A da ne mata suka fuskanci ƙalubalai a aikin jarida – Khadija Salihu

“Girki na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure”

Daga AISHA ASAS

Masu karatunmu Allah Ya kawo mu, sati ya zagayo, sannunku da ƙoƙarin bibiyar jaridar Manhaja. Shafin Gimbiya mai kawo maku fira da mata daban-daban kan sha’anin rayuwarsu, tun daga sana’o’insu ko ayyukan da suke yi, zuwa ƙalubalai da kuma nasarorin da suka samu.

Shafi ne da ke ƙoƙarin ganin ya zama allon kallo ga mata, ta hanyar zaburar da su kan neman na kansu, taɓo ɓangarorin da za su share hawayen wasu mata su fahimci ba su kaɗai ne ke fuskantar matsalolin da suke ciki ba, kuma ilimi gare su mata, ta hanyar amfani da matakan da baqin namu ke bi wurin shawo kan matsalolinsu ko sana’o’insu da sauransu.

A wannan satin, mun samu baƙuncin matashiya mai sana’ar kayan ƙwalama, wato snacks da kuma kek na zamani. Matashiyar da ta haɗa ɓangarori biyu, wato ilimin sana’a da kuma na zamani.

A tattaunawar Manhaja da ita, za ku ji yadda ta yi zurfi a ilimin boko, da yadda hakan bai hanata neman na kanta a ɓangaren sana’a ba, duk da cewa ba wai ba ta sha’awar aiki ba, sai dai kallon sana’a da ta ke yi a matsayin abokiyar rayuwa da kowa ya kamata a ce yana yi.
Mai karatu, gyara zama, domin Aisha Asas ce tare da Khadija Salihu Yusuf:

MANHAJA: Za mu so jin tarihin rayuwarki.

KHADIJA SALIHU: Sunana Khadija Salihu Yusuf, an haife ni a garin Kano, Dala lga. Na yi primary da secondary school ɗina a nan Kano daga nan na tafi B.U.K, na yi digiri na a Mass Commication, wato aikin jarida. To kuma daga nan aka fara gwagwarmayar rayuwa.

Wacce alƙibla gwagwarmayar ta fuskanta, sana’a ko aiki?

Gaskiya dai yanzu sana’a aka sa gaba.

Ba mu labarin irin sana’ar da ki ke yi.

Ina sana’ar siyar da ‘cake’, ‘desserts’ da kuma ‘snacks’.

Me ya sa ki ka zaɓi sana’ar a cikin dubban sana’o’in da mata ke yi?

Eh to, gaskiya zan iya cewa soyayyata ga kek (cake) shi ya sa na fara wannan sana’a, saboda na kasace Ina son cin ‘cake’ sosai, har ya kasance idan na gan shi ko a hoto anyi masa ado yana yimun kyau sai na ji ni ma Ina son naga na fara wannan sana’a.

Ita wannan sana’a da ki ke yi ta girke-girken kayan maƙulashe, ko ana zuwa koyonta ne, ko kuwa da ka ake yi?

To kinsan idan har za ka fara sana’a kowacce iri ce kana so ka fara ta bisa tsari da kuma ilimi, wanda hakan zai sa ta yi kwarjini a idon mutane. To kuma hakan ba za ta kasance ba har sai ka neman ilimin wannan abin da ka ke so ka fara a wurin waɗanda suka iya shi, domin aka ce wanda ya riga ka kwanciya, dole zai riga ka tashi. Hakan zai taimaka ma kasan ta inda za ka fara. Don haka ni ma kaina sai da na je na koya wanda har yanzu ma ina ƙara koya. Tabbas ana zuwa koyan ta kamar yadda ake iya koyon kowanne daga cikin girke-girken da ake yi. Ni ma karan kaina sai da na je koya a wurin wata ƙawata.

Bari mu koma ɓangaren karatun da ki ka yi, wato na aikin jarida. Shin kin karance shi ne don sha’awar yin aikin na jarida ko ya abin yake?

Haka ne, a ɓangarena na karanta aikin jarida saboda gaskiya Ina son aikin jarida sosai. Gaskiya tin ina ƙarama Ina sha’awar aikin jarida sosai, wanda shi ya sa na yake hukuncin karantar sa a jami’a wanda kuma cikin hukuncin ubangiji na samu na yi karatun.

Wasu daga cikin mata musamman na Arewa na fuskantar matsaloli idan suka shiga aikin jarida, wanda hakan kan iya zama wata manuniya ga wasu masu karatun wannan ɓangaren da zai sa bayyan sun kammala su gujewa aikin. Ko hakan ta kasance gare ki?

Gaskiya dai ni hakan ba ta taɓa kasansewa tare da ni ba, domin dai ni ko yanzu na samu aiki da ya shafi aikin jarida a shirye nake da na yi, saboda Ina so naga Ina ‘practicing profession’ ɗina.

Ko za mu iya jin ta bakinki kan dalilin da ya sa wasu mata ‘yan jarida ke fuskantar ƙalubalai a aikin?

Ni dai a ganina a zamanin baya shi ne mata suka fuskanci ƙalubale sosai a wurin aikin jarida, amma a hankali kai yana wayewa za ki sami mata sun tsunduma cikin wannan aiki sosai saboda za ki ga duk wani wuri na aikin jarida maza da mata ne ke aiki a wurin, saboda kai ya waye su ma matan an ba su dama wannan ‘mentality’ ɗin na cewa mata baza su iya aikin ba ya zama tarihi yanzu.

