Rayuwar ‘yan matan Arewa a Tiktok

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na daɗe ina son na yi wannan rubutun domin jan hankali da faɗakarwa ga al’ummarmu ta Arewa musamman iyaye da ’yan mata game da wasu abubuwa da ke faruwa, amma wasu dalilai suna sa ina jinkirtawa, sai a wannan karon da batun wata yarinya mai suna Rahama Sa’idu da ta yi karatu a Kwalejin Koyar da Aikin Jinya ta Jihar Kebbi ya taso, inda rahotanni ke cewa wai hukumar gudanarwar makarantar ta kore ta saboda rashin mayar da kai a karatu da sharholiyar da aka ce tana yi a manhajar Tiktok.

Kodayake wata majiya ta bayyana cewa hukumar makarantar ta musanta zargin cewa ta kori Rahama ne saboda alaƙarta da Tiktok, sai don ta kasa samun makin da ake buƙata kafin a tsallake zuwa mataki na gaba, da kuma rashin zuwanta makaranta.

Tun kafin wannan batu na Rahama ya kunno kai, jama’a da dama ke bayyana ra’ayoyinsu bisa yadda rayuwar matasan Arewa a manhajar Tiktok ta ke neman wuce makaɗi da rawa. Saboda irin fitsara da abubuwan rashin kunya da wasu ke yi, musamman ‘yammata, da za ka ga sun dage suna tiƙar rawa ana murguɗa jiki da karkaɗa nonuwa da sunan nishaɗi ko neman suna da magoya baya. Sau da yawa ma za ka gansu cikin sutura ta rashin tarbiyya da fitsara iri-iri kai ka ce ba ‘ya’yan Musulmi ba ne, ko kuma basu da iyaye ko ’yan uwa da za su tsawatar musu.

Za ku iya tunawa a shekarar 2022, wata kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta tava ɗaure wata fitacciyar mai bidiyon barkwanci da rawar banjo a manhajar Tiktok, mai suna Murja Ibrahim Kunya tare da wasu abokan tambaɗarta bisa laifin vata tarbiyya da yaɗa maganganun batsa da suka savawa al’adu da koyarwar addinin Musulunci, wanda akasarin al’ummar Kano ke bi.

A farkon wannan shekarar ma sai da Hukumar Hisbah ta Kano ta ba da sammacin kama wata matashiya Hafsa Fagge da ta yi ƙaurin suna wajen yaxa bidiyon batsa da rashin kunya, bayan wasu matasa Ashiru Idris Mai Wushirya da Aminu BBC, da Sadiq Shehu Shariff da aka yankewa hukuncin sharar harabar asibitin Murtala da masallaci, da bulala, bisa abubuwan rashin kunya da suke yaɗawa.

Abubuwan takaici da ke faruwa sun ma zarta batun raye-rayen batsa ko kalamai na rashin tarbiyya, don har ma aibata juna da tayar da husuma a tsakanin qawaye da abokai da ke hulɗa da wannan manhaja ta Tiktok waɗannan matasa suke yi. Don sau da yawa za ka yi ta jin su suna yi wa junansu fallasa da terere a kan wasu ayyukan banza da suke aikatawa a bayan fage, amma da zarar an samu saɓani da juna sai su fito Tiktok suna zage-zage da jifan juna da wasu maganganu waɗanda kowa ya ji ya san lallai tarbiyya ba ta wadaci waɗannan yara ba.

Har zargin aikata fasadi, fasiqanci, luwaɗi da maɗigo za ka ji suna yi wa junansu, babu kunya babu tsoron Allah. Wasu ma idan suna magana sai ka fahimci lallai waɗannan yara ba a cikin hayyacinsu suke ba, ko dai a cikin maye suke ko kuma suna da matsalar ƙwaƙwalwa, saboda tasirin shaye-shaye.

Manhajar Tiktok kamar sauran zaurukan sada zumunta ne da ake da su, inda mutane da dama ke hulɗa da su ta hanyar buɗe shafuka don yaɗa manufofi, kasuwanci, aƙidu, nishaɗi da fitattun abubuwa. A yayin da za ka ga mutane suna buɗe shafuka don samun wata moriya, karatuttukan malamai da wa’azozi, ilimomi na cigaba, waƙoƙi ko finafinai, wasu kuwa suna yi ne don nuna wa duniya kansu da irin fitsarar da suka iya, babu kunya ko tunanin abin nan da suke yi watarana zai dawo ya vata musu suna da mutuncinsu.

