Yakamata iyaye da sarakuna ku daina kashe kes na cin zarafi a tsakaninku – Rabi Salisu

“Za mu tabbatar da ƙwatar wa marasa ƙarfi ’yancinsu”

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al’umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al’umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda kuma a dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a matsayin kwamishinar jinƙai ta jihar. Wakilin Blueprint Manhaja, Mahdi M. Muhammad ya zanta da wannan baiwar Allah wacce ta kasance mai hidima kan harkokin jinƙai, kuma jajirtacciya a fannin kwatar wa masu ƙaramin ƙarfi ’yanci.
Ga yadda tattaunawar ta kasance;

MANHAJA: Za mu iya cewa yanzu kina wata na biyu a kujerar kwamishina ta harkokin jinƙai, za mu so ki yi mana bayanin ina aka dosa a wannan tafiyar?

RABI: A gaskiya, irin wannan tambaya tana buƙatar nazari sosai ganin cewa wannan ma’aikata ta harkokin jinƙai da kuma walwalar al’umma ta tara fannoni da dama, abubuwan da mu ka saka wa gaba su na da yawa, kamar haka; ɓangaren da ya shafi matasa, ɓangaren da ya shafi mata, sannan muna da ɓangaren da ya shafi walwalar yara da mutane masu nakasa da kuma dai sauran ɓangarori da dama. Don haka ma’aikatar tana da girma sosai ganin yadda ta ƙunshi waɗannan vangarori, wanda hakan ya sa idan za mu aiwatar da wani abu, sai mun duba dukka ɓangarorin. Mu na da kuma vangaren da ya shafi karkara da birane. Akwai abubuwan da mu ke kallo da dama, irin su; yaƙi da cin zarafin ƙananan yara, mata har da maza ma, wanda mu ke ɗaukar mataki idan aka ci zarafin su ta ɓangaren wuraren aiki, auratayya, ko kuwa yara ƙanana ne da ake yi wa fyaɗe, ko kuwa abin da ya shafi yaran da su ke samun matsaloli, har abin da ya shafi makarantun tsangaya, da almajirai da mutane masu fama da nakasa. Irin waɗannan abubuwan duk wanda aka ɗauko mu na da tsarin sa, duk da cewa gwamnati ɗaya bayan ɗaya ne, amma duk tsarin iri ɗaya ne, cigaba kawai ake samu, sai dai ɗan ƙarin da ake yi na wasu abubuwa. Abubuwan da mu ka zo muka taras, mun ci gaba da yi ne sai dai mu ke ƙara faɗaɗa su domin al’umma su amfana.

To, Hajiya waɗanne hanyoyi ne yanzu ku ka ƙara don ganin cewa wannan tsari na ku ya cimma mabuƙata, ba wasu daban ba?

