Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI
Tun bayan da aka ba wa Nijeria ‘yancin kai na shekaru 63, har yanzu Nijeriya ba ta samu wata guda ba cir ba tare da an ɗauke wutar Lantarki ba a duk sassan faɗin ƙasar. Wannan shi ne ‘yancin kai?! Na tava hira da wani matashi a ƙasar waje zai kai shekaru 25 a wancan Lokacin. Ya ce, ya ɗauka wutar lantarki halitta ce kamar rana da wata da taurari. Har sai da ya ƙara wayo sannan ya gane cewa fasaha ce. A Nijeriya yaro ɗan shekara biyu ya san Idan aka ce NEPA! Ana nufin an kawo wuta kenan. A mulkin tsofaffin azzaluman shugabannin Nijeria har manyan birane suna fama da matsalar wutar lantarki.
Idan muka koma fagen ilmi, kafin a ba wa Nijeria ‘yanci, ilimi kyauta ne. Har da alawus. Yanzu mun yarda an yi yawa, amma me ya sa ba za a sauƙaƙa ilmin ba ta yadda kowa zai samu damar yi cikin sauƙi ba? In ya so sai ya zama doka kamar ƙasashen da suka cigaba. Idan ka gama karatun, za ka yi wa gwamnati aiki na shekaru kaza kyauta, banda Nijeriya. Mu azzaluman shugabanninmu ma so suke su haramta wa talaka yin ilmin ma gabaɗaya.
Batun kiwon lafiya, har yanzu muna fama da matsalolin rashin kayan aiki ko ƙwarewar aiki a asibitocin gwamnati. Wanda a shekaru 63 da ba wa Nijeriya ‘yancin kai in dai ba zaluncin shugabanni ba ya kamata a ce asibitocinmu sun haura yadda suke a yanzu. Ya kamata a ce daga sauran ƙasashen Afirka ana shigowa Nijeriya neman magani ba wai mu daga Nijeriya mu fita waje neman magani ba.
Batun noma, talaka da gwamnati da masu hannu da shuni da yan siyasa mun yi barci gabaɗaya, saboda rashin sanin muhimmancin wannan ɓangaren na noma. Amma da idonmu biyu ba mu yi barci ba, da tuni noman Damina da na rani da kiwo ya yi nisa a Nijeriya, ta yadda sauran ƙasashen Afirka da Turai ma za su dogara da Nijeria wajen samar da abinci da sauran kayan masarufi, saboda albarkar da Allah ya yi wa ƙasar mu ta noma da kiwo. Amma sai duk gabaɗaya mu mu ka yi barci.
Batun samar da hanyoyin sufuri na ƙasa tun bayan ba wa Nijeriya ‘yancin kai, yau shekaru 63. ya kamata a ce birni da ƙauye ko’ina an samar da tituna da za a iya amfani da su wajen gudanar da rayuwar harkokin sufuri. Amma abin haushi a cikin birni ba a ƙauye ba in ka ga Wani titin sai ka ɗauka ma gwamnati ba ta san akwai wajen yana ba.
Batun samar da hanyoyin sufuri na sama. wannan ma gwamnati ta yi barci ko na ce ta yi sakaci, lokacin da aka ba wa Nijeriya ‘yancin kai indai har gwamnatin Nijeriya da gaske take da tuni Nijeriya ta zama sansanin tashin jiragen sama a duk faɗin Afirka. Domin daga shekaru 63 zuwa yau, ba na jin Saudiyya da Habasha da da gaske Nijeriya take za su fi ta yawan hada-hadar samar da sufurin jirage.
Mu koma ɓangaren tsaro. Wanda shi a baya-bayan nan muka fara fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, abinda har yanzu bai haura shekaru 20 ba. In har Da gaske gwamnati take na samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tabbas da yanzu rashin tsaro ya zama tarihi a Nijeriya. Domin ire-irenmu da muka haura shekaru 40, mun taso cikin tsaro a ƙasarmu Nijeria, ta yadda za ka yi tafiya zuwa wani baƙon waje ba ka san kowa ba, a sauke ka, a ba ka makwanci. A ba ka ci da sha. In za ka tafi, a yi maka sha tara ta arziki. Mun taso cikin tsaron da za ka iya tafiya cikin dare ba tare da fargabar komai ba, sai dai ta kare ko maciji, ko wata dabbar. Amma ba tsoron sharrin mutum ba.
Iyakar waɗannan abubuwan da na lissafa kaɗai ya ishi mai hankali yi wa Nijeria jajen ba ta ‘yancin kai da aka yi lokacin ba ta isa yaye ba! Gaskiya Turawan Ingila da su sardauna sun yi garaje wajen ba wa Nijeriya ‘yancin kai lokacinta bai isa ba.
Ko a fannin siyasa ya kamata a ce cigaba mu ya wuce inda muke a Yanzu na murde zaɓe a bawa Wanda al’umma basa so ya mulke su ko a ba wa wanda ya tabbatar bai ci zaɓe a rumfunan zaɓe ba, a ƙwata ta ƙarfin tsiya a kotu a ba shi ko ta hanyar maguɗi.
Abinda zance game da ranar Lahadi, 1 ga Oktoba, ni Abdullahi Jibril Larabi (Uncle Larabi) Ina taya ‘yan uwana ‘yan Nijeriya baƙin cikin yaye ƙasarmu Nijeriya a lokacin yayenta bai yi ba. tare da miƙa ƙasar a hannun waɗanda bai kamata a ce su ne shugabannin da suke jagorantar talakawan ƙasar ba. Don sam talaka ba ya cikin tsarinsu.
A ƙarshe, Ina yi wa ƙasarmu Fatan zaman lafiya da tsaro da kuma fatan samun shugabanni nagari masu adalci da tausayin al’ummarsu.
Abdullahi Jibril Larabi (Ankul Larabi) Mai sharhi ne a kan al’amurran yau da kullum musamman na siyasa. Ya rubuto daga jihar Kano. Lambar waya: 08065418892.
