Rubutuna ya fi mayar da hankali kan illolin bin bokaye da ‘yan tsubbu – Lailat Abdullahi

“Ya kamata manyan marubuta su kama hannun ƙanana, su yi masu jagora”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Zainab Abdullahi Musa mai laqabi da Lailat, matashiyar marubuciya ce daga Jihar Katsina, wacce ta kasance mai himma da kishin rubutun adabin Hausa. Duk da kasancewarta ɗalibar koyon aikin jinya, bai hana ta ware lokaci na musamman don yin rubutun da zai taimaka wajen ilimantar da matasa ƴan’uwanta game zamantakewar rayuwa, da muhimmancin bin iyaye. Kawo yanzu ta rubuta littattafai guda biyar, har yanzu tana cigaba da rubutu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, marubuciyar ta bayyana masa irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta zama marubuciya, da ƙoƙarin da ta yi wajen neman goyon bayan iyayenta don su sa mata albarka a rubuce-rubucen da take yi.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

LAILAT: Sunana Zainab Abdullahi Musa, wacce aka fi sani da Lailat. Kuma ni marubuciyar littattafan Hausa. Sannan yanzu haka ni ɗaliba ce da ke karatun aikin kiwon lafiya a matakin diploma. Sannan har wa yau ina taɓa harkokin kasuwanci na kayan soye-soye, na ƙwalam da maƙulashe.

Menene taƙaitaccen tarihin rayuwarki?

To, kamar dai yadda na faɗa a farko, sunana Zainab, amma jama’a da dama sun fi sanina da Lailat. An haife ni a Jihar Katsina, a ƙaramar Hukumar Katsina. Na yi karatuna na firamare a makarantar Ahmadu Commassie Science Model Primary School da ke nan Katsina. Sannan na tafi qaramar sakandire ta gwamnati da ake kira da Day Sahara. Bayan nan kuma sai na tafi, Babbar Kwalejin ‘Yanmata ta Gwamnati da aka fi sani da l Government Girl’s College Senior, inda na kammala karatuna a matakin sakandire. A halin yanzu kuma ina karatun koyon aikin jinya a Makarantar Koyon Aikin Jinya ta Jihar Katsina. Har wa yau kuma ina cigaba da neman ilimin addini a makarantar mu ta Islamiyya da ake kira da Madarasatut Taɗbiƙus Sunnah Katsina.

Waɗanne abubuwa ne na darasin rayuwa za ki iya cewa sun yi tasiri a rayuwarki, tun lokacin tasowarki?

Lokacin da ina aji ɗaya a ƙaramar sakandire na tava tambayar mahaifina zan je wurin bikin yayar ƙawata, sai ya hana ni zuwa. Ni kuwa bayan fitar shi sai na shirya na yi tafiyata wurin wannan biki, domin na saka a raina ina son zuwa, kuma a lokacin mahaifiyata ba ta nan ballantana ta hana ni. Shi kuwa mahaifina bayan ya fita sai ya kasa natsuwa, ya kuma ji a ransa cewa zan iya fita, kawai sai ya juyo ya dawo gidan domin ya samu tabbaci, cikin rashin sa’a kuwa sai ya tarar na tafi duk da ya hana ni.

Ransa ya vaci sosai, hakan ya sa ya yi tanadin abin duka kafin na dawo. Ni kuwa ban san wainar da ake toyawa ba, sai da na gama hidimata sannan na nufo gidan. Tun da na fahimci mahaifina ya dawo gidan tsoro mai tsanani ya kama ni, sai na fara laɓe lave, da rakuve rakuɓe, duk dai alamun rashin gaskiya sun gama tabbata tare da ni. Ƙanwata ce ta je ta faɗa ma shi na dawo, shi kuwa ya nufe ni da abin duka yana tambayar dalilin da ya sa na fita alhalin kuma sai da ya gargaɗe ni kada na fita, cikin tsoro na dinga yi ma shi magiyar ya yi haƙuri kada ya dake ni ba zan sake ba. Ganin irin tsoratar da na yi ya sa bai yi dukan ba, amma ya tambaye ni idan na sake miye zai mini, ni kuwa saboda tsoron da na ji da kuma yarinta sai nace idan har na sake yin abu alhalin na san ya hana ni to, na yarda ya kashe ni.

A lokacin shi kanshi sai da ya yi dariya, kuma sai nake tunanin wannan ne dalilin da ya sa ya ƙyale ni. Wannan yana daga cikin babban darasin da na riqe ya zauna mini daram a zuciyata, cewa duk abin da zan yi sai na nemi yardar iyayena da amincewarsu. Sai da aka shafe lokaci mai tsawo ina tsoron aikata laifi, domin ina tunanin da na aikata kashe ni ɗin zai yi, kuma har yanzu duk lokacin da na yi laifi ya ɓata masa rai sai ya tuna mini da waccen maganar nayi.

