Na fi gane na buga littafi maimakon na saka a onlayin – R.A. Adam

“Masu hali ba sa ƙarfafa gwiwar marubuta”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Rufa’i Abubakar Adam, wanda aka fi sani da R.A. Adamu, wani matashin marubuci ne da ya taso cikin sha’awar karance-karance da rubuce-rubuce har kafin Allah ya sa ya zama mai aikin ɗab’i da zane-zane a na’urar kwamfuta. Yana daga cikin matasan marubutan da suka kafa ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Gombe (GAMJIG), domin haɗa kan marubutan Gombe da samar da wasu hanyoyi na bunƙasa cigaban adabi da harshen Hausa. Gwagwarmayar da ya sha a baya a yayin ƙoƙarinsa na ganin ya zama marubuci ya silar kawo sauyi a Jihar Gombe, ita ce ta sa ya zama tauraro a tsakanin marubutan Jihar Gombe. A tattaunawarsa da wakilin jaridar Manhaja Blueprint Rufa’i ya bayyana burinsa na ganin ya kafa wata cibiyar nazarin al’adun Hausawa da tarihi, wanda duniya za ta yi alfahari da shi. 

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka?

ADAMU: Sunana Rufa’i Abubakar Adam. Ni marubuci ne ɗan asalin Jihar Gombe. Sannan ni malamin makaranta ne, kuma ina aikin zane-zane da kuma sarrafa na’urar kwamfiyuta. Ni magidanci ne, ina da mata da ‘ya ɗaya. 

Ka ba mu tarihin rayuwarka a taƙaice.

Kamar yadda na faɗa a baya, sunana Rufa’i Abubakar Adam, amma a jikin bangon littatafaina nakan saka R.A Adam don taƙaitawa. Ni ɗan Jihar Gombe ne, kuma an haife ni ne a garin Gombe a Unguwar Bolari. Na halarci makarantar firamare da kuma sakandire duk a cikin garin Gombe. A matakin karatu na gaba da sakandire kuwa ina da digirin farko a fannin Koyar da Fasahar Gine-gine wato (Building Technology Education). Sannan ina ayyukan kasuwanci, ina buga littattafai da sarrafa na’urar kwamfiyuta. 

Tun yaushe ka fara sha’awar fara rubuce-rubucen Hausa?

Na tsinci kaina a duniyar rubutu ne tun ina makarantar firamare wajejen 1997 ke nan. Tun tasowata na taso da ɗabi’ar karance-karance, a lokacin duk kuɗin da nake ɗan samu a sayen littattafai suke ƙarewa, na tara littattafai masu yawan gaske, har ta kai ga ina bayar da hayar su, a lokacin ne na fara rubuta labarina na farko mai suna Nafsuzzakiyya.

Wane ne ya fara ɗora ka a hanyar zama marubuci? Kuma da wanne labarin ka fara?

Gaskiya ba wanda ya dora ni a layin rubutu kawai dai yawan karance-karance ne ya jawo na ga ni ma ya kamata na yi rubutu. A lokacin nakan karanta littattafan marubuta irinsu Nazir Adam Salih, domin shi ne gwanina har gobe, da marubuta irin su marigayi Abubakar Imam, Ado Ahmad Gidan Dabino, Bala Anas Babinlata, da Aliyu Abubakar Sharfadi, daga baya-baya kuma akwai marubuta irin su marigayi Abdullahi Mukhtar (Yaron Malam), Shehu Usman Muhammad, Shafi’u Dauda Giwa da su Abdul’aziz Sani Madakin Gini, kafin na koma karanta na turawa musamman James Hadley Chase. Don haka yawan karance-karance ne ya sa na fara rubutu, musamman idan na ga akwai wata matsalar da ya kamata a ce an yi rubutu a kai, amma ba a yi ba sai kawai na ɗauki alƙalami na yi rubutu a kai.

Wacce matsala ka fara fuskanta a farkon fara rubutunka?

Matsalar da na fuskanta a farkon fara rubutuna bai wuce matsalar kuɗi ba, domin ba na mantawa tun a 2002 na so na buga littafina da na rubuta mai suna Wasa Kwakwalwa amma saboda rashin kuɗi ya sa ban kai ga ci ba. A haka har littafin ya ɓata a hannun wani mai buga littattafai da ke unguwarmu. Rashin kuɗi dai ita ce babbar matsalata ta farko da na fuskanta.

Kawo yanzu littattafai nawa ka rubuta?

