Rubutu ya sauya min rayuwata da duniyata – Ramlat Manga Maidambu

“Na sha wahalar rubuta littafina na farko”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ramlat Abdulrahman Manga, wacce aka fi sani da Maidambu, na daga cikin jajirtattun marubuta onlayin da aka sha gwagwarmaya da su a duniyar marubuta, tun ba a san ko ita wacce ce ba. Ta yi rubuce rubuce da dama, waɗanda suka samu karvuwa a wajen jama’a har kuma ita ma ta yarda cewa ta samu alheri sosai. Tana daga cikin marubutan adabi da suka fito daga Jihar Bauci kuma take bai wa mara ɗa kunya wajen ɗaga sunan jihar a harkar batun rubuce-rubucen Hausa. A zantawarta da Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana ra’ayinta kan abin da ta kira rashin mutunta basirar ƙananan marubuta da masana’antar Kannywood take yi. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ina so mu fara da jin cikakken sunanki, da bayani game ke wacce ce.

MAIDAMBU: To, masha Allah. Salamu alaikum. Da farko sunana Ramlat Abdulrahman Manga, wacce aka fi sani da Maidambu. Ni ‘yar asalin Jihar Bauchi ce. Ni marubuciya ce, kuma ƴarkasuwa. Ina sana’ar sayar da kayan ƙwalama na yara, irin su tuwon madara, aya, gullisuwa, illoka, gyaɗa mai gishiri da sauransu. Sannan kuma ina sayar da littattafai. Ina da aure da yara uku.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki.

To, tarihina ba wani mai tsayi ba ne. Kamar yadda na faɗa, ni yar asalin Jihar Bauchi ce, amma an haife ni ne a kudancin ƙasar nan a garin Asaba na Jihar Delta. A can na fara rayuwata har zuwa lokacin da aka yi wani rikicin ƙabilanci a jihar, abin da ya tilastawa iyayena suka yi ƙaura daga can, muka dawo Arewa a shekarar 2006. A nan Bauchi na ƙarasa karatuna na sakandire, sai dai a lokacin ban samu na cigaba da karatuna ba, aka yi min aure. Amma a halin yanzu cikin yardar Allah ina shirye-shiryen sake komawa makaranta.

Ko za mu san inda sunan Maidambu ya samo asali?

Sunan Maidambu ya samo asali ne daga wata rigima da aka tava yi a tsakanin marubutan onlayin, a wasu shekarun baya. A lokacin duniya na kwance marubutan onlayin a sannan ba mu wuce mu arba’in ba. Sai ya kasance ana ta samun matsala, har aka samu rabuwar kai, aka rabe gida biyu. Idan har aka san daga wancan ɓangaren ka ke za a cire ka. Mu kuma a lokacin sai muka riqa sauya suna, don kada a gano muna leƙen asiri ne. Na riqa amfani da sunaye kusan uku, kafin na bar Maidambu. Ban tava tunanin sunan Maidambu zai zama sanadiyyar samun ɗaukakata ba. Domin daga baya sai sunan ya bini, har ma ya voye sunan Ramlat Manga.

Yaya ki ka samu kanki a harkar rubutun Hausa?

To, ni dai na kasance mai yawan son karance-karance ce, a lokacin sai ni ma na fara gwada yin nawa rubutun a qaramin littafi ina ajiyewa. Sai daga baya da aka fara fitar da labari a onlayin a zaurukan sada zumunta sai na fahimci ni ma zan iya ba da tawa gudunmawar ta hanyar fitar da nawa labarin. Kuma Alhamdu lillahi, kamar da wasa na fara, amma sannu a hankali sai rubuce-rubucen nawa suka fara karɓuwa duk da a lokacin babu wanda ya san da ni a cikin sanannun marubuta. Amma a haka na jajirce na cigaba da ƙoƙari, har dai aka fara sanina, ana kuma neman labaraina. Gaskiya lokacin ba ƙaramin al’amari ne a wajena, domin rubutu ya sauya min rayuwata da duniyata.

Wane ne ya fara zama miki jagora yayin fara rubutunki?

