komai ya huta da bani da kati ko ba ni da data tunda za ki yiwa kanki ba sai kin jira shi ba.

Idan ya kasance mace ba ta da jari, kuma tana son yin sana’a ta ina za ta fara?

Ta fara samun ilimin ita kanta sana’ar. Daga baya komai zai biyo baya

Duk da cewa ba ki yi aure ba, a fahimtarki rashin sana’a na taka rawa a rashin zaman lafiya a tsakanin ma’aurata ko yaya?

Sosai ma kuwa. Domin yau da gobe sai Allah. Yau kin ce a bani kuɗi kaza zan siya, gobe ma kin ƙara faɗa, hajiyata jibi dole ki ga sauyi. Idan kuwa kina da sana’a yau idan an ba ki, gobe sai ki kawar da kai ki yi wa kanki.

Wane irin miji ki ke burin aure?

Mai addini kuma yana aiki da shi, sannan ya kasance zai so ni fiye da yadda na ke son shi. Wanda zai bar ni na nemi na kaina.

Me ya sa ki ka zaɓe wanda zai bar ki ki nemi na kanki ba wanda zai yi ma ki duk abinda ki ke so ba?

Saboda yau da gobe, ba wanda bai gajiyawa da mutum, sai wanda ya halitta shi. Idan Ina da sana’a zan cike guraben da gajiya da hidimar ta zo masa.

Waɗanne irin ƙalubalai ne ki ka ci karo da su tun tasowa, a matsayinki ta mace?

Alhamdulillah kawai zan iya cewa, domin akwai su kam, sai dai ba za su faɗu ba.

Wane buri ki ke da shi kan sana’ar da ki ke yi?

Babban burin da na ke da shi kan kasuwancin da na ke yi shi ne, Ina so na zama babbar ‘yar kasuwa.

Daga ƙarshe, wane kira za ki yi ga mata ‘yan’uwanki?

Babban kira na ga ‘yan’uwana mata mu tashi mu nemi na kanmu shi ne, mutuncinmu da ƙimar mu a duk inda za mu tsinci kanmu.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.