Abin da ya sa ban damu da saka fitattun jarumai a finafinaina ba – Kabiru Musa Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Bayan tsawon lokacin da ya shafe ba tare da ya fito da sabon fim ba, fitaccen furodusa Kabiru Musa Jammaje, wanda ya saba shirya finafinai da harshen Turanci a masana’antar Kannywood. A yanzu haka dai ya ci gaba da shirya sabon fim ɗin sa mai suna ‘Princess of Galma,’. Wakilinmu ya tattauna da shi a game da yadda aikin fim ɗin yake da kuma manufarsa ta shirya wannan sabon fim ɗin, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance

MANHAJA: Kai ba sabo ba ne a cikin harkar fim a wannan masana’anta ta Kannywood, amma dai an ɗan samu lokaci ba ka fito da sabon fim ba, sai a yanzu da ka shiga wannan aikin.

JAMMAJE: To shi wannan aikin na ‘Princess Of Galma’, da ma can akawai labarin da aka rubuta shekarun baya, to sai Allah ya sa ba a yi shi ba sai yanzu. Amma dai yanzun ba wancan labarin ba ne, wani labarin ne daban, sunan ne ɗaya, wannan Hussaini Ali ne ya rubuta shi, labarin sa ne, kuma Muhammad Galadima shi yake bayar da Umarni, kuma Alhamdulillahi ga shi mun shiga aikin, komai yana tafiya daidai.

Amma dai asalin labarin shi ne na wata gimbiya ce Nafisa wacce take da mahaifi ya tsufa, sai a ke tsoron kada ya mutu ya rasa magaji, kuma kamar yadda al’adar masarautar Galma take, idan sarki ba shi da da namiji, ‘yarsa za ta auri wani, kuma wanda ta aura ɗin shi ne zai zama sarki, a haka sai ya zama duk wanda ya zo wajenta da nufin neman aure ba ta sauraron sa. To kuma sai ya zama a mafarki ne take haɗuwa da wanda take so. A cikin mafarkin suke haɗuwa su yi soyayya har su yi aure. Kuma dai wannnan wani salo ne da muka zo da shi da zai iya zama baƙo.

Kamar yanzu yadda aka sauya harkar fim a Kannywood, zuwa yin finafinai masu dogon zango. Shi ma ‘Princess of Galma’ fim ne mai dogon zango?

A’a shi ba mai dogon zango ba ne, fim ne mai gajeren zango kamar yadda aka saba na tsawo sa’a biyu, kuma tsarin sarauta ne ta Bahaushe, amma ta zamani ba ta da can ba, kuma mun yi tsari na ƙirƙrar wata masarauta ne mai suna Galma, don ba za mu ce Kano ko Katsina ko Zaria ba. Mun ƙirƙiro ne kawai, amma dai za a iya ganin wasu abubuwa da suka yi kama da na masarautun wannan kuma ƙoƙarin da muka yi ne wajen samar da fim ɗin da ya dace da tsarin masarautunmu na Ƙasar Hausa, amma dai sunan Galma, babu wata masarauta da take da wannan sunan.

To ganin yanzu an samu sauyin kasuwar fim ɗin Hausa, ko wacce kasuwa za ka ci da wannan fim ɗin idan ya kammala?

E shi wannan fim ɗin za mu nuna shi ne a sinima a Kano, in Allah ya yarda, duk dai sinimar Shooprita yanzu babu ita, amma dai akwai wadda za mu nuna fim ɗin a cikin ta. Sannan kuma muna ƙoƙarin samar da wata cibiya ta kallon fim, wadda ko da ta wucin dagi ce za a yi don a kalli wannan fim ɗin idan Allah ya yarda zuwa ƙarshen wannan shekarar zuwa watan Disamba kenan. Sai kuma gidajen TV da za mu kai, kuma idan hali ya yi ma sai ka ga mun tsallaka mun je wani dandamali da a ke da su a Intanet, za mu kai musu, idan an yi sa’a sai a karɓa. Kuma kamar yadda aikin yake tafiya, muna fata in sha Allah zai fitar da mu kunya.

Finafinan ka ba ka cika saka su a YouTube ba. Ko me ya sa ba ka yin hakan?

To ni dai abin da ya sa ba na saka finafinai na a You Tube, saboda ba wani abu na ga ana samu sosai ba, ko da wasu su na ganin ana samu, to ni ban ga wani samu da ake yi sosai ba. kuma shi ne kamar mataki na ƙarshe a sakin fim, sai ka je ka kai shi ko’ina ka gama cin kasuwar sa, sai ya zama You Tube shi ne waje na ƙarshe, ya zama kamar ka jefar da fim ɗin ka ne a wajen.

Zuwa yaushe ka ke ganin za a fara kallon ‘Princess of Galma’ bayan an kammala aikinsa?

Da yardar Allah zuwa nan da Disamba, lokacin da a ke bukukuwan ƙarshen shekara kamar dai yadda na saba sakin finafinaina a baya.

Ko me ya bambanta wannan fim ɗin na ‘Princess of Galma’ da sauaran finafinan da ka saba yi a baya?

Na farko dai kayan aiki ya bambanta su, saboda ci gaban zamani, sai kuma yanayin labarin, da ma yanayin yadda a ke ɗaukar fim ɗin ma. Aiki ne da ba ya yin sauri, amma za ka ga ana ɗaukar sa da kyau.

Ba ka cika saka fitattun jarumai a fim ɗin ka ba, ko a wannan ma haka ne?

Haka ne. Ni yanzu ban duba da fitattun jarumai ba, kawai jarumin da zai iya taka rawar da zai iya, shi na ke ɗauka ko da ba a san ka ba. Kuma ka ga akwai jarumai da yawa a cikin fim ɗin waɗanda mu muka yaye su a makarantarmu ta Jammaje Academy ‘yan ajin koyon aktin, to da yawansu su na cikin wannan aikin, kuma wannan shi ne ma babban abin da ya ƙarfafa mini na yi wannan aikin, domin na ba su ƙarfin gwiwa don haka ɗaliban mu ne, da yawansu mu muka samar da su a makarantar Jammaje Academy, sai kuma wasu jarumai sanannu da muka ɗakko daga Kannywood kamar Magaji Mijinyawa na ‘Gidan Badamasi’ da ya fito a matsayin sarkin, ita ma sarauniyar ta yi finafinai amma dai ba sosai ba, kuma muna fatan wannan fim ɗin zai ƙara haskata.

Wanne saƙo ka ke da shi ga jama’a?

To saƙon da nake da shi, baya ga wannan an ɗan ji mu shiru ba mu yi fim ba. To na tafi ne ina buɗe rassa na Jammaje Academy a jihohin Arewa da ma ƙasar bakiɗaya. A yanzu kusan a kowacce jiha a Arewa muna da reshe, don haka a yanzu na gama da wannan, na kuma dawo harkar fim, don haka bayan wannan ma akwai wasu da za su biyo baya. Muna fatan Allah ya ba mu nasara.

Madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.