Gaskiya babu wani da zan ce gashi shi ne ya koya min rubutu. Ni kaɗai na yi ta faɗi-tashina, tun ina kwavawa ba tare da kiyaye ƙa’idojin rubutu ba, har dai a hankali na fara fahimtar yaya ake yi da taimakon wasu ƙawayena marubuta, Ummyn Yusrah da Hajara Oum Nass. Sune suka riƙa taimaka min da shawarwari har na iso inda nake a yanzu.

Wanne littafi ki ka fara rubutawa, kuma yaya salon labarin yake?

Littafina na farko shi ne, ‘Sharrin Cikin Gida.’ Ba na mantawa shi ne littafina na farko wanda a lokacin nasan yana cike da kurakurai. Labari ne da na ƙirƙire shi akan rikicin zaman gidan yawa, wanda ke cike da makirci, kishi, da hassada. Kasancewar shi ne labarina na farko na sha wahala wajen rubutawa, saboda a lokacin ina sabuwar marubuciya babu ƙwarewa.

Daga wancan lokacin zuwa yanzu, waɗanne abubuwa ne suka canza game da yadda ki ke rubuce-rubucenki?

Abubuwa da yawa sun sauya, a da rubutun kawai nake yi kara zube, amma tun daga lokacin da na fara gwada bincike a kan labarin da nake so in rubuta, lokacin da na yi wani littafina mai suna ‘Masarautar Jordan,’ sai na fahimci muhimmancin bincike yayin rubuta littafi. Na gane cewa, shi labarin da aka yi bincike akai kamar abinci ne da aka haɗa mishi kayan alatu sosai na girki, ka ga ko baka ci ba, zai burge ka.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa?

Na rubuta littattafai kimanin ashirin da wani abu. Daga ciki akwai, ‘Daula Biyu’, ‘Matar So’, ‘Matar Malam’, ‘Mrs Amidud’, ‘Yar Yadiko’, ‘Zanen Ƙaddarata’, ‘Ina Da Buri’, ‘Ƙwarƙwara’, ‘Nazneen’, ‘Sanin Gaibu’, ‘Wata Alƙarya’, ‘Abinda Ya Baka Tsoro’, ‘Zayn Malik’, ‘Dashen Allah’, ‘Baƙin Haure’, ‘Bororoji’, ‘Kallabi’, ‘Kishi’, ‘A Tsakanin Zubda Jini’, sai kuma ‘Ruwa’.

Shi labarin’ Masarautar Jordan’. Labari ne da aka gina shi akan wata masarauta da ke yankin ƙasashen Larabawa. Na bayyana yadda aka rufewa Sarkin masarautar labarin rayuwarshi ta hanyar kashe mahaifinsa, mahaifiyarsa kuma ta gudu don ceton rayuwarta, tare da haqura da ɗanta. Sai wani likita ne a masarautar ya taimaka mata, har a ƙarshe ‘yarshi ta yi sanadin haɗa ɗa da uwa.

Littafin Bororoji kuma labarin wata yarinya ne Almamoon da aka riqa canza mata kamanni ana yi mata shigar maza, tun daga haihuwarta, har zuwa girmanta. Sakamakon wata muguwar ɗabi’a da wasu Fulanin Bororoji suke ita, ta yi wa ƴaƴa mata ciren mijin aure ko suna so ko basa so. Daga wannan ciren idan an tafi da yarinya shi kenan an rabata da danginta, wasu daga baya a kan dawo da su a wani irin yanayi. A labarin Bororoji shi ma abinda ya faru kenan da mahaifiyar Almamoon, wacce aka yi wa cire a ranar aurenta, sanadiyyar haka ta rasa danginta bakiɗaya. Har aka gama labarin dai bata sake haɗuwa da kowa nata ba.

Shi kuwa littafin ‘Kallabi’ labari ne a kan Masarautar Gobir ta wancan lokacin, yayin da aka fuskanci rigimar sarauta, sharri da zalunci, har aka raba sarkin da matarsa, saboda zalunci. Bayan wasu shekaru yaran sarkin da aka fitar, suka koma, inda aka samu damar kashe ɗaya daga cikinsu domin tagwaye ne.

Wanne ƙalubale ki ka samu a farkon fara fitar da littafinki?

