An garzaya da shugaban NLC asibiti bayan gana masa baƙar azaba

Daga BASHIR ISAH

An garzaya da shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Comrade Joe Ajaero, zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Owerri sakamakon baƙar azabar da ya sha a hannun ‘yan sanda.

An garzaya da Ajaero asibitin ne alhali idonsa na dama a kumbure suntum.

Shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa a jama’a na NLC, Benson Upah, ya bayyana lamarin da yunƙuri garkuwa wanda ya riƙiɗe ya zama yunƙurin kisa.

A cewar Upah, “An gayyaci Joe Ajaero da misalin ƙarfe 15:30 a asibitin’yan sanda da ke Owerri, daga nan kuma aka ɗauke shi zuwa Babban Asibitin Tarayya a Owerri don yi masa magani, idonsa na dama a kumbure sosai.”

Ya ƙara da cewa, “Ajaero, wanda ya kasa bayani sosai, ya ce jim kaɗan bayan tsare shi da aka yi an gana masa azaba bayan an rufe masa idanu, kana aka ɗauke shi zuwa wani wuri inda aka ci gaba da gana masa azaba.

“Kuɗinsa da wayoyinsu da sauran abubuwan da yake ɗauke da su duk an ƙwace ba tare da an maido masa su ba.”

Tun farko NLC ta yi barazanar shiga yajin aikin gamagari muddin ba a sako mata shugaban nata ba ya zuwa ƙarshen Laraba

Tashar Channels Television ta rawaito cewa an tsare Ajaero ranar Laraba a Owerri, babban birnin Jihar Imo biyo bayan zanga-zangar da ma’aikatan jihar suka gudanar kan danne musu ‘yanci da suka ce gwamnatin jihar ke yi.

MANHAJA ta kalato cewa har sakatariyar NLC a jihar ‘yan sanda ɗauke da manyan makamai suka je suka cafke Ajaero suka tafi da shi wani wurin da ba a san ko ina ne ba.