Da Ɗumi-ɗumi: Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Ola Olukoyede a matsayin sabon Shugaban Hukumar EFCC a yayin zaman da ta yi a ranar Laraba.

Haka nan, Majalisar ta tabbatar da naɗin Muhammad Hammajoda a matsayin Sakataren hukumar ta EFCC.

Naɗin nasu ya biyo bayan kammala tantance su da majalisar ta yi.

Idan za a iya tunawa a ranar 12 ga Oktoban 2023 Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar, sannan Hammajoda a matsayin sakatare.