Menene ya fara jan hankalinki ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Tun ina primary school ina haɗa baƙi da ƙyar na fara sha’awar karance karance, lokacin ina karanta irin su ‘Magana Jari Ce’, ‘Ruwan Bagaja’, -Jiki Magayi’ da sauran su. Lokacin da na fara girma sai akalar karatun nawa ya canja zuwa kowanne irin littafi in dai na Hausa ne, kama daga na yaqi, ko na soyayya. Amma duk da haka ina yi ne a ɓoye, don mahaifina ba ya so. Akwai lokacin da za mu tafi wani taron horar da ɗalibai Musulmi a lokacin hutu, wanda aka fi sani da IVC a Jihar Sakkwato, mahaifina ya bani kuɗi masu ɗan yawa don amfanin kaina, ko da wata buƙata za ta taso mini, ni kuwa gabaɗaya sai na sayo sabbin littattafan Hausa da su. Bayan na dawo ne yana buɗe jakata ya ci karo da su, nan take ya ƙone su, shi kenan sai nayi biyu babu. Ina maganar a shekarun baya ke nan, amma yanzu da amincewarsa har na fara rubutun nawa littattafan.

Za ki iya tuna labarin da ki ka fara rubutawa, kuma a kan wanne jigo ki ka yi labarin?

Ƙwarai kuwa zan iya tunawa. Labarin da na fara yi shi ne wanda na sa wa suna ‘Guguwar Fansa’. Kuma jigon labarin shi ne illar rashin yin biyayya ga iyaye, sannan a ciki kuma na saka illolin da ke cikin hassada.

Waye ya fara taimaka miki wajen sanin ƙa’idojin rubutu da yadda ake gina labari?

To, a gaskiya malaman nawa suna da yawa waɗanda suka koyar da ni a wannan fanni, kuma suke cigaba koyar da ni. Don har yanzu ni ɗin ɗaliba ce. Daga cikinsu Malam Abba Abubakar Yakubu, Malam Abdulrahaman Aliyu, Malam Jibrin Adam Jibrin, Malam Yusuf Gumel da sai kuma Aunty Hassana Ɗanlarabawa.

Kawo yanzu kin kai shekara nawa kina rubutu, kuma littattafai nawa ki ka rubuta?

Na fara rubutu a farkon shekarar 2021, don haka yanzu shekaruna biyu kacal da fara rubutu. Zuwa yanzu kuma na rubuta littattafai guda biyar, sai kuma gajerun labarai masu yawa.

Kawo mana sunayen littattafan da ki ka fitar?

‘Guguwar Fansa’, ‘Ramuwar Gayya’, ‘Wani Dare’, ‘Inuwar Sharri’, ‘Wasa da Rayuwa’. Waɗannan su ne littattafan da na rubuta a halin yanzu.

A kan wanne jigo ki ka fi son gina labarinki a kai?


Akasarin littattafaina na fi mayar da hankali ne kan illolin bin bokaye da ‘yan tsubbu. Kuma a wasu littattafan kuma ina nazari kan abubuwan da ke faruwa na yau da kullum a tsakanin jama’ar da nake rayuwar tare da su.

Shin kina yin rubutu don sha’awa ne ko don neman kuɗi?

Gaskiya a halin yanzu dai ina rubutu ne don sha’awa, ba don kuɗi ba. Domin kuwa gabaɗaya waɗannan littattafan nawa da na lissafa guda ɗaya ne kaɗai na tava yi na kuɗi, shi ma sai da wasu daga cikin marubuta ‘yan’uwana suka mini ca, sannan na sa masa farashi.

Ta yaya ki ke sake labarinki, kina buɗe zaure ne a WhatsApp, ko pdf ki ke sayarwa ko kuma a manhaja?

Ina da zauruka a Whatsapp da kuma na ƙawayena marubuta. Duk lokacin da zan fitar da labarina a nan nake yaɗawa, tare da taimakon waɗannan ƙawayen nawa da muke taya juna yaɗa rubuce-rubucen mu.

Su waye manyan ƙawayen da ku ke musanyen shawarwari da zumunci a tsakanin marubuta?

Marubuta da yawa ina yin zumunci, da neman shawara a wajensu, musamman akan abinda ya shafi rubutu. Amma akwai wasu daga cikin su da suka zame mini tamkar ‘yan’uwana na jini, su ne kuwa Shamsiyya Manga, Milhart Yakubu, Queen Nasmah da Meenat ‘Yandoma.

Wanne tsarin kasuwancin littafin ne ya fi kawo miki riba?

Ni kawai a WhatsApp nake tallar littafina, kuma a nan na yi cinikin shi wanda na sanyawa. Kuma Alhmdullahi na samu alheri mai yawa.

Kawo yanzu wanne littafinki ne ya fi samun karɓuwa a wajen masu karatu?

