Ilimi ne ƙashin bayan cigaban Zamfara – Lawal

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ayyana ilimi a matsayin ƙashin bayan cigaban Jihar Zamfara.

Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙincin ɗaliban makarantar Leadsprings International School a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau a ranar Laraba.

Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce yayin ziyarar, ɗaliban sun miƙa wa Lawal muhimman ƙudurori guda bakwai don amfanin gaba.

Suleiman ya ce ƙudurorin sun haɗa da raya babban birnin jihar, wato Gusau, inganta fannin tsaro, samar da kamfanin jirgin sama mallakar Zamfara, bunƙasa fasaha, bunƙasa fannin noma, ɓangaren kasuwanci da sauransu.

Sa’ilin da yake yi wa baƙin nasa jawabi, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta farfaɗo da fannin ilimin jihar.

Ya ce, “Ilimi shi ne fannin da gwamnatina ta fi bai wa muhimmanci, sai kuma ɓangaren tsaro. Kodayake a baya fannin iliminmu bai taka rawar yadda ya kamata ba.

“Musamman ma Jihar Zamfara, jihar ta yi ta fama da koma-baya a fagen ilimi. Wannan ne ya sa na ayyana dokar ta-ɓaci a fannin.

“Kuma daga cikin matakan da muka ɗauka don farfaɗo da ɓangaren sun haɗa ɗaukar ƙwararrun malamai, samar da kayayyakin koyo da koyarwa da samar da sabbin dabarun koyarwa.

“Gwamnatina ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bunƙasa fannin ilimi don cimma buƙatun talakawan jihar,” in ji Gwamna Lawal.

Ga ƙarin hotuna daga ziyarar: