Gwamnati ta lissafa Mamu da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta lissafa Tukur Mamu tare da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyi ayyukan ta’addanci a ƙasa.

Sashen tattara bayansn sirri kan hada-hadar kuɗi (NFIU) ya bayyana sunayen  mutum 15 da lamarin ya shafa, da suka haɗa da wasu mutum tara da cibiyoyin canji (BDC) shida da uma wani kamfani ɗaya.

Bayanan NFIU sun nuna cewar Kwamitin Kafa Takunkumi na Ƙasa ya yi zama a ranar 18 ga Maris, inda a Ƙarshen zaman nasa ya bada shawarar kafa wa wasu takunkumi saboda samun da aka yi da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci.

Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa shi ne Tukur Mamu, wanda gwamnati ke ci gaba da takfa shari’a da shi bisa zargin tallafa wa ‘yan ta’addan da suka kai wa jirgin ƙasan Abuja-Kaduna hari a watan  Maris na 2022.

An tsare Mamu ne a birnin Alƙahira na ƙasar Masar inda aka dawo da shi Nijeriya bisa rakiyar matarsa da wani a ranar 6 ga Satumban, 2022.