Aƙalla zuwa yanzu na rubuta littattafai guda goma da waɗanda na buga da waɗanda ban buga ba. Sun haɗa da ‘Nafsuzzakiyya’, ‘Wasa Ƙwaƙwalwa’, ‘Arnan Daji’, ‘Bahaguwar Fahimta’, Mathematics, ‘Ina Son Ki’, ‘Lu’ulu’u A Cikin Juji’, ‘Duniyar Audu’, da kuma ‘Zakara Mai Neman Suna’. Sannan akwai na haɗaka kamar guda uku, ‘Dambarwar Siyasa’, da ‘Siyasa Ba Da Gaba Ba’, sai wanda muke ƙoƙarin bugawa cikin wannan wata da muke ciki ‘Mece Ce Sila?’
Shi littafina na ‘Bahaguwar Fahimta’ na ɗauki aqalla shekara takwas ina rubuta shi, domin na fara rubuta shi tun a 2017 ne, labari ne a kan binciken kisar da aka ɗaurawa wani bawan Allah da bai ji ba bai gani ba, duk don a sace wata muhimmiyar na’ura da ya ƙirƙiro.
Idan ka ɗauki littafina mai suna Lu’ulu’u A Cikin Juji, ƙirƙirarrun gajerun labarai ne guda shida na wasu shaharrarun mutane a ƙasar nan da aka gaza gane cewa suna da wata baiwa. Hakan ya sa aka yi watsi da su, amma daga baya suka zama abin kwatance a duniya. 
Sai kuma Duniyar Audu, shi kuma haɗakar gajerun labarai ne na nishaɗi kamar dai littafin Hikayoyin Shaihu Jaha ne. Sai kuma littafin, ‘Ina Son Ki’, shi ma littafi ne na rikici da yake ƙunshe da soyayya.

Ka na buga littattafanka ne ko kai ma a onlayin ka ke fitarwa?

Gaskiya ni ina buga littattafaina ne, domin kamar yadda na faɗa a baya yanzu haka ina sana’ar buga littattafai ne, don haka yana zuwa min da sauƙi wajen bugawa. Kodayake ina sayen kayan aikina ne ina bugawa a hankali idan na samu kuɗi. Waɗanda ma ban buga ba ina da burin buga su nan gaba, in sha Allahu. Domin kamar yadda na fi jin daɗin karanta bugaggen littafi a zahirance, haka ni ma na fi gamsuwa da na ga na rubuta littafi sannan na buga shi, duk da cewa a yanzu soshiyal midiya ta dakushe kasuwar littafi.

Yaya kasuwar littattafai take a nan Gombe, kuma wanne ƙalubale marubuta a Gombe ke fuskanta wajen fitar da littattafansu?

Kasuwar littattafai a Gombe kam za a iya cewa ta mutu, domin shago ɗaya ne tal ya rage wanda har yanzu in ka je za ka iya samun burbuɗin littattafan Hausa a garin Gombe, wato shagon Malam Sulaiman Mailittafi da ke tsohuwar kasuwa, duk sauran sun watsar da sana’ar sun koma wata sana’ar daban. Nakan ji takaici matuqa idan ina neman littafi na rasa, wanda wani lokacin sai na tura har Kano, Kanon ma ba kowanne littafi ake samu ba, kasancewar kasuwar littafin ba a iya Gombe kaɗai ne ta mutu ba. 

Yaya alaƙarka take da sauran marubutan Jihar Gombe?

Ina da alaƙa mai kyau da sauran marubuta na nan Gombe. Saboda kyakkyawar alaƙar ne ma ta sa har muka yi haɗaka muka samar da littattafai na haɗakar gajerun labarai har sau biyu; Siyasa Ba Da Baba Ba, da kuma Mece ce Sila? (Gajerun Labarai Kan Mace-macen Aure a ƙasar Hausa).

Mene ne ya zaburar da ku ku ka ga ya dace ku kafa zauren Gamayyar Marubutan Jihar Gombe?

Babban dalilin da ya zaburar da mu har muka kafa Gamayyar Marubutan Jihar Gombe shi ne son mu haɗa kan marubuta a waje ɗaya domin sada zumunta, ƙarfafa wa juna gwiwa da kuma tattaunawa a kan duk wani abu da ya shafi rubutu da raya adabin Hausa.

Ku na da ƙungiyoyin marubuta a Gombe kamar nawa?

E, muna da su, duk ba su da yawa, akwai ƙungiyar Hausa ta Jihar Gombe wanda ta ƙunshi ba iya marubuta kaɗai ba, har da manazarta, mawaƙa, malamai, da duk wani mai sha’awar harkokin adabi, ƙungiyar da Dokta Ibrahim Lamiɗo shugaban Sashin Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar Tarayya da ke Kashere, yake jagoranta. Sannan a da dai na san akwai ƙungiyar GOSWA ta marubuta, sai kuma daga baya-bayan nan akwai Dot & Pen Gombe Writers Association, sai kuma zauren ƙasar Hausa Writers, sai yanzu kuma da aka samar da wannan Gamayyar Marubutan Jihar Gombe. Akwai kuma ƙungiyoyin marubuta masu amfani da harshen turanci kamar su Jewel Writers da sauran su.

