Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa kotun ta neman kotu ta ba shi damar gabatar mata da sabuwar hujja a kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da bayanan da ya ce ya samo game da karatun da Tinubu ya ce ya yi a Jami’ar Jihar Chicago ta ƙasar Amurka.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar na ra’ayin cewa bayanan bogi ne Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a yayin shiga takara.

Sai dai, Tinubu ya ƙi yarda kotun ta amince da buƙatar ta Atiku, yana mai cewa Atikun ya shigar da buƙatar tasa bayan ƙarewar wa’adin kwana 180 da aka ƙayyade don shigar da duk wata ƙara.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ana ci gaba da shari’ar wadda ake sa ran a yau waɗanda shari’ar ta shafa kowa zai san matsayinsa.