Babu ma kamar yara mata da ke da burin watarana za su yi aure ko neman aiki da sauransu. Yaya za su ji idan an binciki rayuwarsu ta soshiyal midiya an ga banzar rayuwar da suke yi? Wacce makarantar ce za ta ba su gurbin karatu? Wanne uban ne zai amince ɗansa ya auri mai irin wannan rayuwa? Yaya za ta kalli mijinta da ’ya’yanta kan irin rayuwar da ta yi a baya?

Dubi dai yadda kafafen watsa labarai suka yi ca kan batun wannan ɗaliba Rahama Sa’idu, da aka sallama daga karatu, duk kuwa da cewa makarantar sun bayyana korarta bashi da alaƙa da harkokinta na Tiktok, amma jama’a sai qara bankaɗo abubuwan da ta yi a baya suke yi, suna daɗa fallasata da aibata salon rayuwar ta na soshiyal midiya.

Wata marubuciya mai sharhi kan harkokin da suka shafi tarbiyya, Sadiya Garba Yakasai ta yi wani tsokaci a shafinta na manhajar fesbuk inda ta ɗora alhakin lalacewar tarbiyya da abin da waɗannan yara ke aikatawa a zaurukan sada zumunta kan iyaye, musamman iyaye mata waɗanda suka fi samun kusanci da yara mata a gida. Ta nemi iyaye mata su daina bari soyayya da rashin son takurawa yara, ya rufe musu ido kan kula da tarbiyyar yaransu, da abubuwan da suke yi na baɗala a cikin daƙunansu suna yaɗawa a duniya.

Marubuciyar ta cigaba da cewa, ‘Wannan yarinya saken da ta samu lallai daga iyayenta ne don ba za su gaza sanin mai take aiwatar wa ba to, ga lokaci ya ƙure har ta shiga duniya. Ta yaya za a ce ta samu miji kamili wanda zai so ya zaɓa wa yaransa irin wannan yarinya (a matsayin uwa) ba don tunanin sa ita ma tarbiyya bata ishe ta ba, mai za ta bawa nasa yaran? Wannan waya da muke amfani da ita wallahi ba ƙaramar illah ta yi mana ba tunda a ciki dai yaran nan suke ta iya shege kala-kala.

Don Allah iyaye mu tashi a tsaye akan yaranmu, wannan abu ne mara daɗi wallahi abin kuma kunya ne a gunmu, don Allah maza ku taimakawa matanku, su bai wa yara tarbiyya ingantacciya. Jan kunne, don Allah in haka ta samu a daina zagin yara da tsine musu. Don Allah mu taru mu ceto yaran mu!’

Lallai akwai buƙatar iyaye, malamai da hukumomi, su tashi tsaye wajen faɗakarwa da jan hankalin matasa kan muhimmancin tsaftace yadda suke harkokin su a soshiyal midiya, a matsayinsu na matasa manyan gobe, waɗanda alhakin shugabanci da tarbiyya zai dawo hannunsu nan gaba. Su kuma ’yammata masu girgiza jiki da karkaɗa ƙirji su tuba su san abin da suke yi, bai dace da tarbiyya ba, kuma babu wata wayewa ta rayuwa da ta amince da haka. Hatta su kansu waɗanda ba Musulmi ba da suke yin irin waɗannan abubuwa na rashin tarbiyya ba suna yi ne don rashin mafaɗi ba ko don tarbiyyar al’adunsu da addininsu ya amince da hakan ba.

Mu dubi yadda su turawan da suka ƙirƙiro da waɗannan manhajojin da mutanen Asiya masu Tiktok ɗin ai ba haka suke yi ba, suna yaɗa abubuwan cigaba ne, da wayewa, da fasahohin da ƙasashensu ke taƙama da su. Irin yadda ’yammatan mu na Arewa, Musulmi, suke nuna kansu a duniya, a zaurukan sada zumunta, bai dace ba gaskiya.

Ba a hana ki shiga soshiyal midiya ba, amma ki yi abin da zai kare mutuncinki, da mutuncin iyayenki, martabar addininki, da makomar rayuwarki ta gaba. Babu yadda za ki samu irin mijin da ki ke so ya aureki a irin wannan rayuwar. Tashen balaga ba hauka ba ne. Da yawanku kun wuce a ce ƙuruciya ce ke ɗibanku ku ke yin abin da ku ke yi. Kuma kun san dai ba a neman mijin aure da haka.

Ku sani, abin da ɗanyen kashi ke jawowa bai wuce ƙuda da yaɗa cuta ba. Shi kuwa ƙuda dama a wajen kwaɗayi yake mutuwa!