Waɗanne ayyuka ku ka yi a baya da ya fitar da sunan marubutan Gombe a idon duniya?

Ayyukan da muka yi a baya sun hada da samar da littafin haɗaka da muka sanyawa suna Siyasa Ba Da Gaba Ba, wanda muka buga a bara lokacin da ake ta gwagwarmayar yaqin neman zaɓe na 2023. Mun samar da littafin ne domin wayar da kan matasanmu a kan illar bangar siyasa da faɗace-faɗace, sai kuma wasu littattafai guda biyu da za mu ƙaddamar cikin karshen shekarar nan Matasa Mu Farka wanda shi ma littafin haɗaka ne da Kungiyar Hausa ta shirya, kuma za a ƙaddamar da shi a ƙarshen shekara a bikin ƙaddamar da kungiyar. Sannan sai littafin Mece Ce Sila? Wanda shi ma mun kusa kammala aikinsa, wanda shi ma littafi ne na gamayyar marubuta shida, da muka samar domin bayyana dalilan yawaitar mace-macen aure a ƙasar Hausa.

Ba mu bayanin zaurenka na yanar gizo mai suna TASKAR ƘASAR HAUSA, mene ne dalilin kafuwarsa da gudunmawar da yake bayarwa?

Zaure ne da na buɗe don tattara tarihin ƙasar Hausa ta hanyar adana littattafansu da kuma cigaba da raya duk wani abu da ya shafi Adabi. Aƙalla a kowanne wata nakan samu maziyarta shafin mutum dubu da ɗari biyar, manazarta da ɗalibai sun sha su kira ni a kan binciken da suke yi, ko kuma a kan wani aikin makaranta da aka ba su a makaranta game da shafin.

Wanne buri ka ke da shi nan gaba a harkar rubuce-rubuce?

Babban burina bai wuce na yi rubutun da ko da bayan raina ne za a tuna ni da shi, ana yi mini addu’a kamar dai yadda ake wa su marigayi Abubakar Imam da su Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Ka taɓa shiga wata babbar gasar marubuta? Wacce nasara ka samu?

E, na taɓa shiga gasar da jaridar Aminiya ta shirya a shekarar 2020, a inda na zama ɗaya daga cikin zakaru 15 cikin marubuta 258, wanda har aka buga labaransu cikin littafin da suka yi wa take da Dambarwar Siyasa.

Ta yaya ka ke gani marubuta za su zamanantar da harkar rubutun adabi kamar sauran takwarorinsu na kudu?

Marubuta dai suna ƙoƙarinsu wajen dacewa da zamani, tun da a yanzu da muka ga kasuwar littafi ta mutu wasu daga cikinmu sun koma sayarwa a onlayin, kawai dai gwamnati da manyan mutane da attajirai ne ba su ɗauki rubutu da muhimmanci ba, da zarar ka haɗu da wani babba a matsayinka na matashi nasihar da zai yi ma ka shi ne ka yi karatu to, amma idan da za ka rubuta littafi wanda hanya ce ta yaɗa ilimi da sawa mutane ɗabi’ar karatun, sai ka nemi wannan attajirin ko babban mutumin ko gwamnati ka rasa. Babu wani taimako da za su iya yi maka. A nan ne za ka gane abubuwan da suke fada duk yawanci a baki ne kawai.

Ka na ganin akwai buqatar marubuta su riƙa mayar da hankali ga rubutun littattafan ilimi a maimakon na nishaɗi?

Ai a ganina ai duk wani littafin ilimi akwai burbuɗin nishaɗi a cikinsa, shi kansa ilimi idan ana son isar da shi yadda ya dace to, ya kamata a saka nishaɗi a ciki. Domin ko malaman addini idan suma son isar da wani saƙo za ka ga suna buga misalai da labaru na hikaya waɗanda suka faru da ma ƙirƙirarru don masu saurara su fahimta cikin sauƙi. A ganina a cigaba da rubutu a dukkan ɓangarorin, amma cikin tsari mai kyau yadda al’umma za su amfana ba su cutu ba ta hanyar koya musu munanan ɗabi’u ko sauya musu tunani ba.

Mene ne shawararka ga marubutan adabi a Jihar Gombe?

Shawarata ba ta wuce idan mutum zai yi rubutu ya rubuta abin da ya san zai amfani al’umma duniya da lahira ba, domin ka sani akwai ranar da za a tsayar da kai a tambaye ka duk abin da ka rubuta walau mai kyau ko akasinsa.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.

Na gode.

Ni ma na gode.