Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Maryam Ibrahim Hotoro da aka fi sani da Maryam Hotoro, jaruma ce a masana’antar fim ta Kannywood kana ma’aikaciya ce a tashar Arewa24, ƙwararriya a wajen fassara da kuma ɗora murya. A tattaunawar ta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma yadda ta zama mawaƙiya inda har ta buɗe kamfanin waƙoƙin bikin aure. Ku biyu mu:
MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki?
MARYAM HOTORO: Sunana Maryam Ibrahim Hotoro, amma anfi kirana da Maryam Hotoro.
Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?
An haife ni a unguwar Katsina Road, na yi primary a can, sanna na yi secondry a GGC Dala, sannan na yi FCE Kano na kammala, to sai na shiga harkar murya.
Menene alaƙarki da Hotoro da ake ce ma ki Maryam Hotoro?
Kamar yadda na faɗa an haife ni a Katsina Road ne to amma sai muka tashi muka koma Hotoro, anan na tashi wannan ne ya sa ake haɗa sunana da Hotoro.
A ɓangaren finafinai kamar guda nawa ki ka fito a ciki?
Finafinai gaskiya ban yi da yawa ba, saboda na fi ƙarfi a ɗora murya. Amma na fito a ‘Daɗin Kowa’ da ‘Tsangayar Malam’ da kuma ‘Rumfar mai shayi’, da sauransu.
Yaushe ki ka shiga Kannywood?
Gaskiya ban fi shekara takwas ba a Kannywood.
A ɓangaren ɗora murya fa yaushe ki ka fara?
Gaskiya na kai shekara 16 ina cikin harkar ɗora murya.
Lallai kin daɗe! To ta yaya ki ka fara harkar ɗora murya?
Gaskiya na daɗe ina sha’awar ɗora murya tun da daɗewa, tunda ni na fara da waƙa ne, Ni mawaƙiya ce duk da yake ban shahara ina waqa ba, amma dai mun gode Allah. To daga nan ne aka yi ‘introducing’ ɗina zuwa voicing fild.
Tsarin ɗora murya yana buƙatar ƙwarewa. Ta yaya ku ke aiwatar da shi?
Abinda kusan wasu mutanen ba su fahimta ba a harkar ɗora murya shi ne, ana raba aikin ne sashi-sashi, wato department department, idan aka sayo ‘content’, misali na Turanci ne ko na Indiyanci ko kuma na Larabci, to sai a kai shi sashin fassara, sai a fassara shi, idan sun kammala sai a kai shi sashin ɗora murya, sai a zaɓi muryoyin da aikin ya dace da su, sai a dora, to daga nan sai a saki fim ɗin.
Da wane fim ki ka fara ɗora murya?
Eh gaskiya wani Chanis ne yanzu ba zan iya tuna sunansa ba, kuma ba a Nijeriya a ke amfani da shi ba, to da shi na fara ɗora murya. Waɗanda na fara a Arewa24 kuwa gaskiya suna da yawa domin duk wani carton da za ka gani a Arewa24 da sabbi da tsofaffi za ka samu da muryata a ciki. Sai a ɓangaren Indiya munyi ‘Kundali Bagiya’ da ‘Sufni Suhani’ da ‘Tarkon Ƙauna’ da finafinan Turkiya, kai kusan duk wani fim da ake saka wa Arewa24 in dai na ɗora murya ne to akwai ni a ciki.
Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu?
Nasarori kam gaskiya Alhamdulillah, domin da ba wanda ya sanka amma yanzu kana tafiya za ka ji cewa wannan ita ce wance, wanda wasu kai tsaye za su kira ka da sunan ‘character’ ɗin fim, har mamaki abin yake ba ni, domin wani lokacin ƴar magana kaɗan zanyi sai ka ji an gane ka kuma an ambaci sunanka ka ga wannan ma nasara ce.
Ƙalubale fa, wane irin ƙalubale ki ke fuskanta a wannan aiki?
Ƙalubale ba za a rasa shi ba, wani lokacin idan mutane suka ga wani abu sai su yi ta suratu. Alhali su mutane ba su san irin ƙoƙarin da muke ba, domin mutanen nan da muke fassara ɗin su ba a ƙasarmu da addininmu ɗaya ba, muna iya ƙoƙarinmu wajen kiyaye al’adarmu da addininmu na Musulunci, amma wasu ba sa gani. Wannan shi ne ƙalubalen da muke fuskanta.
Kina da wani kamfanin shirya finafinai ne ko na kasuwanci?
Ina da kamfani na yin waƙoƙi, da yake ina waƙoƙi kamar yadda na faɗa a baya, kuma yanzu haka mun fito da wani tsari na waƙoƙin biki zalla ko suna kwanan nan muka fito da shi. to akwai Album da za mu yi wanda ya shafi wannan wanda za mu tallata.
Ba ya ga finafinan Arewa24 da ki ke ɗora murya akwai wasu finafinai ne da ki ka ɗora murya?
Eh wasu da yawa ma, misali yanzu haka muna ɗora murya a tashar Tv ta ZWorld, munje Legas, mun yi watanni muna ɗora masu murya, amma yanzu an dawo da yin aikin a Kano.
Ya batun aure. Kin taɓa yi ne?
Eh na taɓa yin aure, ina da ‘ya’ya ma. Akwai mace da kuma namiji.
Kina tunanin sake yin wani auren?
Dariya! Ƙwarai kuwa, shi aure nufi ne na Allah ko yanzu Allah ya kawo miji, wanda raina ya kwanta da shi, zan yi aure.
Kin san wasu kamarki da suka daɗe a masana’antar Kannywood sai su ce sai sun tara da yawa kafin su yi aure ke a wane mataki ki ke?
A’a ni ba ni da niyyar yin haka gaskiya, kuma su ma ba su sami abinda suke so ba ne shi yasa da sun samu da sun yi.
Wane saƙo gare ki ga masoyanki masu kallonki a fim da masu jin waƙoƙin ki da masu jin muryarki a fim?
Gaskiya masoya su ne tushen komai, ba ni da abinda zan ce masu sai godiya, ina ƙara gode masu kuma ina ƙara ba su ƙwarin gwiwa akan abubuwan da mu ke yi muna yi ne don faɗakarwa da nishaɗantarwa, mu ƴan adam ne ba mu wuce kuskure ba, duk lokacin da muka yi kuskure a yi mana afuwa, ina ƙara gode masu.
Mun gode da ki ka amsa gayyatarmu.
Ni ma na gode.
