Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya, wanda ya rubuta fiye da littattafai (400) na addinin Musulunci da hannunsa.

Malamin, wadda jigo ne a ɗarikar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Fatawa da Al’amuran Musulunci a Nijeriya (NSCIA).

Malamin ya kasance ɗan ƙabilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da suka haɗa da; Makka, da Madina, da Masar, da Pakistan, da Iran, Senegal da sauran su, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Al-Ƙur’anin nan Mahmoud Khalilul Khusari, a Masar.

An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini, CON, a daren ranar Asabar, 12 ga Mayu, 1938, a Aredibe, wani qauye kusa da Dikwa a Jihar Borno, da ke Arewa maso gabashin Nijeriya.

Mahaifinsa, Sheikh Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawy, shahararren malamin addinin Musulunci ne da ya yi fice a fagen ilimin addinin Musulunci.

Mahaifiyarsa Fatima bint Sheikhh Muhammad Al-Bashir Al-Hussaini, mace ce mai yawan karamci da tsoron Allah (SWT), sannan ta kasance abar girmamawa ga kowa a cikin al’umma.

Ta kasance mai ladabtarwa mai kuma tsananin sha’awar ilimi. Da yake mijinta ya rasu sa’ad da ɗansu yake ɗan shekara bakwai kawai, ta karvi horonsa har ya girma.

Babu shakka ita ce ta kasance mafi girman tasiri a rayuwarsa, da ta sa a yau Sheikh Ibrahim Saleh ya zama babban malami a duniya.

Misali, ta tava qin amincewa da shawararsa ta yin watsi da neman ilimi maimakon cinikin dabbobi, lokacin ya na ɗan shekaru goma sha biyar kacal.

Shakka babu, ta taka rawar gani wajen tabbatar da Sheikh Ibrahim Saleh bisa gwadabe madaidaiciya.

Sheikh Ibrahim Saleh, ya fara koyon Al-Ƙur’ani mai girma tun ya na ɗan ƙaramin yaro, in da koyaushe yake kasancewa tare da mahaifinsa, wadda ya kasance mafi yawan dararen sa ya na gabatar da sallar nafila (nawafil).

Wannan ne ya sa ya fara haddace ayoyin Al-Ƙur’ani tun kafin ya shiga makaranta gadan-gadan. Sau da dama, ɗaliban da ke karatu a wurin mahaifinsa na yawan mamakin irin ƙoƙarinsa da basirarsa sakamakon yadda yake cin su gyara a karatu duk da sun sha gaban sa.

Ya kuma fara karatunsa a makarantar mahaifinsa, ɗaya daga cikin shahararriyar makarantun islamiyya a Borno a lokacin.

Daga shekarun 1944 zuwa 1964, ne lokacin da Sheikh Ibrahim Saleh ya yi gwagwarmayar ganin ya yi tasiri a fagagen karatun Al-ƙur’ani da ilimin addini, da kuma sauran vangarorin ilimi da suka haɗa da kimiyyar lissafi, da falsafa da balagar harshe, da sauran wasu littattafai.

Bincikensa na neman ƙwarewa a ilimin Al-ƙur’ani ya fara ne a gida, wadda daga baya ya koma zuwa wasu fitattun cibiyoyin ilimi waɗanda aka fi sani da “Tsangayu” a Maiduguri da kewaye.

Ba da daɗewa ba shahararsa ta ɗaukaka a fannin karatun Al-ƙur’ani a duk wuraren da ya yi zamansa don neman ilimi, kamar: Tarmuwa, Gulumba, Gide, Maishumari da kuma Maiduguri.

Ya kasance mai sauƙin sha’ani, har ma ga malamai wadda ya haɗu da su a karon farko, sakamakon kyawawan ɗabi’unsa, ladabi da biyayya, da zurfin karatunsa da kuma saninsa a cikin karatun Al-ƙur’ani.

Akwai malamai da dama da suka yaba da ƙoƙarin Sheikh Ibrahim Saleh, tun ya na ƙaramin yaro kuma a matsayin ɗalibi, tare da yi masa kyakkyawar fahimta da cicciɗa shi domin kai wa ga tudun tsira a lokacin da yake tasowa a matsayin ɗalibi.

Akwai irin su; Sheikh Muhammadul Habib jikan Sheikh Ahmad Al-Tijjani (Abul Abbas) a ziyarar da ya kawo Maiduguri daga Aljeriya, Sheikh Muhammad Mustafa Alawi, Sheikh Al-kadi Lari Abani, Sheikh Mustafa Birshi, Sheikh Ahmad Ali Abulfathi, Sheikh Gibrima Dagira, Sheikh Tijjani Usman, Sheikh Abubakar Atiku da wasu da dama.

