Ministan Labarai ya buƙaci NBC ta gyara ɗamararta

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa, NBC, da ta sako masu ruwa da tsaki cikin harkokinta domin binciko kafafen da ke saɓa dokar yaɗa labarai.

Idris ya yi wannan kira ne yayin ziyarar aikin da ya kai babban ofishin hukumar da ke Abuja.

Ya ce akwai buƙatar NBC ta gyara salon aikinta maimakon ƙaƙaba takunkumi da tarar da takan yanka wa kafafen da ta samu da take doka.

Ya ce, “Ban yarda cewa ƙaƙaba takunkumi shi ne kaɗai abin da NBC ta sani ba. Duk lokacin da aka ji NBC a labarai bai wuce ta ƙaƙaba wa wata kafa takunkumi saboda take doka ko makamancin haka.

“Ina ganin lamarin ya wuce gaban haka, ya kamata mu duba, akwai buƙatar wayar da kan al’umma. Game da haka, ina ganin ba a wayar da kan al’umma yadda ya kamata ba.

“Akwai buƙatar wayar da kan jama’a don a ƙara fahimtar ayyukan NBC. Domin kuwa, jama’a kan ji NBC ne kaɗai idan da batun ƙaƙaba takunkumi.

“Yana da kyau NBC ta fito da wani tsari don fahimtar da jama’a kan cewa ƙaƙaba wa tasha takunkumi ba shi ne aikinta kawai ba, a san cewa hukumar ma na da haƙƙin taimaka wa kafafen yaɗa labarai su bunƙasa.

“Na san kuna bakin ƙoƙarinku, amma akwai buƙatar a ƙara himma, ta haka ne ‘yan ƙasa za su riƙa yi muku kallon abonkan hulɗa.

”Ba a yi la’akari da wasu abubuwa ba a lokacin da aka kafa hukumar, don haka akwai buƙatar a yi wa dokar hukumar kwaskwarima,” in ji Ministan.

Da yake maida jawabi, Darakta-Janar na NBC, Balarabe llelah, ya ce hukumar na da ofisoshi 28 a jihohi sannan ofishin shiyya guda 10 da kuma ma’aikata 419.

Ya ƙara da cewa, tashoshi sama da 777 hukumar ke sanya wa ido a faɗin ƙasa. Ya ce, 609 daga adadin gidajen rediyo, sannan 168 gidajen talabijin.