Macen Arewa ba raguwa ba ce kamar yadda wasu ke faɗa – Ayat Uba Adamu

“Wasu mazan na jiran matansu su samu ne su ba su”

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda aka sani, matan Arewa sun yi fice wurin biyayyar aure, kula da ‘ya’yansu tare da haƙuri da duk matsalolin da za su iya cin karo da su a gidan aure.

Macen Arewa ce za ta miƙe haiƙan ta nemi na kanta, ta yi amfani da abinda ta samu a neman nata, ta girka abinci, ta ciyar da ‘ya’yanta har ma da mijin idan yana tare da su.

Macen Arewa ce za ta ɗora kaso mai yawa na buƙatun gidanta a wuyanta, tsayin lokaci, amma hakan ba zai sa ta tsallake umurnin mijinta ba.

Macen Arewa tsayayyar mace ce da ke neman na kanta koda kuwa ta yi sa’ar samun miji mai kula da ita.

A wannan mako, shafin Gimbiya ya yi wa masu karatunmu babban kamu, kamar yadda muka saba faɗa, shafin Gimbiya ƙofa ce gare ku mata, da za ku iya samun ilimi mai tarin yawa, domin masu azancin magana suna cewa, rayuwar wani makaranta ce ga wani.

Jajirtacciya, mace mai kamar maza da ke layin matan da ke siya wa matan Arewa ƙima a idon duniya, masaniya kan sha’anin kiyon lafiya, kuma shahararriyar ‘yar kasuwa, mai kishin ‘yan’uwanta mata.

A tattaunawar Manhaja da ita, ta yi muhimman batutuwa da suke da tasiri ga duk wata mace da ke buƙatar sanin hanyoyin da za ta iya samun ilimin yadda za ta iya gudanar ko bunƙasa sana’arta.

Masu iya magana dai sun ce, waƙa ga bakin mai ita ta fi daɗi, don haka, Aisha Asas ce tare da Hajiya Ayat Uba Adamu:

MANHAJA: Wacce ce Ayat Uba Adamu?

HAJIYA AYAT: Sunana Ayat Uba Adamu haifaffiyar Jihar Kano. Na yi dukkan karatuna na addini da na boko a Kano. Ina da aure da yara.

Me aka sa gaba?

Kamar yadda aka san kusan ko wacce ‘ya mace wajen fuskantar kula da iyalinta da kuma neman na kai, to ni ma haka ne, sai ma ƙari ta fannin yadda za a kawo wa mata ɗauki cikin sana’o’in su, domin dogoro da kai.

Kafin mu tsunduma tattaunawar tamu, za mu so ki fara da mana bayanin matsayin sana’a ga macen Arewa.

Macen Arewa ai ba raguwa ba ce kamar yadda wasu suke faɗa, domin tun asali ita macen Arewa an gina ta wasu abubuwa ne na tarbiyya dan haka ake ganin kamar ba su san nema.

a lokacin baya, iyayenmu maza suna ƙoƙari sosai wajen katange mu daga ganin babu, domin duk abinda ‘ya mace ke buƙata zasu nemo su bata, idan ta je gidan aure ma haka ne, sanan su iyayenmu mata a zaman su, kusan duk gidan da ki ka shiga akwai lambu a ciki ko a bayan gidan, kuma ba wai iya ƙauye ba, har birni. Kinga ni a Lamiɗo creasent aka haife ni, nan ne gidan ubana, amma na tashi na ga lambu, akwai alayahu, shuwaka, da sauran su.

Da an tashi ne kawai zagawa za a yi a ciro, haka ma na tashi a gidan ana kiwon kaji , ana saida lemon kwalba wanda ma daga kampani mota ke zuwa ta ajiye lemon. Kuma duk wanan abin fa da iyayen nawa mata suke, suna da ilmin boko. domin mahaifiyata ma’akaciyar asibiti ce, abokiyar zamanta kuma malamar makaranta ce, don haka gaskiya tun zamanin baya macen Arewa ba raguwa ba ce tasan neman na kai.

Abinda ya jawo yanzu aka fi ganin neman shi ne, kamar yadda na faɗa a baya, iyayenmu maza sun katange mu daga babu haka mazaje a waccan lokacin, yanzu kuma da yawa wasu iyayen suna jiran ma yaran su ba su ne, haka wasu mazajen ma suna jiran matayen su ba su, ko kuma ba su sauke nauyin da Allah ya ɗora musu ba.

Don haka sana’a a wannan lokacin sai ta zama kamar sinadarin karin ingancin zaman aure, domin idan macen na sana’a, zata taimaka wa mijin ta hanyar kula da yaranta, ba kamar a wanan yanayin da muka tsinci kanmu na tsadar rayuwa, wanda mazan ma da suke ƙoƙarin kula da iyalinsu su ma a wannan lokacin suna buƙatar tallafi daga matayensu, ta hanyar tausasa harshe, da kuma hanyar tallafi a kula da gidan, wanda idan mace ba ta da sana’a duk wannan abin bazai samu ba.

Kenan matan da ke zaman kashe wando ba su samo wannan tarbiyyar daga tushe ba?

Gaskiya kai tsaye ba za a iya cewa, eh ko a’a ba, domin ko a yaran da aka haifa wani yana da sha’awar kasuwanci wani kuma karatu ko aikin gwamnati. Kinga idan daga irin wannan ra’ayin ba yadda zakai da yaro, amma abinda ya kamata shi ne, a wannan rayuwa komai yaronka zai karanta ya kasance ka koya masa wani ‘skill’ da zai taimake shi, kamar ni a gida ina da yarinya ‘yar shekaru sha huɗu, kuma ajinta huɗu a sakandare, amma na kai ta koyon ɗinki, tun lokacin Korona. Kinga a lokacin ma bata kai wannan shekarun ba, kuma yanzu haka tana yi, kuma tana saida su gullisuwa, da aya, duk don ka sawa yaro sha’awar abin kuma ka saita shi.