Kamar maganar da Mai Girma Gwamna Jihar Kaduna, Uba Sani yi yi a kan batun rabon kayan tallafi don rage wa al’umma raɗaɗin cire tallafin man fetur, to kafin Gwamnatin Tarayya ta ayyana bayar da wani kaso ga al’umma na tallafi, akwai tsare-tsaren da Gwamnati Jihar Kaduna ta yi nisa akai na fara tanadar abinci daga rumbumta don bai wa jama’a, sai kuma Gwamnatin Tarayya ta ayyana za ta bai wa kowacce jiha Naira biliyan biyar, wanda Alhamdulillah Jihar Kaduna tana cikin jihar da ta samu wannan kuɗi, duk da kaso arba’in da uku na kuɗin za a mayar, sauran bashi ne ga jihohi, sauran kaso hamsin da bakwai gudunmawa ne ga al’ummar waɗanan jihohin. Mu jihar Kaduna abin da mu ka samu shi ne Naira biliyan biyu cikin wannan biliyan biyar da aka yi alƙawari, amma muna sa rai Gwamnan Tarayya za ta cika alƙawarinta na ba da sauran kuɗaɗen don bai wa ’yan ƙasa. To, wannna kuɗi an yi amfani da shi ne wajen sayen kayan abinci, wanda Mai Girma Gwamna ya faɗi hasafin kayan abinci da za a saya na Naira biliyan ɗaya da Naira miliyan ɗari tara da arba’in da wani abu, miliyan sittin da ’yan kai ne zai rago na bayar da tallafin tsabar kuxii ga gidajen marayu ko mutane masu nakasa, tsofaffi da matan da mazajen su suka rasu. Amma a rabo na biyu, ana sa ran za a bai wa manoma taki, za a tada zirgin ƙasa mai zirga-zirga a cikin jihar, da kuma shiga mota kyauta da abubuwa da dama. Amma a wannan karo na farko, abinci ake da buƙata wanda mutane za su amfana. Sannan Alhamdulillah, wannan ma’aikata mu na da ruwa da tsaki a harkar rabo duk da cewa ita Mai Girma Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe Sabuwa, ita ce shugabar wannan kwamitin da gwamna ya naɗa, ta ke jagorantar mu tare da ’yan ƙungiyar ƙwadago, ƙungiyar ‘yan kasuwa, ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin masu nakasa da dai sauran ƙungiyoyi duk an gayyace su don su faɗi yadda za a raba wa al’umma wannan tallafi. An tsara rabon wannan tallafi ne a ƙananan hukumomi 23 da Jihar Kaduna ta ke da su, wanda za a kai wa waɗannan ƙananan hukumomi waɗannan kaya don rabo, wanda ake sa ran mutum miliyan ɗaya da ɗari da hamsin ne za su amfani da wannan kaya. Kuma ba a tava rabon kaya masu yawa irin wannan ba, duk rabob da yi a baya. A yadda aka tsara ma, mutum zai iya ci na kwana goma ko mako ɗaya a gidansa. Idan ka kai su ƙananan hukumomi, sai an kira liman, fasto, mai unguwa, masu ruwa da tsaki, masu nakasa da matasa, duk a gaban su za a raba na gundumomi. Don haka ba a yarda ƙaramar hukuma ta tara mutane ta raba kayan ba, sai kowanne gunduma ya zo ya ɗauki na shi. Su ma idan suka kai wajen su ba a yarda su raba ba sai sun kira kowanne yanki sun ba su na su, su kai garinsu su raba. A halin yanzu ana duba waɗanda su ka fi kowa buƙata ne, ba a fara zuwa ga ma’aikata ba.

Za mu so ki yi mana ƙarin haske kan yadda aka fara gudanar da rabon kayan tallafin?

Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna ya naɗa kwamiti ƙarƙashin jagorancin mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe tare ’yan kwamitin mutum kusan 29, sun fara gudanar da wannan aiki na rabon kayan tallafi cikin himma da kwazo. Wannan kwamiti ya ƙunshi ƙungiyar ƙwadago, ƙungiyoyin addini, cibiyoyin sarakunan gargajiya, ƙungiyar mata ’yan kasuwa, ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman (nakasassu), ’yan majalisar jiha, shugabannin ƙananan hukumomi, da wakilan gwamnatin jihar. An tanadi isassun tsare-tsare domin tabbatar da cewa, kayayyakin tallafin sun isa zuwa wurin rabon kayayyakin abincin ba tare da wata tangarɗa ba da kuma jigilar kayayyakin zuwa ƙananan hukumomi daban-daban da ke jihar. Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani shi da kansa ya ƙaddamar da shirin raba buhunan shinkafa 43,000 mai nauyin kilo 50 domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a baya, wanda gidaje 210,000 na masu ƙaramin ƙarfi za su ci gajiyar shirin rabon tallafin a kashin farko na rabon tallafin a jihar. An raba wannan tallafi a ƙananan hukumomi 23 na jihar cikin wuni ɗaya, inda aka jera manyan motoci cike da kayan tallafin. A bai wa kowanne ƙaramar hukuma adadin nata kayan, yawan mutane, yawan abincin da za a raba.
Misali, a ƙananan hukumomin Igabi da Zariya da suka yawan jama’a, an fi ba su mai yawa duba ga adadin mutanen da ke yankunan. A ƙananan hukumomin ma akan duba yawan akwatuna, kamar a Igabi mu na da akwatuna ɗari shida, don haka a wane akwati an ɗauki mutum biyar-biyar a yankin da kwatin yake, ba kuma lallai sai mutumin ya zama yana kaɗa ƙuri’a ba, ko kuma dole yana zave, a’a, a akan duba masu tsananin buƙata ne a inda akwatin yake, kamar mace da ba ta da miji, makaho, gurgu da dai sauran su. Mun bi dukkanin ƙananan hukumomin jihar don tabbatar da cewa an yi rabon yadda yakamata kuma cikin aminci, kuma ba a samu wata matsala ba sai dai yabo daga mutane, domin ba a tava irin wanman rabon ba. Abin da zai burge mutum shi ne babu siyasa a cikin rabon, saboda ita yunwa ba ta da addini, jinsi ko jam’iyyar siyasa. Ganin yadda cire tallafi fetur ya yi wa al’umma illa ya sa gwamnati ta ce a yi wannam rabon, kuma gwamnatinmu ta APC ta tabbatar ta yi adalci tare da jawo sauran manyan jam’iyyu cikin kwamitin rabon.

A kan batun da ki ka yi magana ɗazu na ɗaya daga cikin ayyukan ma’aikatarki, duk da kuwa daman kin yi fice wajen kare haƙƙin masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda aka zalunta, to yanzu Allah Ya ba ki mulki, shin me ki ke yi na ganin cewa an hukunta masu zaluntar al’umma?

Kamar mutum ne a ce ‘za shi kitsu sai aka haɗa masa da masilla’, daman can mu na yi a matsayinmu na ’yan sa kai, to yanzu kuma aikin ne aka ɗauka aka ba mu na gwamnati, kuma wannan ma’aikata ce ke da alhakin irin waɗannan abubuwan na kare haƙƙoƙin yara da mata a duk faɗin Jihar Kaduna. Zan yi ƙoƙarin ganin cewa mun san waɗannan matsaloli da kuma inda su ke, mun san kuma hanyouin magance su, wanda a da sai dai mu yi kira ga gwamnati ta yi. Yanzu zan yi amfani da sanayya na gano tushen matsalolin, da kuma yadda za mu bi shi a riƙa samu hukunci a cikin lokaci, duk da cewa ba ni ba ce mai yin hukunci, mu na mu bibiya ne. Mun yi haɗin gwiwa tare da ma’aikatar shari’a da hukumar ’yan sanda.

A ƙarshe, waɗanne ƙalubale ne ku ke fuskanta a wannan ma’aikata?

Duk wani abin cigaba ba a rabuwa da ƙalubale, muna tun da mu ne ake kawowa kuka, to mu kuma sai dai mu kai kukanmu wajen Allah. Abin da kawai za mu iya cewa shi ne, ba ma son iyaye, sarakuna da masu unguwanni su na kashe kes a fadar mai unguwa, duk abin da ya zama babban laifi, a bar shi ya fito a yi hukunci don ya riƙa zama izina ga masu burin aikata irinsa. Ƙalubale na biyu shi ne ƙyama ga waɗanda aka zalunta, wanda idan an ce su zo a taimake su, sai su ce a’a, saboda za a yayata su, jama’a su kyamace su. Bai kamata al’umma su kyamaci waɗanda aka zalunta ba, azzalumi ne abin kyamata. Muna fatan al’umma su riƙa taimaka wa waɗanda aka zalunta.

Mun gode.

Ni ma na gode.