Sheikh Ibrahim Saleh, ya shafe shekaru 20 ya na neman ilimi a matsayinsa na ɗalibi, kuma ya koyi kusan dukkan karatunsa a Najeriya, amma ba hakan ke nufin duka malamansa ’yan Nijeriya ba ne.

Ya kuma karanci harshen Turanci a birnin Landan.

Karatun Sheikh Ibrahim Saleh, ya fi ƙarfi a ɓangaren Hadisai da Usulul Fiƙihu da Ilmul Kalam, da kuma Tafsiri. Misali, duk wata aya daga cikin Al-ƙur’ani idan aka ambato ta, malamin zai iya faɗin idan ta na da alaqa da wani hadisi a tattare da ita. Malamin ya kuma yi nisa ƙwarai a karatun Tauhidi da Fiƙihu.

Wasu daga cikin malamansa su ne; Sheikh Al-Qadi Abanj Borno, da Sheikh Abubakar al-Waziri Borno, da Sheikh Adam al-Mahrusa Borno, da Sheikh Ahmad Abulfathi, da Sheikh Tijjani Usman (Zangon Barebari), da Sheikh Abubakar Atiku Sanka Kano, da Sheikh Muhammad al-Arabi bin Kubbani, da Sheikh Abubakar al-Kashnawiy, da Sheikh Muhammad al-Hafiz, da Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hussary, da Sheikh Ahmad Nur al-Barni, da Sheikh Muhammad Zakariya al-Kandahlawiy, da Sheikh Ibrahim Nyass Kaolac, da sauran su.

Ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin ilmantarwa mai inganci da Sheikh Ibrahim Saleh ya gano tun da wuri shi ne, duk ɗalibin da ke son zama malami, dole ne ya zaqulo wasu nau’ikan malamai daga cikin al’ummomin da suka gabata, kuma ya yi ƙoƙarin koyi da su.

Daidai da wannan dabara, ya tashi don yin koyi da tsara rayuwarsa a cikin tsarin Al-Ghazali. Al-Hafiz bin Hajaral Asƙalani, dangane da Hadisi; da Abdulwahab Sha’arani, ta fuskar samar da ilimi da dama, da kuma gwargwadon ƙoƙarin sauran malamai na wannan zamani.

Tasirin waɗannan manya-manyan malaman Musulmi a rayuwar Sheikh Ibrahim Saleh ya haskaka.

Ba kamar yawancin mutanen zamaninsa ba, Sheikh Ibrahim Saleh ya kiyaye rashin kwanciyar hankali a tsakanin tsarin zamani na neman ilimin addini, da kuma rungumar al’adar Musulunci da ta daɗe ta na tantancewa da ba da shaida ga malamai.

Ana cikin haka ne yunƙurin da ya yi na kwatanta rubuce-rubuce da sauran malamai, da kuma miƙa kansa gare su domin a yi musu bincike mai zurfi, ya kai shi manyan cibiyoyi masu daraja ta ilmin addinin Musulunci da ilmantarwa a Nijeriya da ma nahiyar Afirka.

Misali, a shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya tafi qasar Saudiyya a karon farko da nufin yin aikin Hajji da kuma samun takardar shaida (ko ijaza) a fannin Hadisi da karatun Al-ƙur’ani da sauran rassa na ilimin addini.

Ya gana da wasu daga cikin manya-manyan malamai da ake girmama su da kuma sanin su a fagage kamar: Sheikh Umar bin Ali Al-Faruq Alfullati, Sheikh Alawi bin Abbas Al-Maliki, Sheikh Muhammadul Arabi Al-Tubbani da Sheikh Hassan bin Ibrahim Al- Sha’ir. Duk sun same shi ya isa ya mallaki takardun shaida. Haka zalika, a qasar Masar, Sheikh Ibrahim Saleh ya samu amincewar da ta dace a fagen Hadisi daga Sheikh Muhammadul Hafiz, da sauran fagagen da suka haɗa da karatun Al-kur’ani daga Sheikh Mahmud Khalil Al-Husari da Sheikh Amir bin Usman Al-Sayyid.

Sauran malamansa da suka ba da shaidar ƙwarewarsa a fannin Hadisi sun haɗa da; Sheikh Ahmad Nur Al-Barmi daga Pakistan, Sheikh Muhammad Zakariyya bin Yahya Al-Khan Dahlawi daga Indiya, da kuma shahararren malami kuma jagoran ɗarikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Nyass daga Senegal.

Za mu cigaba a mako mai zuwa.