Mutum uku ne suka ɗora Tinubu

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA

Ranar 25 ga watan Fabrairu 2023, jama’ar ƙasar nan suka fita filin zaɓe domin su zaɓi wanda zai mulke su tsawon shekara huɗu.

Mutum huɗu ne suka fi samun tagomashi. Na ɗaya, ɗan takarar jam’iyyar APC wadda ke kan mulki, Jagaban Borgu, Bola Ahmed Tinubu. Na biyu Wazirin Adamawa Atiku Abubakar na PDP, na uku Peter Obi, na LP, sai na hudu Injiniya Rabiu Kwankwaso na NNPP.

Hukumar zaɓe ta ƙasa ta bai wa mutane miliyan 93 katin zaɓe. Amma da aka zo hakikanin zaven, kashi 27 ne suka fito. Da quri’ar Tinubu da Atiku da Peter Obi da Kwankwaso da sauran masu takara ko miliyan 25 ba su kai ba.

Ba a taɓa yin zaɓen da mutane suka ƙaurace masa ba a Nijeriya kamar na 2023. Mutanen da suka yi zaɓen, su miliyan 24 da ‘yan kaɗan, cikinsu mutum milyan 15 ba su zaɓi Bola Tinubu ba. Mutum milyan takwas ne kacal suka jefa masa ƙuri’a.

In maganar siyasa ta gaskiya za a yi, da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su ne suka kawo Bola Tinubu kan mulki. Na ɗauki tsawon lokaci ina kamfen cewa masalahar Nijeriya shi ne a duba dama-dama cikin waɗanda suka fito neman mulkin Nijeriya a zaɓi Atiku Abubakar a kawar da APC daga kan mulki. Ra’ayina shi ne, a zavi PDP, idan bayan shekara huɗu PDP ta yi mana rashin adalci, mu sake kayar da ita. Ana haka wata rana za a dace. Ba mu da wani dalili na dawo da APC kan mulki, hukunci na gaskiya mu kore ta daga kan mulki. Amma muka ƙi, saboda dalilanmu na ƙashin kanmu. Tunda mun zaɓo ta, sai mu biya farashi.

To yanzu saboda kauce wa ainihin lissafinmu an zabo dan fojare. Gumu- ta – gumu, Atiku Abubakar yana kiran Kwankwaso da Obi su dawo a haɗu a yaki Tinubu don a tabbatar da dimokuraɗiyya. A 2019, Kwankwaso ne fa wakilin Atiku Abubakar a Kano, a 2019 kuma Peter Obi shi ne mai rufa wa Atiku Abubakar baya a takarar shugabancin Nijeriya! Lissafin ya ƙwace. Su ukun nan su suka kawo Tinubu. Ya zama alaƙaƙai.

A cikin ƙasa da kwana 140 da hawan Tinubu, komai ya ta’zzara. Mutane sun daɗa talaucewa, ba kuɗi a hannunsu, in kuma sun samu kuɗin ko kaɗan ba su da daraja. Ba a ma san alƙibar gwamnatin ba. Yau ɗin nan litar man fetur 650 ake siyarwa.

Ku duba fa ku gani, wai yau a Naieriya, shugaban ƙasa ne da kansa ya shirga ƙarya na shekarunsa da karatunsa, kuma da kansa da sanin muƙarabbansa aka miqawa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC takardar bogi. Me shugabanni za su gaya wa sauran ‘yan Nijeriya?

Bello Muhammad Sharaɗa, mai sharhi ne kan al’amurran siyasa. Ya rubuto daga Kano.