Gwamna Lawal ya bada tabbacin tallafa wa makarantun sojoji a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada aniyarsa ta tallafa wa makarantun sojoji da ke faɗun jihar.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban makarantar sojoji ta Nigerian Army Education Corps (NAEC), Manjo Janar Bello Alhaji Tsoho, a Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce Shugaban makarantar ya kai ziyarar ne domin ƙarfafa alaƙa tsakanin makarantar da Gwamnatin Zamfara.

Idris ya ƙara da cewa, Kwamandan ya nemi goyon bayan gwamnatin jihar kan ci gaba da kafa makarantun sosjoji a jihar.

A cewarsa, “Gwamna Lawal ya ƙarfafa kan cewa fannin ilimi shi ne fannin da wannan gwamnati ta fi bai wa fifiko. Gwamnati na yin bakin ƙoƙarinta wajen bunƙasa fannin.

“Gwamnan ya bai wa Kwamandan tabbacin zai bada gudummawa gwargwadon hali ga makarantun sojojin da ke Gusau da Talata Mafara.

“Ya kuma yi alƙawarin sanya hannun kan yarjejeniya a wannan makon domin ɗaukar nauyin ‘yan asalin jihar shiga makarantun sojoji da kuma gudanar da ayyukan more rayuwa,” in ji Idris.

Tun farko, Manjo Janaral Bello Alhaji Tsoho, ya ce Gwamnatin Zamfara ta kama hanyar bunƙasa makarantun sojoji. Yana mai cewa in ban da Zamfara babu wata jihar Arewa da ke da irin waɗannan makarantu.

“Na zo ne domin duba makarantun sojoji, ganawa da kuma assasa alaƙa da Mai Girma Gwamna da ma Gwamnatin Zamfara,” in ji shi.