Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure

Tare da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A wannan mako zan so na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta bayan rabuwar aurensu. Da farko dai wacece bazawara?

Bazawara ita ce wacce ta rabu da mijinta ta hanyar sakin aure ko kuma wanda ya mutu, ko ma wanda ya vace. Ƙasar Hausa kamar yadda muke gani a halin yanzu, ta zama tamkar shalkwatar yaye ƙanana da manyan zawarawa har ma da dattijai. Ba sai na kawo dalilan da suke jawo yawaitar mace-macen aure a ƙasar Hausa ba a cikin wannan rubutun.

Amma insha’Allah ina da niyyar kawowa a wani rubutu a gaba. Amma abinda za mu lura shi ne, mutuwar aure ta yawaita sosai a ƙasar Hausa. Ta yadda da wuya ka iya nuna wani mutum guda wanda zai iya bugar ƙirji ya ce ba bazawara a danginsu ko guda ɗaya. To ba wani abu nake son faɗa a wannan mako ba illa yadda zawarci ya zama dandalin bajekolin fitsara a wajen wasu mata. Da kuma barazanar da yake haifarwa.

A ƙasar Hausa da zarar an ce ga bazawara, maza marasa kirki sun yi rubdugu don kawai su a wajensu garaɓasa ta samu.

Haka wasu matan marasa kirki. da zarar mace aurenta ya mutu ko mijinta ya mutu, wata ba ta bari ta ƙarasa ko iddarta ba ma sai ka ga ta ɓalle da bushasha. Tuni su ma ƙadangarun bariki kamar da ma kaɗan suke jira. Sai a zo a yi mata rubdugu kamar Allah ya aiko su.

Wasu su zo da niyyar fasiƙanci sak, ta hanyar amfani da damar cewa yanzu fa tana cike da kewar namiji. Wasu kuma su zo da sigar nuna mata kuɗi da abin Duniya, idan kwaɗayayya ce kun ga ai sai ta afka. Wani kuma da niyyar aure zai zo mata, amma sai ya yi amfani da son auren da take yi ko son da take yi masa ya shigar da buƙatarsa. Kafin ka ankara sai ka ga matar da take kamilalliya mai tsoron Allah lokacin da tana gidan miji, yanzu ta zama tantiriyar ‘yar Duniya ta buga misali. To me yake jawo haka?

*Kwaɗayi: Wasu matan akwai kwaɗayi da son burga da gasa da ƙawaye. So suke su haɗa kansu da sauran ƙawayensu ‘yammata da zawarawa masu kuɗi ta fuskar kwalliya da ado da sauran abubuwan rayuwa. Sai dai kuma ita ba sana’a ko nema ta iya ba. Don haka, za ta yi ƙoƙarin yadda za ta samu kuɗaɗen yin bushasha don burga. Shi ya sa sai ka ga sun fara bin mazajen banza don su samu kuɗaɗen da za su biya waɗancan buƙatun nasu. A haka bazawara ko ta Allah ce, kwaɗayinta zai sa su kuma mazajen su yi amfani da damarsu don ganin an yi ban gishiri, in ba ki manda. Daga nan kuma idonta ya buɗe, wata ko aure sai ta ƙi yi saboda bariki ta riga ta buɗe mata ido. Tana ganin ta riga ta rungumi a binda ya fi aure a hannunta. Amma ‘yaruwa kina tuna tsufa kuwa? Lokacin da kyawunki da surarki ba za su birge su waɗancan ƙadangarun barikin ba? Sannan kina tuna mutuwa da makomarki bayan kin mutu. Haka kada ki manta ko bayan mutuwa kin bar zuriya a baya. Wanne tarihi kika bar musu wanda da su da sauran al’umma za su tuna ki da shi?

*Rashin kulawa daga tsohon miji ko danginsa. Mun zo zamanin da da zarar an saki mace to har yaranta ma an saki. Sai ka ga ubansu ko danginsa dukka ba abinda ya sha musu kai da yaranta ko ita. Wata ma mijin mutuwa ya yi. Kuma ba lallai ne kowanne mutum idan ya mutu a ce ya bar wa iyalinsa wani abu ba. Amma sai ka ga gabaɗaya dangin uba saboda rashin zumunci an watsar da yaran ɗanuwansu. Wannan uwar idan iyayenta ba su da qarfi haka za ta yi ta faɗi-tashi tana samar da abinda za su rayu tare da yasnta. Ga ci da sha, sutura, ilimi, lafiya da sauransu.To irin waɗannan mata idan ba a samu masu tsoron Allah ba, ai ba hanyar da ba za su bi don samar wa yaransu rayuwa ba, ko halas ko haram. Zawarawa da dama sun afka cikin irin wannan ƙangi na rayuwa. Sai ka ga mazajen banza sun yi amfani da wannan raunin sun yi alƙawari fitar da ita daga ƙangi idan har ta amince da su. Kuma ba kowacce ke iya tsallake wannan siraɗin ba. Kuma daga ta fara su ɗaya, ta tsaga ta ga jini, shikenan. Da wuya ta daina idan ba ikon Allah ba.

*Wasareren iyaye: Iyaye suna mantawa tare da wasarere da ɗiyarsu mace bazawara. Sun manta ita tana jin tana da lasisi za ta iya aikata dukkan abubuwan da budurwa ba ta ƙoƙarin aikatawa. Shi ma wannan rashin sa idon na saka zawarawa cin karensu babu babbaka. Ya kamata iyaye su kula da haka. Sannan su tallafa mata.

Za mu cigaba a mako na gaba in rai ya kai.