Gaskiya ƙalubalen shi ne, rashin sanina a harkar rubutu, don haka mutane na min kallon baƙuwa ba su san salon labarina ba, don haka ba kowa ke karanta littafina ba. Sai dai idan wasu ne suka yaba da labarin a wani waje ko suka tayaka tallatawa, sai ka ga an fara nema, har wasu su saya don su karanta. Gaskiya a farko na fuskanci matsala, kamar yadda sauran sababbin marubuta suke fuskanta. Sai da na yi littafi har huɗu, amma mutane ƙalilan ne ke karantawa, a na biyar ne duniya marubuta ta fara sanin wace ce ni.

Kin taɓa wallafa wani daga cikin littattafanki ko duk a onlayin ki ke sake su?

Gaskiya dukkansu a onlayin nayi su, babu wanda na buga.

Wanne salon rubutun ki ka fi amfani da shi wajen isar da saƙonninki?

E, to! Zan iya cewa ba ni da wani takamaimen salo da nake amfani da shi, ya danganta ga inda labari ya jani ne. Sai dai wani lokaci na fi gina labarai na akan abubuwan da suka shafi masarautun gargajiya da na zamani da rikita-rikitar da ke faruwa a gidajen sarakuna da tsakanin iyalansu. Amma ko’ina ina tavawa.

Shin kin yarda rubutun finafinai da kallo ya janye hankalin marubuta da masu karatu?

E, zan iya yarda da haka. Domin kuwa na lura akasarin matasa musamman ƴammata hankalinsu ya fi karkata zuwa kallon finafinai. Ba na mantawa lokacin da na gama rubuta littafin ‘Ƙwarƙwara’, a ranar wata ta fara ba ni shawarar da na fara kallon finafinan ƙasar Koriya, domin a lokacin ban tava tsayawa kallonsu ba. Sai daga baya da na fara kallon na fahimci wasu marubutan suna kallon labarin wani fim ne sai su juya shi zuwa littafi. Yanzu haka saboda yawan kallon ina iya fahimtar ko littafi na karanta matuqar an yi fim ɗinsa, ina gani zan fahimta.

Yaya ki ke kallon gudunmawar marubuta ga cigaban masana’antar Kannywood?

E, a gaskiya a ra’ayina masu shirya finafinai na Kannywood ba sa taimakon marubuta. Ba sa janyo qananan marubuta a jiki suna ba su aikin rubutun fim, ko kuma su sayi labarinsu da daraja. Kullum su kenan daga Ibrahim Birniwa sai Yakubu S. Kumo. Ba wai muna musu hassada ba ne, amma an ce ba don makoya ba da gwanaye sun ƙare. Muna da fasihan marubuta sosai a cikin mu, amma ba a san da mu ba, ko kuma ba a yarda za mu iya har ma ƙila mu yi wani abin da waɗancan ba su kawo ba.

Ta yaya za a iya bunƙasa harkar rubutun adabi ta kai darajar yadda masu shirya finafinai suka kai?

Idan manyan marubutanmu da manyan masu shirya finafinai a masana’antar sun so, za su iya wannan hoɓɓasan. Akwai matsayar da za mu iya cimma, don mu taimakawa juna a, samu cigaba ta kowanne vangare. A Nijeriya ne za ka ga marubuci bai da wata daraja, amma a ƙasashen da aka cigaba za ka ga yadda ake son cigaban marubuci har ya kai ga nasara. Dubi misalin marubuciyar littafin Herry potter, ita kanta bata kawo cewa labarin zai kai ga nasara ba, amma an wayi gari sai da ta yi mafarin Herry Potter wato Fantastic Beast.

Sannan a 2022 zuwa 2023 akwai wani fim da aka yi a ƙasar Koriya, wanda marubutan labarin mata ne. A lokacin zan iya ce maka fim ɗin ya danne kowanne fim a ƙasar. Kasan me ya sa? Saboda gwamnatinsu ta bunƙasa harshensu, sannan ta tsaya musu kan su cigaba. Ba irin ƙasar mu ba, da za a yi ta gudun ƙananan marubuta ana neman manya. Shi ya sa zai yi wahala a samu bunƙasa darajar harshen Hausa zuwa matakin da ake so, domin an ware zaratan marubutan da suke da gogewa ana yi da su.