Ba mu labarin yadda ki ke gudanar da kasuwancin naki.

Ina gudanar da kasuwancina yawanci ta yanar gizo ne, duk wanda yake so wani abu da nake siyarwa zai kirani ko yayi min magana a shafukana na sada zumunta, su zavi abinda suke so, su biya kuɗin abin, ranar da za su karɓa su zo su karɓa ko kuma ayi musu ‘delivery’, wato a kai masu har gida. Wasu lokutan kuma zan tallata cewa zanyi wani abu ranar kaza misali, na tallata a yanar gizo cewa zanyi cake ‘slice’ ranar Asabar Naira 100 mai so zai yi min magana, ya turo kuɗinsa ranar da na yi sai ya karɓa.

Waɗanne irin ƙalubale ki ke fuskanta?

Rayuwar ma dai gabaɗaya ƙalubale ce ai, amma dai babban ƙalubalen da nake fuskanta a wannn lokacin bai wuce hauhawan farashin kayayyakin aiki ba. Yau idan ka siye buhun fulawa 200 gobe idan ka koma ya tashi yakoma 1000, da kuma rashin jari mai yawa wanda za ka iya siyan kayan aikin da yawa ka ajiye izuwa wani lokaci mai tsawo.

Sanar da mu nasarorin da ki ka samu ta hanyar sana’a?

Gaskiya an samu nasarori da yawa sai dai na ce, Alhamdulillah. Ma sha Allah, tin da dai Ina iya biya wa kaina buƙatu da yawa har da wasu ma, kuma akwai manyan mutanen da ko a mafarki ba na tunanin akwai wani abu da zai haɗa ni da su, amma ta sanadiyar wannan sana’a mun haɗu kuma sun siye abinda nake siyarwa har kuma su turo wani nasu ma su siya.

A taki fahimta, a wannan lokacin da muke ciki, sana’a dole ce ga ‘ya mata ko abar sha’awa?

Gaskiya dai ni a fahimtata a wannan lokacin da muke ciki sana’a fa ga mata kawai ta zama dole ce, domin mu mata Allah ya yi mu da hidindumu masu yawa ko kina da mahaifi mai kuɗi, ko miji mai kuɗi, za su gaji da kullum sai dai kice a baki, amma idan kina da sana’a fa za ki biya wa kanki buƙatu da yawa ba tare da wani ma yaji ba.

Sanar da mu muhimmancin girki ga matar aure?

To shi dai girki abokin rayuwa ne saboda indai da rai da lafiya za a ci abinci saboda haka iya girki yana taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure sosai, kuma gaskiya dole a dinga samun matsala tsakanin ma’aurata idan har matar ba ta iya girki ba.

Wane kira ki ke da shi ga matasan mata kan neman na rufa wa kai asiri?

Kiran da zan yi gare su shi ne, wallahi su farka su tashi su nemi na kansu, yin sana’a yana hana abubuwa da yawa fa kamar zaman banza, faɗa, munafunci, tunani mara amfani, saboda a kullum lissafinki ta yaya za ki mayar da 5 ta zama 10 ne.

Su kuma matan da ke zaman kashe wando, wane kira za ki yi gare su?

Matasan mata ku dage ku dinga neman na kanku idan har kuna yi to kun wuce wargi, wallahi babu wani namiji da zai zo ya ce, zai ruɗe ku da kuɗi ko wani abin duniya tunda duk abinda ki ke so kina sana’a za ki iya yiwa kanki, to sai kuma me ya rage? babu.

Wasu na ganin macen da ba ta iya girki ba auren bai cika zaman lafiya ba, wasu ma na ganin bai cika tsawon rai ba. Shin menene gaskiyar zance?

Girki yana taka muhimmiyar rawa a rayuwar zamantakewar aure kamar yadda na faɗa a sama, saboda zan iya cewa yana cikin sahun farko na zamantakewar aure gaskiya, kamar yadda bature yake cewa “the way to a man’s heart is through his stomach,” wato hanyar isa ga zuciayar namiji ita ce cikinsa. Ciki bai samu abinda yake so ba to kuwa Ina batun wata soyayya.

Mu koma vangaren iyali. Kina da aure?

Eh Ina da aure, amma ban haihu ba tukunna.

Mata da kwalliya aka san su aka ce. Menene naki ra’ayi game da kwalliya?

Wannan gaskiya ne, ita mace ai ‘yar kwalliya ce. Mace da kwalliya aka santa, saboda haka kwalliya ita ce mace.

Idan aka ce kwalliya me ake nufi?

Ni dai a wurina idan aka ce kwalliya ba wai ana nufin a shafa ‘powder’, ‘foundation’, ko janbaki, ko kuma kwalli ba ne kaɗai kwalliya ba. Mace ta tsaftace jikinta da kayanta shima duk yana cikin tsarin kwalliya.

Wane irin abinci ne ya fi birge ki?

Gaskiyar Ina son shinkafa da wake sosai. Ni abinci indai da mai da yaji ne to yana burge ni sosai.

Sanar da mu irin kwalliyar da ki ka fi son ki yi.

A kwalliyar fuska na fi son ɗan ‘simple makeup’, hoda, kwalli da ‘lip gloss’. Kwalliyar jiki kuma Ina son sa atampa da abaya.

Mun gode.

Ni ma na gode.