Lionel Messi ya lashe kyutar gwarzon ɗan kwallon ƙafa na duniya na 2023, Ballon d’Or.
Wannan shi ne karo na takwas da Messi ke lashe wannan kyauta ta bajinta a duniyar wasan tamaula.
Messi tsohon ɗan wasan Barcelona da Paris St Germain mai taka leda a Inter Miami a Amurka ya ɗauki kofin duniya a Qatar a 2022.
Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe babban kofin duniya na farko a wajensa, sannan na uku a kasar jimilla.
