Rusau: Kotu ta umarci Gwamnatin Kano ta biya N30b a cikin mako guda

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta biya Naira biliyan 30 cikin mako guda.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Samuel Amobeda, ta umarci Gwamnatin Kano da ta biya wannan kuɗi ne sabili da ƙarar da aka shigar a kanta na rushe gine-gine ba bisa ƙa’ida ba.

Masu shaguna a Masallacin Idi da sauran ‘yan kasuwa da rusau ɗin ya shafa ne suka shigar da ƙarar.

Idan za a iya tunawa, a baya Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Isah Haruna Dederi, ya faɗa cewa shari’ar ta ta’allaƙa ne kan batun mallakar kadarorin, sannan dukkanin filayen mallakin Gwamnatin Jihar ne.

Alƙalin kotun, Samuel Amobeda, ya umarci Gwamnatin Jihar a kan ta biya Naira biliyan 30 a cikin asusun kotun a tsakanin kwana bakwai kafin a ga yadda sakamakon ɗaukaka ƙara zai kasance.

Kotun ta ce biyan kuɗin sharaɗi ne da ta gindaya kafin amincewa da wani ƙudiri da masu shigar da ƙara ko waɗanda ake bi bashi suka shigar.

A cewar kotun ƙudirin kuwa shi na neman kotun ta tabbata a kan hukuncin baya da ta yanke a ranar 29 ga Satumban 2023.