‘Guguwar Fansa’ shi ne littafina na farko, kuma shi ne littafin da ya fi samun karvuwa a wurin mutane, na samu alheri sosai sanadin wannan littafi. Duk da kasancewar littafin na kyauta ne, amma na samu kuɗin da suka ninka waɗanda na samu a lokacin da na yi na kuɗin.

Kina da YouTube Channel ne da ki ke sa littattafanki, ko sayarwa ki ke yi wasu su fitar a nasu channel din?

Ba ni da YouTube Channel, amma akwai wacce ke siyan littafina ta karanta shi a YouTube Channel ɗinta.

Ta yaya ki ke sanin jigon da ya kamata ki yi rubutu a kai?

Duk lokacin da aka bani labarin faruwar wani abu, wanda ya tsaya mini a rai, ko kuma ni da idona na ga faruwar wani abu. Sai kawai na ji ina so na yi rubutu akan abin, daga nan kuma sai na yi fatan saƙon nawa ya isa ga al’umma.

Wanne lokaci ne ki ka fi jin daɗin yin rubutu?

Ina jin daɗin yin rubutu lokacin da ake yin ruwan sama, da kuma lokacin da nake cikin damuwa.

Wanne darasi za ki iya cewa zama da marubuta ya koya miki?

Na koyi iya zama da mutane ko waɗanne iri ne, kuma ko da kuwa wanne irin hali gare su. Bayan haka na koyi abubuwa da yawa waɗanda ba zan iya lissafawa ba. Ina girmama duk wanda nasan ya girme ni, waɗanda kuma muke sa’annin juna muna girmama juna da su, mu yi wasa, mu yi dariya. Don haka ban tava fuskantar wani ƙalubale ko wata matsala da wata marubuciya ba.

Wanne alheri ki ka taɓa samu ta dalilin rubutu da ba za ki manta da shi ba?

Akwai wata baiwar Allah ‘yar Jihar Bauchi lokacin da nake rubuta littafina na farko. Ta kira ni a waya ta faɗa min sunanta da garin da take, ta kuma faɗa mini tana cikin masu karanta wannan littafi nawa. Bayan kwana biyu kuma ta sake kirana ta ce min ta bayar da saƙo a mota a kawo min, bayan saƙon ya zo da na buɗa na tarar da kayan kwalliya masu kyau da tsada. Kamar irin turaruka, mayukan gyaran gashi, har da rubutacciyar wasiqa na ƙaunar da take min da rubutuna. Na yi matuƙar farin ciki da wannan kyauta, sannan kuma na ajiye wannan wasiƙar don tarihi ne na musamman a gare ni, kuma har yanzu muna gaisawa.

Ban da harkar rubutu wanne abin ki ke yi, karatu, ko sana’a?

Duka biyu. Ina yin karatun aikin jinya da wayar da kai kan kiwon lafiya. Sannan kuma ina yin sana’ar kayan soye-soye irin su snacks, wanda ake rabawa a wajen biki, ko suna, ko wani babban taro.

Wanne lokaci ne ki ka fi samun natsuwa da nishaɗi a zuciyarki?

Lokacin da nake cikin iyaye da ‘yan uwana. A kowane dare muna haɗuwa mu yi hira, mu kalli labarai, ko mu saurari labaran manyan tashoshin rediyo irin su BBC Hausa, Rediyo Faransa da su Muryar Amurka. A lokacin da mu kan ci abinci tare da mahaifinmu, mahaifiyarmu da kuma sauran ‘yan’uwana. To, wannan lokaci shi ne ya fi saka ni farinciki fiye da kowanne lokaci.

Wacce ce madubinki a cikin marubuta?

Ina da manyan marubuta biyu da nake ɗauka a matsayin madubina, su ne kuwa Fatima Hussaini El-Ladan, da Hassana Ɗanlarabawa.

Wacce shawara ki ke da ita ga marubuta?

Shawarata ita ce manyan marubuta su kama hannun ƙananan marubuta, su yi mu su jagora, su nuna musu hanyar da suka bi suka yi nasara. Kada hassada da ƙyashi, da tsoron kada tana ƙaramar marubuciya, wata rana za ta iya zama babba, har ta zo ta tarar da mu, ko ma ta wuce mu ya sa mu ƙi taimakon juna. Asalin manyan sun fara ne daga ƙanana, haka su ma watarana ƙananan za su iya zama manya, don duk abinda ka ke so ka zama, ko ka riga da ka zama. Kafin kai wasu ne suka fara zama, amma sai suka taimake ka ba tare da sun maka baƙinciki ba. Mene ne zai sa kai ka yi wa wani na ƙasa da kai baƙinciki. Allah ya ƙara haɗa kan marubuta gabaɗaya.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Da na gaba ake gane zurfin ruwa. Sai kuma, abin rabo ne kuturu ya kama tarwaɗa. Waɗannan karin maganar suna da tasiri a gare ni, domin kuwa akwai tunatarwa da hikima sosai a cikinsu.

Mun gode.

Ni ma na gode.