Kin ɗauko zancen kula da iyali. A wata tattaunawa da muka taɓa yi da wata, ta ce, kaso mafi rinjaye na matan Arewa na yin kaso mai tsoka na daga buƙatun gida, baya ga bauta da suke yi da jikinsu. A taki mahangar me za ki iya cewa a wannan ƙiyasi na ‘yar’uwa?

A tawa fahimtar indai akwai zama na amana da fahimta ai ba komai ba ne don mace ta yi wannan, ai kyautatawa ce, kuma amfanin neman kenan, domin tallafa wa juna, a gudu tare a tsira tare, ‘more especially’ yanzu da rayuwar ta zama sai addu’a, idan ki ka cire maigida wanda shi ne dama ke nemowa, to idan ba shi da shi ba fa mai taimaka wa wannan iyalin, don haka kinga don mace ta hidimtawa iyalinta ai abin alfahari ne ma. Babban abinda ake so dama ya kasance a zaman aure akwai fahimtar juna, da tausayawa. Idan akwai wannan mace ko duniya ta mallaka za ta iya ba wa iyalinta, kuma wannan fahimtar juna ita zata samar da farin ciki ga iyalin wanda hakan zai samar da kyakkyawar al’umma.

Ko za ki sanar da masu karatunmu irin sana’a ko sana’oin da ki ke yi?

Da farko na fara da kawo takalman yara daga Chana, daga baya kuma na koma dukkan nauin kayan yara ba iya takalma ba, wanda ita wannan sana’ar nai mata register ta CAC da TIN da ‘Ayatullah collections’ wanda cikin ikon Allah ana tafiya Allah ya qara ba ni dama na fara samar da tumatir wato ‘tomatoes paste’, amma a kwalba nake sakawa. A haka dai ana yi ana siya har aka zo kan sarrafa hatsin tamba wanda yanzu Allah ya sa mun samar da ɓangaren kayan gonar da muke sarrafawa, shi ma dai kamar wancan an masa register tasa daban mai suna ‘Farm Produce & Veggies Limited. Shi wannan ɓangaren kayan gona kawai zai dinga sarrafawa, wanda muke fatan al’ummarmu za su amfana da shi da yardar Allah.

Bayan wannan kuma ni ma’aikaciyar asibiti ce a jiharmu ta Kano mai albarka, yanzu haka ni ce secretary ta haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa reshen jihar Kano, wato ‘Medical and health workers union of Nigeria’ ( MHWUN), kuma ‘Founder’ ta ‘women online vendors association’ WOVA.

Ma sha Allah. Wato dai sana’a goma, masu iya magana suka ce maganin mai gasa. Bari mu fara da ɓangaren da ba kasafai ake samun ‘yan Arewa a fagen ba, wato sarrafa wasu daga cikin ababen da aka albarkace mu da su, tare da zamanantar da su, ta yadda za su iya shiga ko’ina. Ba mu labarin yadda ki ka yi sha’awar fara wannan sana’a.

A’a ana samun mata masu sarrafa kayan gona tunda ga ƙungiyar wofan ma, kuma a ɗaiɗaiku ma akwai irin su Maryam Gatawa wacce wani abin ma a shafin ta na yanar gizo da nake bi nake gani nake ƙara ilmin abin, don haka suna da yawa gaskiya da na sani masu sarrafa abubuwan gona a maida su na zamani.

Ta yadda na fara shi ne, maigidana ma’aikacin gwamnati ne, kuma yana tava noma, don haka bayan ya bar aiki ya yi ritaya, sai ya koma ya fuskanci noman, don haka nakan bi shi gonar a haka na fara sha’awar abin, sai kuma wata shekara ya yi tomatir aka samu annoban wani ciwo na tomatir Ebola , duk tumatir ɗin ya lalace, aka yi gagarumar asara, sai na ce, a kwaso min ragowar a kawo min gida, haka kuma aka yi da yake na saba idan anyi noman na kwashi tumatir ɗin na sarrafa iya namu na amfanin gida, na ajiye sai ya shekara bai komai ba. Don haka na ce, a kawo.

Haka kuwa aka yi, aka kawo na tara mata suka taya ni gyaran sa tas na sarrafa na ɗura abina a kwalba. Wata shekara kwatsam sai ga ciwon Korona yazo, sai ‘lock down’. To da wannan damar nai amfani tunda ni Ina fita aiki, na fara tallata tomatir ɗin har aka fara siya, kuma har Allah ya kawo yanzu ake ɗan taɓa sana’ar.

A matsayinki ta mace ko kin fuskanci wasu ƙalubale yayin da ki ka yi yunƙurin fara wannan sana’a?

Babban ƙalubale shi ne rashin kuɗi, (dariya) amma bayan wannan ba wani ƙalubale, tunda akwai mataimaka, kuma ciki har da maigidan. Kinga komai zai zo da sauƙi ta wannan fannin.

Zuwa yanzu za a iya cewa kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu dangane da kamfanin naki?

Anan za mu dasa aya a wannan tattaunawa da muke yi da Hajiya Ayat Uba Adamu, wanda da yardar mai dukka, a sati na gaba, za mu soma da kawo maku amsar wannan tambayar, kafin wasu tambayoyin su biyo baya.