Shin kina da YouTube Channel ne ke ma? Kuma wacce riba marubuta ke samu daga sanya littattafansu a YouTube?

E, ƙwarai. Ina da shi, amma bani da lokacin ɗora littafi a kai saboda ayyukan da suke gabana. Amma babu shakka akwai riba sosai, musamman idan kan son nasara. Dole ka watsar da duk wani abu ka gina YouTube ɗin ka har dai ya kai matakin da za ka iya samun alheri a cikinsa. Gaskiya akwai riba sosai a cikin harkar YouTube.

Wanne littafi ne bakandamiyarki, kuma mene ne ya bambanta shi da sauran littattafanki?

A nan kuwa zan ce maka littafin ‘Ƙwarƙwara’ ne, duk da kasancewar ‘Masarautar Jordan’ ya doke shi wajen karvuwa, amma ni a cikin raina na fi son ‘Ƙwarƙwara’.

A wanne yanayi ki ka fi son yin rubutu ko kuma basirar yin rubutu ta fi zuwa miki?

Bayan sallar asuba, zuwa wayewar gari. Na fi nutsuwa na yi abinda ya dace.

Shin kin tava fuskantar matsalar toshewar qwaqwalwa ta Writer’s Block? Kuma ta yaya ki ka shawo kanta?

Tabbas na tava samun wannan matsalar, kuma har yanzu ma ina fama da ita. Amma na lura sai ina rubuta littafin kyauta ne na fi samun wannan matsalar, ba na samun damuwa idan littafin kuɗi nake rubutawa. Akwai littafaina guda uku da suke jingine, sai na fara, sai kuma na ji komai ya fice min a rai. Sai dai duk lokacin da na fuskanci haka, sai na ajiye rubutun bakiɗaya. Sai bayan na samu nutsuwa ƙwaƙwalwata ta huta, ko na tsiro da fita yawo ko kallon fim, a haka sai in ji sha’awar rubutun tana dawowa.

Menene shawararki ga marubuta don samun cigaban harkar rubutu bakiɗaya?

Tow Allah ya gani bana ce ba, a yi ta haaƙuri ita rayuwa da nasara a hankali ake samun shi, duk wanda ka ga ya samu nasara. Kada ka yi tsammanin lokaci ɗaya ne, tafiyar shi ba yau ya fara ba, don haka nasarar idan tazo dole ya same ta ‘more than how you expect’.

Su wane ne ƙawayenki a harkar rubutu, kuma menene silar aminantakarku?

Hajara Oumnass, Ummyn Yusrah, Sanah matazu. Waɗannan ba laifi ina ji dasu a harkan rubutu. Su ne suka taimaka min sosai.

Wane ne gwaninki a marubuta da ya zama miki madubi kuma tsani a harkar rubutu?

Allah sarki, Zahra’u Baba Yakasai. Ina sonta a duk lokacin da na tuna da rubutunta, sai naga ashe dole na yi aiki tuƙuru domin samun irin nata.

Kin taɓa samun wata matsala da ta sa ki nadama da harkar rubutu bakiɗaya?

E, Alhamdulillahi. A baya can na taɓa samu, amma a yanzu komai ya wuce. Ba ni da wata matsala da mutane, daga marubuta ko masu karatu. Ban cika bari wata alaƙa mai ƙarfi da za ta iya kawo mana damuwa da mutum ta shiga tsakanina da wata ba. Hasalima ban cika shiga cikin mutane sosai ba. Sannan bana damuwa da wasu, harkar gabana da rubutuna sun ishe ni. Idan na ga mutum ɗan bala’i ne, sai na bishi da idanu. Ai zuru bata cin zuru!

Wacce riba ko alheri ki ka samu ta dalilin rubutu, wanda ba za ki manta ba?

Alhamdulillahi Alhamdulillahi, idan na ce Alhamdulillahi ina nufin Alhamdulillahi. Domin Allah Ya ɗaga darajata a hanyar rubutu, na haɗu da mutanen kirki, na samu alkhairi sosai a rubutu. Alhamdulillahi.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shawo sai ya yi.

Masha Allah. Na gode.

Ni ma na gode sosai.